BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 56-60

5⃣6⃣ to 6⃣0⃣

Haka kawu iro ya badawa idon shi kasa yace sam ba za’a yiwa ya’r sa kishiya ba,,a wannan lokacin muhammadu yaji sam ba zai iya bin maganar kawu iro ba,,,saboda haka yana tashi gidan malam idrissa ya nufa abokin baban sa tun na yarin,,ya kwashe komai ya fada masa…malam idrissa tsoho me dattako yace zai shige mai gaba ayi komai,,,,,haka kuwa akayi shida wasu abokanan sa su biyu suka je nema mai auren,,,aka gama komai cikin mutunci kowa na farin ciki aka tsaida rana sati uku masu zuwa,,muhammadu yayi matukar farin ciki da hakan…A lokacin da kawu iro yaji labarin cewa yayi lallai sai ya sakar masa yarinya,,tijara ba irin wanda beyi wa muhammadu ba,,,takanas ya taka har can gidan su inda itama asabe ke zuba ruwan rashin mutuncinta….shima da yake baban nata dakiki irin ta sai ya dora daga inda ta tsaya,,yana cewa lallai sai ya basa takardar ta,,,ai asabe najin zance saki jikinta yayi sanyi dan itafa har yanzu tana son mijinta,,ba kunya ba tsoron allah asabe tace itafa tana son mijinta,,,kawu iro tunda yaji tace haka ya saba babbar rigarsa yayi waje tare da fadin to ai shikenan tunda kin zabi zama da kishiya,,,

Kwanci tashi ba wuya a wajen allah yau saura kwana2 bikin muhammadu da fatima,,,asabe tayi tijarar tayi bala’in tayi rashin mutunci amma duk a banza malamai kuwa sunci iya nasu amma duk ba nasara hakan yasa ta hakura amma ta kudirta a ranta kowa ce aka auro to kamar ta shigo makabar ta ne dan har ta gama tanadin irin rashin mutuncin da zata mata..

Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya dan kuwa a yaune mutanen kauyen kiyawa suka shaida daurin auren muhammadu salisu da fatima hamisu jauro…muhammadu sai washe baki yake kallo daya zaka masa kasan yana cikin farin ciki,,,domin shi a cikin ranshi fadi yake yanzu ne yayi auren soyayya

Ko kafin magarib tayi har ankai amarya dakinta dake gefen dakin asabe,,,,iyayen fatima sunyi kokari sosai gurin tsara mata dakin ta duk da daki ne irin kauye,,amma hakan bai hana shi yin kyau ba‘’ana gama shirya komai mutane suka fara tafiya sai ya’n uwanta na jiki,,,fatima na lullube cikin koren mayafi ba abinda takeyi sai kuka fuskar nan tayi jajir,,,,duk hidamar nan da akeyi asabe bata nan ya’ya’n ta nacan gidan su,,,ita kuma tana can bin yawon malaman ta,,,,,kan kace me kowa ya watse gidan yayi tsiiit…a lokacin ne kuma muhammadu ya shigo dakin amarya fatima ya wuce tunda yasan har yanzu asabe bata dawo,,,amarya fatima na zaune bakin gado,,kanta a kasa…da dabara sai da muhammadu yasa ta saki jiki dashi,,,ledar hannun shi ya bude tsirene a ciki wanda yaji quli da kayan miya sai turiri yake,,,,dakyar fatima taci dan ita nauyin shi takeji,,,shiko ko a jikin sa,,,haka ya lallabata,,,

wannan daren muhammadu yayi kwanan farin ciki a lokacin ji yake kamar bai taba aure ba dama,,,fatima kuwa tasha albarka dozen2,,,,

ita kuwa asabe koda ta dawo ko kallon sashen amaryar bata kalla ba tayi shigewarta dakin,,,a wannan daren asabe bata runtsa zirga zirga takeyi a dakin kamar kwancen hauka,,ji take kamar taje taita buga kofar dakin,,,,

washegari muhammadu ya tashi cikin farin ciki da kansa ya hada mata abin karya wa ya dibar mata nata ya diba na asabe ya kai mata dashi da abincin ko kallon arziki bai samu ba,,,shima bai biye mata ya fita ya koma dakin amarya fatima..

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya fatima na kokarin ganin tayi ma asabe biyayya amma ita kuma bata gani ita da ya’ya’n ta haka suke mata rashin mutunci kala kala,,,ba halin tayi magana haka zasu je kofar dakinta suyi wasa da kasa a kwaba da ruwa suyi kaca2 da wurin su kuma tashi su bar shi,,,haka asabe ke mulkinta son ranta a gidan ta wulakanta fatima yadda ranta yaso ita ya’ya’nta,,,fatima me hakuri ce koda yaushe sai dai ta shige daki tayi kukan ta ita kadai bamai rarrashinta..ko yan’uwanta sunzo bata iya fada musu,,,,ita kuma asabe bata tashi iskancin ta sai taga muhammadu bayanan .har jifanta take sa haladu yayi idan ta fito tsakar gidan,,,shiyyasa yanzu bata ma fitowan koda yaushe tana cikin dakinta,,

Ana cikin haka sai ga cikin ya bayyana a jikin fatima,,,muhammadu murna yakeyi kamar yanzun zaa fara haihuwa a gidan sa,,,,asabe kuwa ina wuta ta jefa fatima dan tsananin takaici da bakin cikin da take ciki,,,CIKI a jikin wannan ya’r mayun to wallahi wannan cikin ba zai taba zuwa duniya tayi alkawari hakan,,,mayafi ta zara tasa shafdeden silifas dinta ta fita a gidan kamar wata mahaukaciya,,,tayi alkwarin ko zatayi yawo tsirara sai ta salwantar da fatima da abinda ke cikinta,,,,

 ANYA KUWA,,,,,

Muje zuwa wai mahaukaci ya hau kura????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button