BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 71-75

Page 7⃣1⃣to 7⃣5⃣

 CIGABAN LABARI

Tun dawowar inna asabe daga wurin bokan ta ta kasa zaune ta kasa tsaye.domin kuwa a yaune take son ta gama duk wani mugun kullin ta a kan jiddah ta rasa yadda zatayi ta shiga dakin dabara ce ta fado mata dakin ta shiga ta dauko kudi sannan ta nufi dakin jiddah.kwance ta tarar da ita amma ba bacci take ba tana ganin shigowar inna asabe ta mike tare da fadin sannu inna ashe kin dawo,eh tace‘’sannan ta fara fadin yauwa jiddah dama so nake na aikeki gidan mutuniyar ki maman salaha ki amso min kayan na 100.

to tace sannan ta dauki hijab ta zira takalmi sannan ta fita.

fitar ta keda wuya inna asabe ta bankade er yagalalliyar katifar dubawa tayi taga ba wani rame a wajen kuma idan tasa a haka zaa gane wuka ta dauko ta samu bakin katifar ta bula sai da taga yayi zurfi sannan ta barshi ta ciro layar dake daure a habar zanin ta ta tura ciki kara komawa dakin ta tayi ta dauko zare da allura ta dinke bakin wajen sai da ta kalla dakyau ta ga ba wani alamun da za’a gani sannan tayi murmushin mugunta tace‘’jiddah na gama dake kodah wannan na barki na rama bakin cikin dana kunsa na uwarki da naki,mikewa tayi ta fice daga dakin.

AMMAR ne zaune a daki shi kadai yana hutawa yau bashi da lecture ya kara kyau ya kara fari fatar nan sai glowing take saboda hutu da amfani mayuka da alamu dai kasar india ta amshe shi,wani dan karamin passport ne a hannun shi tun dazu ya kura masa ido yana duk sanda ya kalli ta jikin hoton sai gaban shi ya fadi,wayar sa dauko domin kiran ta kamar dai ko yaushe yauma a kashe take,

wurgi yayi da wayar cike da takaici yana fadin why jiddah zaki kashe waya bayan kinsan zan nemeki.

Abbas ne ya shigo dakin tare da fadin kaga na jiddah ba da kanka asare idan aka ga bacin ranka to jiddah aka tabo.

kallon shi ammar yayi kafin ya kaude kai yana fadin saura 2 years na gama karatuna gaskiya yayi min nisa inaso insan halin da jiddah ke ciki nifa ina ji a jikina wani abu na faruwa.

abbas ne ya katse shi tare da fadin “to yanzu me kake nufi kenan?uhm idan kayi hakuri kamar fa gobene yanzu 3years kenan da zuwan ka 2years zai maka wahalan karasa,ka daina sa tunani a ranka jiddah tana nan lafiya.

kallon shi ammar yayi tare da fadin ALLAH yasa hakan.

Ba wani dadewa tayi ba ta dawo hannun rike da kayan miya dakin inna asabe ta nufa ta bata,har zata juya sai kuma ta dawo tana fadin”kawo in gyara,A’a kibar shi kawae jeki cigaba da baccin ki..

dakin ta ta koma ta cire hijabin har zata kwanta ta tuna gobe suna da test,jawo jakar ta tayi sannan ta fara duba littafan ta sai da ta kwashe kusan 1hr sannan ta ajiye ta kwanta kafin la’asar tayi.

Kiran sallah la’asar ne ya farkar da ita tana son tashi tayi sallah amma ta kasa gaba daya jitayi gabobin jikinta na saki.

komawa tayi ta kwanta tana fadin anjima nayi,

haka ya faru a lokacin sallar magrib.

inna asabe ce zaune da su rabi duk cikin su bamai kayan arziki HALADU kuma na gefe yana cin abinci.

inna asabe tace”Rabi dake da asiya ku zabar ma jiddah kaya a cikin naku amma fa duk kananu kamar dai na jikin ku din nan,to suka ce tare da mikewa dan sun riga da sun san manufar hakan..

kallan kayan take daya bayan daya sanda inna asabe takai mata kuma tana fadin wai nata ne su rabi suka bata.

amsa tayi kawai amma har cikin ranta kayan basu mata ba amm kuma ta kasa musawa….

Ur ‘s princes deejerh????
✨✨BA DON SHIBA✨✨

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button