AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 27-28

??27 and 28??

Via OHW???? Jitayi anturo kofar dakin da karfi, duk inda ilahirin jikinta yake yadau rawa, tayi matukar tsorata,
Hilal yashigo yatsaya yana kallonta tana sallah, ya girgiza kai ransa a bace yaja tsaki yafita ya koma falo,

Jitakeyi kamar takarawa sallar gudu, shaf2 ta gama sallar ko adu’a bata tsaya yiba tafito falo a gigice,
Wayarta tagani a hannun hilal, ta zare ido ta zabura kamar anmata sock, tayi matukar razana, taku takeyi cikin sanda ta sunkuyar da kanta kasa,
Jin tafiyarta yasa hilal yajuyo sukayi ido hudu taga yanayinsa ya chanza, ta tsaya cak guri daya tana jiran taji mezaice
A zuci take fadan nashiga ukku yau ruwa yakarewa dan kada”
Ameela ! Hilal ya kirata,
Cike da fargaba murya na rawa ta amsa,

hilal yace “karaso nan” ya nuna mata kujera da hannunsa,
Kafafuwanta har wani rawa suke dakyar takarasa bakin kujera tazauna, ta sunkuyar da kai tana wasa da dan yatsan, gabanta naduka shida shida,

Hilal yadubeta cike mamaki ” ameelah kinbata wayonki a banza wlh, kin zalunci kanki, wane irin rudine shedan yamiki dahar….” Ameela ta katse masa magana da shakankiyar muryarta, kamar mai shirin yin kuka tace ” dan Allah dee kayi hkr wlh…”
Hilal yadaga mata hannu, idanuwansa sunyi jajir yace “banason naji komai daga bakinki, wannan laifin da kikeyi bani kika yiwaba Allah subhanahu wata’ala kike sabawa, hilal yalura da irin tashin hankalin da ameelah take ciki, hawaye suka soma sauka kan kumatunta, yadan tsayar da maganar sa yana kallonta kafin yaci gaba dacewa “meya hanaki sallah da wuriii”

Dasauri ameelah tadago kai tallesa, zuciyarta harwani sanyi tayi, tace
Dee wlh bacci nake, koda natashi time ya wuce, amma kayi hkr bazan karaba”

Ajiyar zuciya yayi ya tashi tsaye, sukayi ido hudu yace ” laifinki biyu kenan kinyi karya a yanzu kuma kinkiyin sallah da wuri, ameelah matukar kinason muzauna lfy dake a cikin gidan nan to karna kara ganin kinyi late din sallah”, mika mata wayarta yayi kafin yaci gaba da cewa “karbi wayarki naxo naga ana kira, kafin nakarasa gurin wayar kiran ya tsinke, wata number mai suna Hmm”
Cike da firgita ameelah tace ” ehhhm”

hilal yakara kallonta “eh amma bansamu daukaba koda na naxo ta tsinke”

ya mika mata wayar sannan yajuya yanufi dakinsa,

Wata irin babbar ajiyar zuciya tayi, ta share hawayen dake edonta, yana shigewa daki tadaga hannu sama “Allah nagodema “
Tana gama fadan hakan ta sauka daga kankujera ta zauna kasa. Ta janyo ledar abinci tafara budewa…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button