BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 41-45

Page 4⃣1⃣ to 4⃣6⃣

kafin kace me har rabi ta gama shiryawa sai a lokacin inna asabe taje ta fada wa jiddah maganar da aiken data musu,,bata kawo komai a ranta sai ma shiri data fara yi tana gama wa rabi tace su tafi..kudin mota inna asabe ta basu sannan tace suyi sauri su tafi,,suna fita mota suka hau suka wuce,,koda suka isa gidan sun tarar bata nan amma sai rabi tace su zauna su jirata kila ba dadewa zatayi ba ta fada kawai domin daga ita har innan sun san bata nan,,zaman taga bana karewa bane gashi kuma ta fara tunanin tafiyar ammar har 4:30 a lokacin amma taga rabi bata da niyyar tashi su tafi,,so take ta mata magana tace su tafi amma ta kasa,,dakyar ta daure tace mu tafi gida mana tunda yamma tayi gashi kuma har yanzua bata dawo ba,,murmushi kawai rabin tayi kafin tace kiyi hakuri jiddah kinsan halin inna idan muka koma babu sakon nan mita zatai tayi,,,ita dai jiddah bata kara magana ba amma fa zuciyar ta fal ta cika da kunci kamar ta fashe da kuka haka take ji dan tasan 5:30 jirgin su ammar zai tashi allah yasa ma a fasa tafiyar(niko nace ai ba fashi jiddah)

karfe biyar dai dai ammar ya tsaya a kofar gidan su jiddah yaron da ya ayka cikin gidan ne yaga ya fito yana fadin wai batanan,,batanan ya maimaita cikin mamaki ina zataje yau friday a wannan lokacin…muryar inna asabe ce ta katseshi tana fadin ai jiddah bata nan sun fita da maman salaha ta rakata zaria kuma naji kamar suna cewa sai gobe zasu dawo…tunda ta fara magana ya bata rai taya zata fita bayan tasan yau zai tafi kuma yacea mata yau din zai zo suyi sallama,,bai ce mata komai ba kawai ya juya dan ranshi a matukar bace yace,,,tafiya kawai yake yana tunanin abinda jiddah tayi,,yana zuwa gida bai tsaya komai ba ya samu abban shi a bakin mota dama shi kadai yake jira dan sun gama komai ko kallon umma dake mai ALLAH ya kiyaye hanya baiyi ba shigewa kawai yayi ya zauna kafin shima abba ya shige ya tada motar,,umma ji take kamar an mata bushara da gidan aljannah yau ammar zai bar kasar sai kuma bayan 5yrs zai dawo,,,
tana ganin fitar su a gidan itama ta fice…

sai karfe shida jirgin su ya tashi ya tafi cike da kewar jiddah domin har hawaye sai da ammar yayi yana kuma jin haushin yanda bai hadu da ita ba,,

sai da sukayi sallar magrib amma har a lokacin bata dawo ba,,sai a lokacin inna asabe ta kira rabi tace su dawo,,shirin tafiya suka farayi,,amma jiddah jikinta a sanyaye tanaji a jikinta ammar ya tafi,,hawaye kawai takeyi a cikin mota amma ba wanda ya lura da hakan,,,suna karasa wa gida sallah ta farayin kafin a miko mata abincinta takai abincin baki kenan..taji inna asabe tace dazu kuwa ammar yazo miki sallama amma bakyanan shine yace to in fada miki ya wuce,,kasa kai abincin bakinta tayi sai hawaye daya fara zuba kamar an bude famfo fadawa daki tayi da gudu kuka takeyi kamar ranta zai fita shikenan ba zata kara ganin sa,,kuka ta kara fashewa dashi…inna asabe kuwa jin kukan take kamar sautin kida ba abinda takeso irin taga jiddah cikin kunci cikin masifa da bala’i amma da yake munafuka shiga dakin tayi ta fara lallashin ta har ta dan tsagaita,,haka jiddah ta kwana tana tunanin ammar tana kuma addu’ar allah ya kareshi duk inda yake,,(masoyin gaskiya kenan)

ammar mutanen india an sauka lafiya dama akwai abokin abba shine ya aiko a dauke shi isar su gidan keda wuya yaga kowa yana ta nan nan dashi daga shi sai matar sa da ya’ya’n su biyu duka maza dayan mai suna abbas sa’an ammar ne sai kuma karamin wanda baikai 20yrs ana ce masa annur,,yanda suka rinka tarairayar sa shi yasashi farin ciki sosai,,,sai daya yi kwana2 yana hutawa kafin ya fara shiga skul shida abbas,,,ammar ya maida hankali sosai a karatun shi ba ruwan shi da babes din dake tururuwa akanshi bakake da fararen wasu abota suke yin dashi wasu kai tsaye zasu nuna sonshi baya kula su dan shi ba tasu yake ba mace daya keda wannan matsayin kuma baya tare da ita amma kullum da ita yake kwana yake tashi a ransa,,har su abbas sun san labarin jiddan ammar,,haka rayuwa take ta tafiya cikin kwanciyar hankali,,

a bangaren jiddah sai ince maganin inna asabe ya fara ci dan yanzu tana ji ana kiran sallah amma bata damu ta tashi tayi ba,bata karatun Qur’ani ballantana kuma azkar din da takeyi haka kawai zata rinka jin kasala a jikinta ko kuma jikinta ya mata nauyi,,inna asabe tana cikin farin ciki tana lura da duk halin da jiddah ke ciki har tana shirin komawa wajen boka ya cika mata aikin da suka fara….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button