Labarai

Nima Uwa ce Kamar Ko Wacce Uwa, Na Haifa Inada Zuri’a Kuma Yayana Suna Jin Zafi idan Aka taba Mutuncina

Nima Uwa ce Kamar Ko Wacce Uwa, Na Haifa Inada Zuri’a Kuma Yayana Suna Jin Zafi idan Aka taba Mutuncina

A wata tattaunawa da akayi da Matar Shugaban Kasar Nijeriya Aisha Muhammad buhari akan kama matashi dan Shekara 23 da tayi kan cewa yaci mutuncin ta a kafar sadar wa na Twitter.

Acikin Satin nan wannan shine labari mafi girma wanda ya karade ko ina a Shafukan Sada Zumunta, Mutane da dama nata bayyana ra’ayoyinsu kan wannan batu inda wasu suke ganin cewa Matar shugaban kasa tayi dai dai wasu kuma na ganin ba’a kyauta ba Kasancewar irin yadda aka kama yaron ya sabawa dokar kasa.

A halin yanzu dai an gurfanar da matashi aminu a gaban kotu inda kuma aka tisa keyar sa izuwa gidan Yari kamar yadda jaridar bbc hausa ta wallafa.

A zantawar da gidan talabijin na TVC news tayi da Aisha buhari ta bayyana cewa itama uwa ce kuma ta haifa saboda haka abunda akayi mata itama yayanta sunji zafin abin Kamar Yadda Kowa Yake ji idan aka taɓa mutuncin mahaifi ko mahaifiyarsa.

Kuma cin mutuncin mutane ba abune mai kyau ba ko a addinance ya kamata kowa ya san wannan.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button