BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 25

25

……..“A’a lafiya?”.
Khaleel dake shigowa ya faɗa idonsa a kansu. Baya Anam ta ɗan ja tana murmushi, ta girgiza masa kanta. “Ba komai Yaya ina dubata ne kawai”.
“Okay tom ai haka yana da ƙyau. Bara nima mu gaisa sai mu wuce kar ki makara”.


Kai kawai ta jinjina masa. Ta watsama Fadwa harara ta juya ta fice a ɗakin. Da ƙyar Fadwa take iya amsa tambayoyin Khaleel, gaba ɗaya a birkuce take da kalaman Anam. Domin kuwa zancen Anam ɗin na nuna mata tabbas taji duk shirunsu da su Sima kenan. Cikin ƙanƙanin lokaci zufa ta gama jiƙe mata jiki. Har Khaleel ya fahimci haka ya tambayeta ko jikin ne?. Kanta ta jinjina masa cikin kaƙaro murmushi. “Kawai inaga allurar da sukai mince bata gama sakina ba barci nake ji”.
“Ayya ALLAH ya ƙara lafiya. Doctor ɗin ma yace zuwa anjima zai sallameki, inaga bara na ajiye Anam a wajen aiki karta makara zan dawo yanzun”.


Kanta kawai ta iya jinjina masa nan ma. Yana fita ta jawo wayarta cikin rawar jiki. WhatsApp ta shiga, ta haɗa group da sauri tare da adding su Siyyah a ciki. Cikin sa’a ta samu Bibah da Sima a online. Cikin bada umarni tace suyi kiran Amal da Siyyah su hau online tanada magana da su. Duk sun san tana asibiti tun jiya, sai dai basu zo ba kamar yanda suka shirya har sai ta koma gida dan karma wani ya zargi wani abu. Tsoron yin voice note wani yajita ko kiransu ya sata tafa musu duk yanda tai da Anam yanzu. Suma hankalinsu ya tashi amma duk sai suka danne kowa ya shiga faɗin albarkacin bakinsa.


Maganar Sima ta sakasu duk maida hankalinsu gareta, dan zancen ya dauki hankalinsu. Sima Inaga ba hankalinmu ya kamata mu tayar ba, idan ita tace kwalba ce uwar sheri sai mu nuna mata muɗin gilasai ne mun fita haɗari. Kafin ta faɗama wani zancen nan dolene mu juya komai kanta, hakan ma zai zama hanya mai sauƙi da zata bar miki gida dan koshi mijinki daba son cikin yake ba na tabbatar sai ya tsaneta.
Cikin ɗan tsumar jiki ta tafa saƙo tana tagging maganar Sima. Kinga Sima bar zagaye-zagaye faɗi minene shirin naki kai tsaye kawai dan ALLAH.


Sima Kafin ta faɗi kin zubar da cikin mu zamu fara sanarwa itace ta zuba miki maganin zubda ciki.
Bibah Ta yaya hakan zata faru tunda bamu da wata hujja Sima?!”.
Sima Muko keda hujja. Doctor zamu samu ya faɗama su cikin ya zube ne ta hanyar magani da aka sha, bayan kowa ya gama ji da ɗaukar ɗumi akan maganar mai-aikinki ta tabbatar musu taga shegiyar sanda take zuba maganin. kinga sai mu samu ƙwaya asa a abinda kika sha na karshe dan ya zama shaidarmu ta biyu, yanda kowa yasan ita da iyyenta ba ƙaunarku suke ba tuni za’a yarda wlhy”.


Siyyah Woow gaskiya wannan shawaran yayi Sima. Shiyyasa kike birgeni, dan kuwa na tabbatar wannan maganar bazata zama ta wasaba. Maybe ma a kanta har sai iyayen Shareff sun maidata inda ta fito”.
A hankali Fadwa ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi, jin motsin kamar za’a shigo ya sata ajiye wayar da sauri ta zame ta kwanta tana fidda numfashi ɗaɗɗaya.

★Kamar yanda suka shirya ɗin hakance ta kasance. Dan kuwa bayan dawowar Khaleel Doctor yake sanar masa bayanan bincikensu akan zubewar ciki. Hankalin Khaleel ya tashi a take ya kira Daddy a waya ya sanar masa. Cikin ƙanƙanin lokaci magana taje kunen kowa daya dace, dan haka daga asibiti gidan su Shareff aka wuce da Fadwa. Anan su Gwaggo suka tirketa da tambayoyi.

Faɗa musu tai ita wlhy bata sha komai ba dan cikin ya zube. Daga dai gama shan lemo cikinta ya kama ciwo shine tace Aysha ta rakata asibiti, suna kuma zuwa Doctor yace cikin na barazanar zubewa. Yay mata allurar kariya daga hakan amma sai ba’a dace ba. Kan kowa ya kulle da zancen, daga ƙarshe Abbah ya tambayi su nawane a gidan.


Cikin kukan da take faman sharɓa ta sanar masa su huɗu da mai aiki sai maigadi a waje da Khaleel da sai dare yake zuwa, da safe kuma ya fice. Babu ɓata lokaci aka tattaro kowa har maigadi sai kulle gidan yayi. Su Anam dama daga wajen aiki nan suka yo. Kafin kowa yace komai Gwaggo Halima ta fara zazzaga masifa akan bazata yarda ba, duk wanda ya salwantar mata da jika sai inda ƙarfinta ya kare, Hakama Mommy sai kumfar baki take. Itako Gwaggo sai ta saka kuka tana kafe Anam da kallo…


Hakan yasa kowa maida hankali kan Anam ɗin. Ta nuna Anam da yatsa tana sake fashewa da kuka. “Kar ku raba ɗayan biyu yarinyar nan ce ta aikata. Lallai ilallah itace da wannan aika-aikar, tunda tana ganin Mustapha ya mata nisa shiyyasa ta ƙulla wannan sharrin na salwantar masa da ɗan tayi. Kai wannan yarinya anyi azzaluma makira, dama yaya ɗan ɗan uba zai taɓa son abokin burminsa da alkairi, dama ni dai dan kar ace an hanata zuwa ne amma naji ajikina wani abu mai muni zai faru, sai dai banyi zaton mai girma irin wannan ba……..”


Abbah ya katseta da sauri cikin ɓacin rai, “Haba Gwaggo wannan wace irin magana ce haka. Yaya Anam zatai wannan babban al’amarin nawa take?”.
“Eh kace haka fa, Abubakar kasan miye mace kuwa? To mace ko ƴar kwana ɗaya ce ta wuce da saninka a fanin makirci da shaiɗanci. Idan kana ganinta karama wlhy sai ta aikata maka abinda mai ɗari bazaiyiba. Kuma idan kitsa mata hakan akayi fa…”


“Wannan dai maganar bashi da amfani gaskiya a bari dai ayi bincike. Ƙilama ita Fadwan da kanta tasha abint…..”


“A’a gaskiya Yaya kar kai irin wannan yanke hukuncin. Taya za’ai ciki na jikinta ta zubar”. Gwaggo Halima ce ta katse Daddy a matuƙar harziƙe mai maganar.. Ran Daddy ya ƙara ɓaci amma sai baice komai ba yay shiru. Abba ne ya ƙara dakatar da hargowar Mommy da Gwaggo. Dole sukai shiru aka fara yima Aysha tambayoyi. Bayan ta gama bada amsa aka juya kan Anam da zuciya tazoma wuya da kalaman su Gwaggo Halima duk da ba komai take fahimta ba saboda hausa sukeyi. Tambayarta itama Abbah ya shigayi sai dai ta kasa bada amsa ko guda ta saki kuka….
“You see! Kun gani ko. Shi mara gaskiya ai ko’a ruwa jiɓi yake. Munafuka dangin tsiya wlhy ko za’a tada yaƙi bazan yarda ba”.

Mommy ce mai maganar, dan haka Daddy ya katseta a tsawace har sai da Anam ta zabura ita da su Aysha. Fadwa ta watsama mai-aikinta harara cike da gargaɗi saboda hango tsoro da firgici cikin idanunta. Ƙyale Anam Abbah yayi ya maida hankalinsa gamai aikin dan ya fahimci zuciya ce ta tokare Anam ɗin. Tiryan-tiryan yanda suka tsara mata ta faɗa. Ko haɗiyar yawu bata gama ba su Mommy suka hargitse falon da hargowa har suna kaima Anam duka da ranƙwashi sai dai Khaleel ya fara kareta. Duk yanda su Daddy suka so suyi shiru hakan ya gagara. Dole Khaleel yaja hanun Anam suka fice da sauri. Mota ya turata ya tayar yabar gidan a guje duk da kiran da Gwaggo Halima ke masa akan ya dawo da Anam ɗin bai saurareta ba..

★Kuka take sosai har numfashinta na fisga. Yayinda Khaleel ke waya da Shareff cikin bacin rai da ƙunar zuciya. Shima daga can yana jiyo shashshekar kukan Anam ɗin. Sun jima suna wayar kafin ya miƙo mata. Ƙin amsa tai sai da Khaleel ya ɗaura mata akan kunne yana faɗin, “Yaya Shareff ne fa”.
“Malama amsa wayar ban son shashanci”. Ya faɗa da alamun ɓacin rai a muryarsa daga can. Amsar tayi, sai dai ta fashe masa da sabon kuka. Shiru bai sake cewa komai ba da alama dai yana saurarenta. Tsawon minti ɗaya taƙi tai shiru ya yanke wayar yana jan tsaki. Kanta ta cusa cikin ƙafafunta tare da sakin wayar ta saki wani sabon kukan. Ba sharrin su Fadwa ya sata wannan kukan ba. Zagin iyayenta da su gwaggo Halima keyi da aibanta su ne ke mata zafi. A hakan ma dan ba komai take iya ganewa ba musamman manya-manyan hausa. Tana matuƙar son iyayenta, bata ƙaunar a aibanta mata su. Amma tunda ta fara wayo ta fahimci waɗanda Abie ɗinta ke kira family nasa basu da wani buri daya wuce cin zarafinsa shi da Mamie da ita kanta dake matsayin ƴar su. Ta rasa mi iyayenta sukaima Mommy da Gwaggo da Gwaggo Halima haka da zafi a duniyar nan?…

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button