WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 13

 ????WATA TAFIYAR????       Story & Written

                By

         Jiddarh Umar

????????????????????????????????

*????✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????✨*

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

 *“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“????`* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~????????~~~~~~~

PAID BOOK

                      

               13

Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank, 

Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.

Ko Katin Waya.

WANNA LITTAFIN NA KUƊI NE,IN KINSAN BAKI BIYA BA DAN ALLAH KAR KI KARANTA, KUMA KAR KI YI SHARIN PLEASE.

Ajayar zuciya ta sauke tana mai ƙarfafa ma kanta guiwa,dan bata sani ba ƙila wannan ne kawai damar da take da shi na ganin meke gudana a gidan,dan haka danna button din ta yi,ai kuwa nan take sai gashi ƙofar ta buɗe ba tare da tayi wani ƙara ba wanda zai nuna alamun akwai ƙofar a wurin,

  Tsabar yanda zuciyar ta ke harbawa da ƙarfi ya  jama gangan jikin ta rawa,alamun dai a mugun tsorace take, 

  Turus ta tsaya a tsakiyar wurin,dan wata duniya ta ganta a ciki,domin kuwa a wani corido ta tsinci kanta wanda hanya ta kasu mata kashi uku,gaban ta, hagu da kuma dama,gabaɗayan su adan ka kalle ko wanne hanya ne sambal har zuwa jikin wani bango wanda shima dole ka ƙarya kwana. 

Kallon hagun ta da damar ta ta yi,sadakarwa kawai ta yi tabi hannun damar ta,tana kaiwa ƙarshen hanyar ta kara karya kwana sai kuma gata a wani irin makeken falo mai ɗauke da ɗakunan a jire,ji ta yi kamar magana ta bayan ta, dan haka da sauri ta shige cikin labule wanda saura kaɗan tasha ƙasa kasancewar ɓata san wani daki ne a wurin ba wanda ƙofar yake buɗe,Allah ne ya taimake ta ta dafa bango sai gata a tsaye,ji ta yi ana ƙoƙarin daga labulen ai da sauri ta shige bayan ƙofa tana kallon su har suka shige ɗayan ɗakin da ke cikin wannan su uku.

Dafa kirjin ta ta yi “yau na shiga uku na kawo kaina inda za’a kashe ni a binne ni ba tare da kowa  ya sani ba, wannan kuma ina ne? Wani irin gida ne haka, me ake yi anan? Allah dai yasa ba gidan yan yankan kai nake ba,kai gwara in rufa ma kai na asiri in koma in da na fito,daganan na yi tunanin ta yanda zanbar gidan”fitowa ta yi cikin sanɗa dan kar su ji ta, har ta kai bakin ƙofa ta ɗaga labule zata fita sai kawai ta ji abu na girgiza da ƙarfi,, yayin da ta ji wani daga cikin dakin na cewa “ku rike shi, kai Haris kara ɗaure hannun da kyau,Nasir yi maza ka mai Alluran mana ka wani tsaya kamar soko”

“Yaya Ahmad idan fa muka ci gaba da mai wannan Alluran yana iya rasa tunanin shi”

“Aikin banza to me zamu yi da tunanin shi ban cin matar shi da yasa hannu a kanta tana hannun mu,,kuma a ko wani lokaci muna iya sawa ta saka mana hannu akan takardun”

“Haka ne Yaya,sai dai fa kamar ka manta mu  ke da bukatar hankalin shi,domin abin da ya mallaka mata ko kashi talatin bai ƙwashe ba na cikin dukiyar,kuma kaga kenan domin gano in da ya ɓoye sauran kadarorin dole muna buƙatar shi a raye”

Karamin tsaki ya ja”gaskiya uncle ni na gaji da wannan abin ace tsayin shekara ukun muna abu ɗaya duk mun kasa,ji irin azabar da muke gana ni shi a kullum amma yaki magana ”

Ji ta yi gaba ɗaya magudanar numfashin ta ya to shi,yanda kasan me cutar Asma,kuma ba Asman bane tsabar tsorata ne kawai ya haifar mata da toshewar numfashi,dan mutum ne sanbal kwance kan gado irin na marasa lafiya,an ɗaɗɗaure shi da belet saboda wani irin girgiza da yake yi,haka kuma kanshi manne da wasu irin igiyoyi waɗanda ke jone da wasu kalan na’ura,sai Mama dake tsaye a kanshi, sai Haris wanda dama ta waye shi,sai su kawunan shi”waiyo Allah me wannan,waye wannan me kuma suke mishi,me suke nufi akan dukiya,ji ta yi gaba ɗaya kanta ya cushe,dan haka da sauri ta juya dan barin wurin,sai dai cikin rashin sani ashe ta taka dogon rigar dake jikin ta, wanda sanadin zaburan da ta yi da ƙarfi dan barin wurin ya haddasa mata tadiyewa sai gata ta faɗi ƙasa,dan ihu ta yi na jin zafin faduwar da ta yi a kan ɗan yatsan ƙafarta ya lanƙwashe,cije baki  ta yi da sauri ta na tashi dan barin wurin,,dan tunu ta ji suna ƙoƙarin fitowa sanadin jin muryan mutun da suka yi, sauri-sauri gudu-gusu haka take tafiya dan barin wurin,sai dai duk yanda ta kai ga son yin sauri ƙafar ta ta mata cikas,saboda irin azaba da raɗaɗin da yake mata.

Kafin ta kai ga lungun da zai sa da ta ga babban corido sai ji ta yi an fincikota da ƙarfi,juyowa ta yi da sauri dan ganin wanda ya janyo ta,sai dai kafin Idanunta su gama dai-daita akan ta,sai jin saukan tawayen mari ta yi a bisa kuncin ta hagu da dama, wanda hakan ya tilasta mata yin ihun da bata shirya ba,domin jin irin raɗaɗin da fuskar ta ke yi. 

Jawo hannun ta  ta yi da ƙarfin tsiya “zo mu je munafuka,dama tun da na ganki naji ina kokon to a kanki,ashe ma kuwa gaskiya ne”har gaban su Uncle ta kai ta da ƙarfin tsiya ta dukar da ita a gaban su,duk tsaye suke a babban falon” Yallabai ga munafukar na kamo”

Basuma gane taba,,duk da irin hasken da falon ke dashi, kasancewar wurin tamkar da rana,”wacece wannan? Cewar uncle Ahmad. 

“Amaryar da aka kawo ne”

“What” Har suna haɗa baƙi wurin faɗa.

Haris ne ya je gaban ta ya tsaya yana ƙare mata kallo, yayin da take gurfane a gabansu. 

Wai dama haka mutun kan tsinci kanshi a ciki idan tsoro ya yi tsoro,dan gaba ɗaya ji ta yi zuciyar ta ta daskare sai wani irin kuna da suya take,gashi ji take kamar numfashin ta zai fita ya bar gangar jikin ta,ita kam yau shikenan ta san ta kawo kanta mahallaka,wannan wani irin tsautsayi ne haka ya ritsa da ita. 

Jin muryan Haris ta yi a kanta wanda sai da ta firgita “me ya kawo ki nan,ta ina kika shigo? 

Ganin yanda ta ƙara gigicewa yasa ya daka mata uban tsawa wanda sai da falon ya amsa,hakanne kuma ya ƙara rikitar da ita,

Cikin fitar haiyaci ta ce” Dan Allah kuyi haƙuri ku mai da ni  gida”

Cikin hasala uncle Nasir ya ce”yau ga ahashasha,,a tambaye ki abu daban, sannan ki bamu wata amsar da ban”

“Wallahi ni banga komai ba,ina ɗaki ne shi ne naji muryan ku na kuma biyo ku,har naga kun shigo nan,shine nima na shigo saboda ban taɓa ganin kofa haka ba”

Bige mata baki ta yi da ƙarfi, wanda nan take sai gashi ya bare da jini “ƙarya take munafuka”

“Ya isa haka Talatu,maza daga ta ki kaita can dakin da mijinta yake ki daure ta ita ma,sai dai saman kujera zaki daure ta”

“To Yallabai”ƙara  janta ta yi da ƙarfi,yayin da ta kwalla ƙara saboda fama ƙafar ta data yi” Waiyo Allah na,Innalillahi wa’inna’ilaihi rajiun,dan Allah ki yi haƙuri ki sake ni,waiyo kafa na na mutu na lalace!shi kenan zata kashe ni, Nanne!Nanne!waiyo Baba na kazo ka taimake ni!”tana mai fashewa da wani irin kuka wanda yake fitowa tun daga zuciyar ta  ya na ba gangar jikinta, dan nan take ta ji jikin ta ya dau zafin dole na zazzabin lokaci guda, wanda tsabar tsoro da fargaba ne ya haddasa mata shi nan take. 

a haka ta jata ba tare da ɗigon tausayi ba har cikin dakin,daurata ta yi saman wani kujera dake fuskantar gadon da yake kai, daure ta ta yi, irin darin nan wanda ko ya ta motsa sai ta ji kamar kara tamke ta ake yi, kasancewar kuma Mama Talatu irin waɗannan manyan matanne,waɗanda  za ka gansu ga kiba ga tsayi ga ƙiran ƙarfi, to haka take. 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button