BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO….. 12

       Bayan ficewarsu Aunty Mimi bin bayan Anam tai. Ganinta zaune tana kallon su Aysha daketa faman shiryawa ta korata itama tai wanka. Ta kuma tabbatar mata idan har ta sake shigowa ta ganta bakamar kowaba saita ɓata mata rai matuƙa. Babu yanda ta iya dole tabi umarninta, su dai su Aysha sai faman dariya suke. Bata kulasuba ta shiga tai wanka, ta fito ta shiryawa a ɗaya daga cikin kayan fitar biki da su Daddy sukai musu. Sai dai kalar nata daban tasa saɓanin ƴan uwanta da duk suka saka atamfa. Sosai lass ɗin yamata ƙyau kasancewarsa skirt da riga kuma bata saba sakawa ba. Tai ɗas abinta kamar itama amaryar ce (Anam team????).


        Alhamdulillahi bayan idar da sallar juma’a dake massallacin juma’a na anguwarsu ɗunbin al’ummar musulmi daga sassan daban-daban na Nigeria da wajenta suka shaida ɗaurin auren Al-Mustapha Muhammad Shareff da amaryarsa Fadwa Sadiq Dakata akan sadaki naira dubu ɗari biyu. Ɗaurin aurene daya tara manyan mutane masu alaƙa da ango da iyayensa harma da ɓangaren amarya.
        Kamar yanda nan gidan su  Shareff ke cike da ƴan uwa da abokan arziƙi acan gidansu amarya Fadwa ma hakane. Taci ado na faɗa aji daya amsa suna ado irin na amare ƴan ƙwalisa masu ji da lokaci (????????Sai dake tawan????????). Tana tsakkiyar ƙawayenta daketa aikin zuba hotuna da videon ɗorawa a tiktok. Tun kafin yau amarya Fadwa ta roƙi angonta da zarar an ɗaura aure ya taimaka ya kirata ya fara sanar mata da kansa. Da farko bai amsaba, sai dai yanda ta dinga nacin damunsa da maganar tsahon lokaci yace zaiyi. Shi mutum ne dabai ɗaukar alƙawari bai cikaba, sai dai hakan ta kasance bisa akasi. A yanzun ma harya shafa’a alƙawarin ya faɗo masa a rai. Yana tsaka da gaisuwa da abokansa yay excusing kansa ya koma gefe yana mai ƙoƙarin cikawa. Ga amarya Fadwa kam harta fidda rai zuciyarta sai faman kaikawo take kamar ta fasa kuka. Ta riga ta gama shiryawa da ƙawayenta domin jiran wannan lokaci, sai dai shiru kakeji sun fara jin kishin-kishin na cewar an ɗaura auran. Dama tasan itama gangancine kawai, Shareff ba irin mazan da ke ɗaukar kowane kalar shirme bane, hasalima ita har yanzu bai san tana harkar yanar gizo ba, da tana da tabbacin sai sun kwashi ƴan kallo da shi…….
      Ring ɗin wayarta ya katse mata tunani, tamkar maijin tsoro ta ɗauka wayar tana dubawa badan ta saka ran ganin shi ɗin bane. Kasa ɗagawa tai har sai da babbar aminiyarta Sima ta ɗaga mata tasa a hansfree dan sunada tabbacin abinda suke zaman jiran ji ne daga angon dama. Sassanyar muryarsa data ratsa cikin wayar ta saka ɗakin ƙarayin tsitt, masu video recording na faman ɗauka. Cikin rawar murya ta amsa, dan haka kawai taji kuka ya taho mata batare data san dalili ba. Daga can yay murmushi saboda jin yanayinta, ashe da gaske aure yaƙin mata ne, dan yasan abinda zai saka Fadwa karaya ba ƙarami bane. Yay ɗan gyaran murya da sake kwantar da murya. “Habibtie kin zama Matar Al-Mustapha, ina roƙon UBANGIJIN daya nufemu da ganin wannan rana ya bamu lafiya da zuri’a masu albarka, tare da haƙurin zama da juna, mai cike da kulawa da soyayya na har abadan. Finally Al-Mustapha ya zama naki”. Kalamansa sun ratsata daga ita har ƙawayenta da abun yay matuƙar burgesu, sai kawai ta sakar masa kukan da taketa faman haɗiyewa. Murmushi yayi, da sake faɗin, “Congratulations once again dear, i love you”.
       “I love you too”.
Ta amsa masa da sake fashewa da kuka. Gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki wani irin ihu da sowa harda masu guɗa. Jama’a dake waje kuwa har ture juna ake wajen son shigowa aga mike faruwa.

      Cikin ƙanƙanin lokaci video ɗin da ƙawayenta suka ɗauka suka ɗaura a tiktok, istagram ya fara yawo fiyema da yanda sukai zato ko tsammani a kowane shafi na sada zumunta kamar yanda sauran hotunan da suketa ɗaurawa na sauran kwanakin ke yawo dama . Wanda ma followers ɗinsu basu kaiba tuni ƙaruwa suke. Comments da like kam ai bama a magana. Ƴammata sai alwashi ake ɗauka da zuwan tasu makamanciyar wannan rana. Wanda ko bikinsu ke shirin zuwa next week dama cikin satin tuni sun fara neman angunan nasu da ƙawaye yanda zasu tsara nasu suma. (Hummm media-media gidan kashe ahu????).

      ★★★  

   Daga wajen ɗaurin aure gayyar abokan ango da abokan su Daddy dama sauran jama’a suka ɗunguma hall ɗin da aka shirya walimar cin abinci domin su. Anci ansha anyi hotuna kafin ango da tawagarsa su nufo gida. Yanzun kam sai da suka fara shiga gidansu yakai kansa ga Mommyn sa. Rungumesa tai cike da farin cikin yaronta ya zama babban mutum yau burinta ya cika. Ƴan uwa da abokan arziƙi nata tayasa murna da masa fatan alkairi. Anyi hotuna shida dangin Mommy dama sauran jama’a har da wanda ke a tsakar gida na kusa. Daga nan gidan su Anam suka nufa da gayyar abokansa tunda dama nan ne masaukin nasu, Mamie kuma tama sake shirya musu wasu abincin anan dama.
       Nan ɗin ma gidan cike yake da ƴan uwa da abokan arziki. Shigowarsu ta saka wasu fara sakin guɗoɗi, yayinda maroƙa keta aikin kirari na al’adar biki. Su Aysha da duk suke zaune a harabar gidan suma kan kujerun roba da aka zube miƙewa sukai cike da farin ciki suka nufi Yayan nasu dan tayasa murna suma. Anam dake faman latsa waya duk hayaniyar da ake gidan batako ɗaga kanta ba taja siririn tsaki, tare da gyara zamanta dan babu alamar zata bisu.
       Har aka fara ɗaukar hotuna bata  ko kalli sashen da suke ba. Sai ma mikewa tai da nufin barin wajen taji an riƙo hanunta. Juyowa tai a fusace da tunanin cikin su Amrah ne, sai tai arba da aunty Mimi. Baki ta tura idonta na tara hawaye, aunty Mimi ta girgiza kanta da faɗin, “ALLAH ya shiryeki Mamana”. Hanunta taja har cikin taron, ta kaita har gaban Shareff ta tsayar.
      Ƙoƙarin haɗiye hawayen dake son zubo mata ya hanata iya ɗagowa ta kalli kowa take, ga idanu tanaji a kanta da maganar da aunty Mimi ke mata akan ta ɗago mai hoto zai ɗauka. Aunty Mimi zata ƙara magana Shareff ya girgiza mata kai, tare da yima camara man ɗin nuni daya dauka kawai. Aiko ɗaukar ya farayi abinsa, bayan an musu su kaɗai kusan kala uku mutane suka fara shiga, daga haka aka cigaba da ɗauka batare da ko sau ɗaya Anam ta kalli camara ba. Daga ƙarshe ma ƙoƙarin zame jikinta a wajen ta shiga yi dan kukan da take dannewa ƙoƙarin fin ƙarfinta yakeyi. Taku ɗaya tai taji an riƙo hanunta, cak ta tsaya, tare da juyowa da sauri zuciyarta na ƙara zuwa wuya. Ɗaukewa numfashinta ya nemayi a dalilin shigar idanunta cikin nasa, ya kuma sarketa da su da iyakar ƙarfin ikonsa. Ga hanunta har yanzu yana riƙe a cikin nasa. Tuni camara man ya maida hankalinsa a ɗaukarsu hoto. Ƙoƙarin janye hanunta tayi ya hana hakan, ga idanunta ma sun gagara fita a cikin nashi. Hawayen da take maƙalewa ne suka silalo a fuskarta a hankali, ta fisge hanunta da sauri tabar wajen harda ɗan haɗawa da gudu. Waɗanda hankalinsu ke kansu duk suka bita da kallo kamar yanda shima ya bita har sai da ta ɓace. Ido suka haɗa da aunty Mimi yay saurin ɗaukewa shima yana barin wajen……….✍

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button