BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 73

73*

………Innalillahi…. Kawai yake jerawa a cikin zuciyarsa har ƙarshe. Ya kafe Mommy da Gwaggo da idanu ko ƙyaftawa bayayi.
“Katashi kaje kar magriba tayi, gashi kace gobe zaka koma aiki kana da buƙatar yin wasu kimtse-kimtse. Dan bana ma son Daddynku ya dawo ya ganka a gidan nan”.
Kansa kawai ya iya jinjinawa, ya miƙe jiki a saɓule ya fice idonsa har wani yaji-yaji yakeyi. Da farko maganar Fadwa ta zubar da ciki ce ta dakesa. Sai dai maganganunsu na gaba sun goge na farko dan a ganinsa Gwaggo ta kawo zancen Fadwa ce ta zubda ciki domin baƙantata su sami damar shigo da zancen auren Bibah, amma kuma zuciyarsa taƙi daina masa wasiwasi. Bashi da wani ra’ayin zama da mata ko biyu tun ful’azal. Sai dai ƙadararsa ta zama haka. A yanzu kuma bayajin duk wuya duk rintsi zai iya rabuwa da Fadwa da Anaam. Dan kowacce da irin kalar soyayyar da yake mata a cikin zuciyarsa. Yama rasa ina zai kama ya riƙe ne a zancen nasu……
Koda ya shigo gidan tsabar yanda zantukan su Mommy suka rikita masa lissafi baibi takan kowa ba tsakanin Anaam ɗin mai karbar girki, da Fadwa mai fita. Kai tsaye sashensa ya nufa. Sai bayan sallar magriba mmn abu ke sanarma Fadwa kamar fa taga motar Shareff. Da mamaki tace “Yaushe ya dawo gidan ban sani ba?”.
“Inaga lokacin kina ciki ne kina wayar nan”.
Ɗan jimm Fadwa tai na wasu mintuna, sai kuma ta shiga bedroom ta dan karo turare ta fito. Kai tsaye sashen nasa ta nufa. Cikin taɓe baki take bin ko Ina na falon da kallo tana mai shaƙar daɗaɗan fresheners da Anaam ta baza ko’ina tare da turaren wuta. Bedroom ɗinsa ta nufa dan baya a falon. Fitowarsa a wanka kenan, ya juyo yana kallonta. Taku take cikin gayu da yanga, sosai kwalliyar tata ta fita da ƙyau dan ko makaho ya shafa yasan ita ɗin gwanace wajen zaman zanawa. Ji yay kaso ashirin bisa ɗarin damuwarsa sun ragu. Ya sauke numfashi a hankali tare da buɗe mata hannayensa alamar tazo gareshi. Da sasaarfa ta karasa ta shige. Suka sauke ajiyar zuciya a tare. Sumbatar gefen wuyanta yayi, muryarsa a sanyaye ya raɗa mata “Kinyi ƙyau Babie na”.
Ajiyar zuciya ta saki da murmushi, ta ɗago tana mai kallonsa, sai kuma ta manna masa kiss a ƙirjinsa. “Nagode Soulmate barka da dawowa”.
Kansa ya jinjina mata, ya kai hannu ya ɗan shafi fuskarta. Murmushi ta sakar masa da janye jikinta a nasa. Baice komai ba ya karasa gaban mirror domin shafa mai. Itama sai takai zaune a bakin gado tana faɗin, “Kayi wani iri kamar mai damuwa. Ko wani abu ya faru ne?”.
Ta cikin Mirrorn ya kallota. Ya ɗan fesar da numfashi a hankali. “Babu komai na gajine kawai”.
“Ayya kona maka tausa?”.
“A’a karki damu nagode wannan aikin ƙanwarki ne ai ko”.
Har cikin rai taji zuciyarta ta sosu, amma saita danne tai ɗan murmushi da mikewa. “Uhhm hakane na shafa’a ne kawai. Kasan idan ina a tare da kai mantawa nake da komai da kowa kai kaɗai ɗin kawai nake iya gani”.
Murmushi yayi mai sanyi yana mai kallonta ta cikin mirror ɗin. “Ngd ƙwarai da gaske Sweety na. ALLAH ya barmu tare har abada”.
“Cikin matuƙar jin daɗi tace amin”.
Itace ta taimaka masa ya shirya, ta rungumesa bayan ta feshesa da turare. Lips dinsu ya haɗe waje guda yana mai mata wani irin fresh kiss da ya nema zautar da ita. Sai da ya tabbatar ya samu wata nutsuwar sannan ya barta suka koma sauke numfashi. agogo ta kalla zuciyarta na raunana ganin lokacin fitarta girki yayi. Dan kuwa ya tabbatar musu daga 6 na yamma ne. Jitai inama ta jawo mintunan su koma baya, dan wata irin matsananciyar buƙatarsa takeji saboda ya sakata a cakwakiya. Sanin komai zai iya faruwa ta fita da sauri tana faɗin tana zuwa. Murmushi yayi har hakwaransa na bayyana ya bita da kallo……

  Anaam da bata san da dawowarsa ba ta fito a toilet daga yin alwalar sallar magrib ya shigo. Sannu da zuwa ta masa. Idanunsa kafe a kanta ya amsa mata. Sosai itama tata kwalliyar ta wuce da nasa imanin. Yaji daɗi har cikin ransa ganin yanzu tana kwalliya. Shiyyasa ya hana Aysha wucewa dan yasan koba komai zata taimakama Anaam ɗin da abubuwa masu yawa da bata gama sani ba a irin rayuwar Nigeria.
  “Haka ake tarbar miji dama?”.

“Kai yaya alwalafa nayi”. Ta faɗa murya a karye. Murmushi ya saki yana matsota. Ta matsa da sauri zata koma toilet. “Nidai ALLAH karka karya mun alwala”. Dariya yayi da yin ƴar ƙwafa ya juya ya fita. Itama saita sauke ajiyar zuciya dan ta san kaɗan daga aikinsa yace zai shanye jambakin dake a lips ɗinta.

Bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i. Kai tsaye kuma sashinsa ya nufa, inda ya iske har an shirya abinci a dining. A falon ya zauna yana sauke numfashi da ƙoƙarin kunna television, so yake ya kauda duk wani damuwarsa domin more wannan daren. Kusan mintuna sha biyar da zamansa babu Anaam babu labarinta. Dan haka ya dauka waya yay kiranta. “An barni ni kaɗai kamar maraya”.

Murmushi tayi da har yaji sautinsa a kunensa. “Immhum ni ai bansan ka dawo bane ba fa”.
“Okay, ai yanzu kin sani”.
Min tuna kusan bawai tsakani sai gata ta shigo, tun kan ta iso ƙamshinta ya karaso. ya rasa a matan nasa wacce tafi wata iya gayune. Duk randa sukejin abin arziƙi susutashi sukeyi gaba ɗaya. Ta bayan kujerar ta tsaya, tare da ranƙwafowa kansa ta manna masa kiss a wuyansa. Numfashi yaja mai yalwa tare da fesarwa. Ya kamo hanunta ya zagayo da ita ya zaunar a cinyarsa. “Irin wannan wanka ai sai ki sakani manta kaina autar mata”.
Murmushi tai da ɗan tabe baki, “Ban san daɗin baki ni dai Yaya”.
“Kinfi ƙarfin daɗin baki ai a wajena. Duk abinda bakina ya furta a kanki shine ai nahin gaskiyar zuciyata”.
Sosai taji daɗi har cikin ranta. Amma dai batace komai ba sai murmushi kawai da taɗanyi. “Yau dai lipstick ɗin nan nawane ko?”.
“A’a”.
“Ashe zan miki kuka”.
Dariya ta sanya tana mai lafewa a jikinsa. “Oh oh ya kaga Yaya ana kuka”.
Murmushi yayi mai faɗi da lakace hancinta. “Wato harma hasasowa kikeyi ko”.
“Sosai ma”.
“Uhhyum mugunta.com”. Yay maganar da kaima lips nata kiss. Bai bari ta shaƙi numfashi ba ya maida lips ɗin nasa kan nata again. Sai dai a yanzu salon dabanne dana farko, dan sai da ya shanye lipstick ɗin tas hankalinsa ya ƙwanta. Lamo tai a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya a hankali. “Tsadar tsada ke ta musamman ce”.
Muryarta a dashe tace, “Ai kaima ɗin na musamman ne”.
Ido yake son su haɗa amma taƙi yarda. “Please ki kalla cikin idona ki faɗa Noorie”.
Murmushi tai da juyowa kamar zata kallesan, sai ta mike zumbur daga jikinsa. Kamota yay yunƙurin yi ta zille tana dariya. “Biyu kenan fa, idan kika bari na kamaki zakiji jiki”. Gwalo ta masa da nufar dining. Ya murmusa cikin jinjina kai.
Waya ya ɗauka yay kiran Fadwa. Cikin murya ƙasa-kasa yace, “Babie kizo muyi dinner”.
“Uhm-uhm”. Ta faɗa a shagwaɓe.
Ɗan kallon Anaam yay, ganin hankalinta ba kansa yake ba ya sake ƴin ƙasa da muryar cikin lallashi. “Why”.
“Nifa bana jin cin komai”.
“Idan kika bari nazo da kaina akwai hukunci kenan”.
Dariya tayi da ga can. “Naji zanzo”. Shima sai yay murmushi da faɗin “Matsoraciya”.
Juyowar Anaam dai-dai yana ajiye wayar. batare data fahimci mi yayi ba ta ɗaga masa yatsu biyu. “Hy Yaya abinci na jiranka”.
Fuskarsa ya dan marairaice. “Kin yarda zaki bani da kanki?”.
Ɗan jimm tai na tunani, sai kuma ta kaɗa kanta alamar eh.
“This is for you my Noorie”.
Ya faɗa yana mai kissing hanunsa ya hura mata.
Dariyar da tafi kama data mugunta ta sakar masa. Ta tare kiss ɗin tana mai lumshe idanu da mannawa saitin zuciyrta. Rungumeta yay sannan ya kai zaune a kujer data ja masa baya. Dai-dai nan Fadwa ta shigo. Koda suka kalla juna ita da Anaam sai kowa ya watsar da ɗan uwansa. Sai da ta karaso ta zaunane Anaam ɗin tace, “Barka da yamma”. A takaice itama Fadwa ta amsa da “Barka”. Sai kuma ta ɗan saci kallon Shareff ta sakar masa murmushi. Murtani ya mayar mata ya ɗauke kansa.
Anaam daba lura tai da su ba tana ta ƙoƙarin zubama kanta abinci, koda ta ɗago sai suka haɗa ido itama da shi. Murmushi suka sakarma juna. Nanma ya kauda kansa batare da Fadwa ta gani ba dan itama ta maida hankalinta ga zuba nata abincinne. Yau ne kuma karon farko da Anaam ta fara girki a gidan, duk da dai tayisane da taimakon Aysha dan bata iya girke-girken Nigeria ba sai ƙalilan a ciki. Saukinma zuwa yanzu ta iya cin abubuwa da yawa ba kamar farkon zuwanta ba.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button