FITAR RANA 12

FITAR RANA 12
Bilti tana ficewa a dakin wasimé tabi ƙofar da wani irin tsoratacen kallo nannauyar ajiyar zuciya ce ta kufce mata jin ko ina ajikinta yana sacewa gabobinta duk sunyi sanyi da feelings na mummunan fargaban za’a hanata jin dadi…
Tsillin Hawayen tsoro da fargaban za’a iya rushe mata farincikinta da zumudinta na tafiya yawo tare da saheeb dinta shiya shiga cirke mata zcya,ahankli ta runtse idanuwanta snn ta fashe da wata kufulallen kuka harda shesheka.
Idanunta a rufe suke gam gam hawaye sharkaf akan kumatunta tashiga yarfa kafa da hannu cikin kuka sosai tace..”Yo nifa wallhi bansan na fadi haka ba”…yanzu sai yaji haushi na ko?dan kawai nace mishi maye yo
Inhi ba maye bane ai maganar baxata darashi ba…
kuka ta cigaba dayi cike da fargaba aranta tamkar wanda akacemata har ankai maganan kunnen taheer, ahakan da kyar ta iya kwantar da hanklinta snn taje tayi wanka.
Bayan ta shafa mai Wani zugummm tayi ta neme waje ta zauna agefen gadon su snn ta rabza wata uban tagumi.
Duk abun duniya ya isheta,haka take sumtimes tana da muguwar anxiety Allah ya zuba mata tsoron taher bakadan ba,har cikin ƙashin jikinta take jin matsanacin tsoron TEJ tasan kuma in yace bazataje koina ba tofa shikenan ya wuce mata kenan har abadaa,ga bilti ma shiru batako leko tace mata tazo tay break fast ba…tasan hala itama fushi tay da ita.
Jiki a sanyaye ta tashi,Sabbin kayantan ta hau sakawa golden atmfa wax ce mai kyau yar dubu goma kalar golden yellow an mata peplum blouse da 4pieces skirt wanda yay mata cas cas
Dan kwalin kawai ta kifa akanta bata tsayayin wani kwalliya ba, kajol dinta ta shafa da dan man baki kawai ta sauƙo.
A hankli take tafiya kamar wanda ruwa ya kwasota, Hanyar Kitchen ta nufa direct tana takawa ahankli cikin sanda yadda
Ko motsinta ba aji harta sauƙo,samu tayi bilti na waya ga tarin wanke wanke agabanta ,a gefe taja tsaya tay shiru kamar wata mareniya tana kare mata kallo.
Bilti tana kammala wayar ta juyo suka haɗe ido cikin sauri tayi saurin kauda kanta gameda mayar da idanuwanta can ƙasa ta cigaba da kallan tiles batace uffan ba. Babu yabo babu fallasa Bilti tace
“Hm wasimé harkin fito ?To ki taho kixauna acan ga abincinki akan table dama ynzu nake shirin zuwa ƙirarki kar abincinki ya huce…
Caraf ta dago kai da muryan kuka sosai cikin kukunin daya gama shake mata wuya tace”Wallhi ƙarya kikeyi”Babu ƙirana da zakizoyi.Makaryciya kawai…
A mugun raxane bilti ta aje plate din dake hannunta snn ta juyo ta kalleta sai taga kuma tana sauƙe hawaye sosai.
Ɓata ranta tay sosai itama cikin daka mata tsawa tace”Wasime
nice yau kuma nakoma makaryaciyan ki?Ke
Añya na taɓa dukanki kuwa?to wallh kinyi na karshe kiƙara wani rashin da’ar anan zakiga abunda zan miki maza Tattara abincinki kiɓacemin anan tunda ke bakiji.
Jikinta na bari ta karaso kan table dib dan Ɓata taba ganin bilti ta bata ranta har haka ba sai gaba daya abun ya ɓata tsoro,kuka takeyi awajen rungume da bangon wajen kamar wani anbugeta.
shareta bilti tay kamar bata wajen ta cigaba da wanke wankenta kamr bata sanda ita ba while a zahirance Xcuyarta cike yake da tunani kala kala akan sauyawar halayyar wasime,ita dai tasan datazo ba hakan take ba sam sam.
Bataso ta ayyana abun aranta ne kawai, amma zcyarta yana lazimin cewa a sanadin tarayyarta da saheeb ne halayyarta yake kkrin sauyawa.
Sau babu adadi tana dan lura da cewa kamr saheeb ne yake cusama wasime wasu tambadadun ra’ayoyi da manya manyan maganganu wanda baidace ace tana furtawa ba.
After like 10mins sai ga sallama a kofar kitchen din,saheeb din ne ya shigo yana mai furta “salama alaikum” tundaga bakin kofar waje
Yana murmushi
Wa alaikisalam
Bilti ta amsa da sakin fuska,but ganin har ya maida kallonsa akan wasime data kama bango tana rabza uban kuka yasata dauke kanta akansu ta cigaba da abunda ke gabanta.
Gabaki daya wasime ta susuce tayi wani fayau idanunta har sun soma haurawa sabida tsabar kukan banza..arayuwa dan tayi kuka akan komi bakomi bane,ita sam kuka baiya mata wuya shiyasa ma bata gajiya da yinshi inta fara.
..’har gabanta saheeb ya matso snn ya tsuguna yana kallonta Sheshheka mai zafi takey Tanajan numfashinta sama sama da kyar,yana kaiwa daidai tsayinta ta wani jaa ajiyar zgiya snn ta rungumesa ta saka sabon kuka mai cike da sakalci da shagwaba
Rarrashinta ya shigayi yana dan mulmula mata bayanta,kwayar idanunshi atake suka nuna alamar baiji dadin tsintar a wannan yanayi ba,Yace”toh kiyi shiru mana wai waya taɓaki ne? Bata amsashi ba ya dauketa cak ya rabata da ƙasa tare da jijjjigata snn yace “meye?…idanunta tahau mutsukawa tana share hawayen cikin zafin sheshheka tayi nuni da bilti…
Dan shiru yay yanakan jijjigata, can snn ya kalli biltin yace bilti kunyi fada da mutuniyarki ce?
Bilti Tana kan wanke wankenta batare da ta juyo ba tace mishi”..
Eh,bataji ne..rashin kunyarta yafarayin yawa.
Dan Murmushi yay snn ya Sauƙeta a kasa ya riko hannayenta anashi yana dan murzawa a memakon ya tuhumeta saiya nuna mata shima baiji dadi ba,can ya dubi biltin yace…”toh ayi mana afuwa bilti..insha Allahu bazata ƙara ba.
Suna cikin hakan saiga sassanyar sallamar taheer akansu,,a nitse ya shigo jikinshi sanye da wata dark brown jallabiya mai guntun hannu,wani mummunan haɗe rai saheeb yay ya dauƙe idanunsa akansa basuce ma junansu uffan ba kowa ya hade rai yana shan qamshi
,saheeb ya miƙe tsaye tare da tura wasime ahnkli”Beauty na Jeki kibata hakuri saita shiryaki inkin gama sai kizo kisameni a mota mutafi ko?”
..kallonshi ta dingayi tana sake boyayyr ajiyar zcya kafun ta gyada masa kai,murmushi yy ya shafa kanta baice ma kowa komi ba yasa kansa yay waje.
Taɓe baki taheer yay yana shirin dauke kansa daga bakin kofar kenan yaji dirar tsiririyar muryanta a raƙube a gefenshi ta tsaya kusa da inda yake,cike da tsoronsa ayanayinta tace…”Ina kwana? kanta na kallan ƙasa..shiru yy abunshi,ya dade yana kallonta kamar wanda ya mance wani abu ajikinta can snn ya amsa gaisuwar ciki ciki snn ya wuce gaba ya samu bilti
A hkli,kuma a cikin nitsuwa yace
Bilti,juyowa tayi ta kallesa sai suka haɗe ido kowannen su yana sakar murmushi,ajyar zcya taga ya sauƙe snn yace
“pls can u see me in my room before i leave!da akwai abunda nakeso mudan tattauna akai ne nd ive got jist 30 mint to get ready..
Dan murmushi tay
Sannan tace insha Allah
Zanzo.Baice uffan ba yay nodding head dinsa snn ya juya ya fita tare da haurawa sama can dakinsa cikin gaggawa.
Wasimé data gama kallonsu har suka kammala maganan su taga babu wanda ya kulata wani shiru tayi ganin bilti ta bala’in shareta batace mata uffan ba haryanzu.
Cikin rasa nayi da tunani irinna yara ta juya ta tafi daki batare da tabada hkrin ba,tana shiga gaban madubi ta soma nufa ta caɓa dan karamin kwalliyarta ta kammala sako kayanta tsaf snn ta fito..balaifi tay kyau abunta.
Ahnkli take tafiya tana waige waige sabida fargaban datakeji acikin ranta sosai,koda ta sauƙo saida tayi tsayuwar mintina biyar abakin ƙofar kitchen manne da bango cikin rasa abunyi,duk tinaninta yadda zata soma budan baki tabawa bilti hakuri.
Aganinta Itafa simple magana tafada batasan abun zaikai har haka ba.
Daga ce mata tay ƙarya shine zata hau dokin zuciya..kai biltin nan akwaita da fadin rai..kai duka yan binni ma haka suke..abu kadan kayi saisuyi ta fushi dakai.