NOVELSUncategorized

DIYAM 14

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forteen : My Boyfriend

Ina ajin karshe a primary Sadauki shi kuma yana ajin karshe a secondary. Mu nan wai muma mun girma a ajin mu sai ake yin irin soyayyar nan ta
yarinta. Kowa da saurayinta, amma ni banda ni. Wannan abin yana kona min rai kullum ina ganin ana rubutowa kawayena love letter su karanta suyi replying amma ni babu wanda yake rubutomin. 

Akwai seat mate dina lubabatu kuma itace headgirl, ita head boy din mu yake so, kuma dan rainin hankali ni yake bawa wasika in bata wai kunyarta yake jiba zai iya bata ba, ita ma kuma inta rubuta reply ni take bawa in bashi, su basu san haushi suke bani ba gabadayan su.

Ranar nan, ina koro yara aji an gama breakfast sai muka hadu dashi. Muka gaisa yana ta sosa keya ni kuma na fahimci me yake so na bata rai nace “kar ma ka tambaye ni, ni bansan inda take ba” yace “ni fa ba cewa nayi ina neman lubabatu ba, yanzu ba zamu gaisa ba sai kinyi tunanin wani abu?” Nayi gaba nace “oho dai, kai kasani” ya biyoni “dan Allah Halima kina ji ba? Ki ce mata bata bani amsar jiya ba fa” nayi kamar ban jishi ba nayi tafiyata. Bayan naje na zauna a aji na ganta tana ta faman zanen flower a jikin plain sheet, nayi tsaki nace “rashin aikin yi, wai soyayya? Yar karama dake har kin ita rubuta wa saurayi wasika. Allah ya sawake, kuma in baki daina ba sai naje gidan ku na fada” ta harare ni tace “Allah yaso ma dai ni wasika kawai nake rubutawa saurayi na, ke kuma fa? Da kullum kuke yawo ke da naki saurayin?” Nayi galala ina kallonta ina tunanin waye take nufin saurayi na, sai kuma nayi dariya nace “wai Sadauki kike nufi? Bafa saurayi na bane ba, yayana ne to” ta harare ni tace “in yayan ki ne to ya akayi ke fara shi baki? Kuma ai munsan ba babarku daya ba kuma baban ku ma ba daya ba” naji haushin maganar ta na dauki jakata na bar mata seat din na koma wani. Amma kuma sai maganar ta ta tsaya min a raina, wai Sadauki ne saurayina.

Ina nan zaune har aka tashi. Ana ta zuwa daukan dalibai sai ga wata sa’adatu yar A ta leko ta window tace da karfi “Halima Usman ki fito ga wannan saurayin naki yana nemanki” Lubabatu ta juyo tana yi min dariya ni kuma na kara kulewa, na dauki jakata na fita.

Kamar hadin baki sai gashi washegari muka je gidan Mama tare da Inna, muna ta harkokin mu dasu Rumaisa su Inna kuma suna hira, sai naji kamar sun ambaci sunan Sadauki sai na saurara ina jin abinda suke cewa. Inna tace “mtsw, Hafsa ba zaki gane abinda nake nufi ba, ni nake zaune da yaran nan ni kuma nake ganin abinda nake gani wallahi. Ina jin tsoro Hafsa. Bana son abinda nake gudu ya kasance” Mama tace “wai gani kike in sun girma zai iya cewa yana son aurenta?” Inna tace “sosai ma kuwa, ya riga ya shanye ta kamar yadda na fada miki, kuma alamu sun riga sun gama nunawa. Tsoro na Allah tsoro na kar ya furta abinda nake tunani saboda kinsan halin baban su, wallahi indai yaron nan yace yana son yarinyar nan bashi ita zaiyi” Mama tace “chafdi. Kice tsugunne bata kare ba kenan. Allah yaji kan inno, da tana raye wallahi da tuni ta fatattaki yaron nan daga gidan nan. Ni babban tashin hankali na shine rashin sanin asalin sa. Ga tambarin da uwarsa take dashi. Yanzu menene abinyi?” Mama tace “ni so nake kije ki kai maganar nan gidan Alhaji Babba, shi kadai ne zaiyi min maganin fitinar nan wallahi” Mama tace “wanne Alhaji Babba? Alhaji Babba ba zai iya yi miki maganin komai ba saboda kinsan halin mijinki ba lallai ne in Alhaji Babba ya gaya masa magana ya dauka ba. Ke dai addu’a zamuyi tayi, idan har Allah ya rubuta aure a tsakanin su to Allah ya daidaita lamarin” Inna tayi saurin girgiza kanta tace “babu, insha Allah babu, da wanne zanji? So kike zuciya ta ta buga?” Mama tace “ni Adda ba sanin yaron nan nayi sosai ba, gaya min, bayan rashin sanin ubansa da ba’ayi ba yana da wani aibun ne?” Inna ta bude bakinta ta rufe, ta kasa tuna wani laifi da Sadauki yayi mata wanda zata bayar da misali da shi.
Duk a cikin hirar su Inna kalma biyu ce ta tsaya min a raina. “So” da kuma “Sadauki” nayi ta kuya kalmomin a raina ina tunanin ma’anar su. Wai soyayya muke yi ni da Sadauki? Sai kawai naji wani excitement ya lullube ni. I can’t wait in bawa Sadauki wannan labarin. Magrib tana yi inna ta ce mu nemo hijaban mu da takalman mu mu tafi gida “kunga yau na jawo muku kunyi fashin makarantar yamma, gwara mu tafi da wuri kar Diyam ta rasa ta daren itama” sannan ta bawa Mama labarin dalilin da yasa ta saka ni a islamiyyar dare. Mama tana ta dariya muka taho.

Muna zuwa gida sallar isha nayi kawai na saka hijab dina na dauki jakar islamiyya ta, Inna ta bani kudi wai ko zanga yara suna siyan wani abu. Nayi mata sallama na fita amma ina fita sai nayi hanyar kofa kamar na tafi sai nacire takalmana na dawo da baya na zagaya ta kofar dakin Baffa na hare saman bene. Ina zuwa na zubar da takalma na a gefe na cire hijab dina na ninke dan kar yayi squeezing na kwanta rigingine na rufe idona ina jin dadin iskar da take kadawa a gurin. Na jima a haka ni ba bacci ba ba kuma ido biyu ba. Sai naji a jikina kamar ana kallona. Nayi murmushi na bude idona a hankali na sauke su a cikin na Sadauki daya zauna ya saka ni a gaba ya zuba tagumi yana kallona cikin hasken farin wata. Yayi murmushin daya bayyana kyawawan jerarrun hakoransa  Yace “wato kinji dadin iska ko? Shine har da bacci?” Nayi dariya kawai, nace masa “ya garage din yau, mota nawa ka gyara yau?” Ya bata rai yace “daya” nace “kawai?” Yace “kinsan irin lalacewar da motar nan tayi kuwa?” Nan ya fara bani labarin irin parts na motar da suka lalace da irin yadda ya gyara su, ni kuma nayi shiru ina sauraronsa duk kuwa da cewa ba ganewa nake yi ba, sai daya gama sannan yace “to ya gidan Maman” nace “lafiya lau” sai kuma na bata rai nace “ina sweet dina?” Yayi murmushi ya saka hannu a aljihu ya dauko alawar splash guda biyu ya miko min, na karba nayi masa godiya sai kuma na bare daya na mika masa dayar kuma na jefa a baki. Sai ya zagaya bayan pillow na shima ya kwanta rigingine ya dora kansa akan pillown da nake kwance akai, sai ya kasance shi a kasa yake ba’a kan katifar da nake ba. Yayi shiru kamar bacci yakeyi amma ni nasan ba bacci yake yi ba, nasan kallon sky yake yi kamar yadda nima nakeyi. 

Can kuma sai naji yace “Diyam? Yau sky tayi kyau sosai” nayi murmushi ina kallon yadda wata ya cika very full, ga stars ba adadi sun cika sararin samaniya. Sai na juya nayi rub da ciki na tallafe fuskata da hannayena, wannan yasa dankwali na ya zame saboda santsin gashi, gashin ya zubo a fuskar Sadauki, ya saka hannu ya tattare su gefe yana kallona, direct nace masa “Sadauki wai kai saurayi na ne?” Sai ya kware da alawar da yake sha, ya mike zaune yana tari yana bubbuga kirjinsa sannan ya kalle ni da mamaki yace “what?” Na daga kafada nace “nima haka naji ana cewa” ya kwanta rub da ciki irin yadda nayi yayi tagumi da hannayen sa yana kallona fuskarsa cike da mamaki yace “a ina kika ji ana fada?” Na bashi labarin abinda ya faru a school, ya ja hancina har yanzu da dariya a fuskarsa yace “ke kuma me kika ce? Are you my girlfriend?” Na juya na koma rigingine nace “oho” yace “oho? Baki sani ba?” Nace “eh, to kaga ai kai baka rubuta min letter da kalaman soyayya” yayi dariya sai kuma ya rufe bakin sa dan kar ajiyo dariyar tasa daga waje yace “kalaman soyayya Diyam? Naga ta kaina ni Aliyu, Diyam a ina kika san kalaman soyayya?” Nace “a makaranta mana. Ka ga lubabatu headgirl din mu to head boy ne saurayinta, kuma kullum sai ya rubuto mata letter ya bani na bata” yace “ohh, wato abinda kuke yi kenan ko? Head boy saurayin headgirl, ke kuma assistant head girl ke ce budurwar assistant head boy ko?” Nace “lah, ni me zanyi da wannan kazamin?” Ya koma ya kwanta, sannan yace “to ni yanzu me zanyi kenan in ina so in zama saurayinki?” Na daga kafada nace “wasika zaka rubuto min” yace “to ni ban iya ba, ki koya min” nace “kaga, plain sheet zaka samu, sai kayi zanen flowers da pencil, sai kazo ka zana heart da arrow yayi crossing heart din ka rubuta sunan ka a sama nawa a kasa, sai ka rubuta I love You Diyam a saman takardar, a ciki kuma sai ka rubuta min kalaman soyayya shikenan” yayi murmushi mai sauti yace “to ni ai ban iya kalaman soyayyar ba” na bata rai nace “ni ma ban iya ba ai” muka yi shiru gaba-daya muna kallon sky. Can sai naji yace “Diyam. Look at the stars, kinga yawansu ko? To zabi daya wadda kike ganin a idonki kamar tafi sauran dukka haske. Concentrate on it kiyi ta kallonta ita kadai ki manta da sauran, ki saka a ranki kamar babu sauran kowanne star a sky din nan sai wannan wadda kike kallo. A hankali zaki ga sauran sunyi disappearing, zaki ga ba kya ganin komai asararin samaniya sai wannan star din guda daya” nayi exactly yadda yace, sai naga komai ya bace a idona sai star guda daya, yace “do you get it Diyam?” Na gyada kaina da sauri ina murmushi, yace “to haka nake ganin ki a idona, ke kadai kike haske a duniya ta, duk sauran mutane da duhu nake ganin su. You are the only star in my sky” nayi murmushi na maimaita “You Are the only star in my sky”  yace “that’s right. Ki rike wannan a ranki, ko mai tsanani, komai shudewar zamani, ke kadai ke zaki kasance a raina har gaban abadan” nayi dariya nace “wallahi ka iya ashe. Yayi dadi sosai” yace “to shikenan na zama saurayinki?” Sai kawai naji wata kunya ta lullube ni, nayi sauri na rufe idona da hannayena guda biyu, yace “au wai kunyata kike ji kuma? Bude idon ki gani” na makale kafada, yace “kinga wani abu” nace “naki wayon” sai yakama hannu na da niyyar bude fuskar ni kuma sai na tashi da gudu na fara sauka daga stairs, shaf na manta da cewa buya nayi, na manta cewa gudun makaranta nayi, sai da naji muryarsa a bayana yace “Diyam!!, Come back!!” A daidai lokacin ne kuma idona ya fada cikin na Inna a tsaye a tsakar gida da tray din tea a hannunta. Muka tsaya muna kallon kallo, cike da mamaki tace “Diyam?” Adaidai lokacin da Sadauki yayi appearing a bayana. Ta saki trayn hannunta ya fadi cike da karar data jawo hankalin Baffa da Ummah suka fito a tare kowa daga dakinsa.

Writing…..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button