BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 20

        Dawowar ƴan kai kaya da saka rana ta sake baje labarin cikin Fadwa a gidan. Kowa sai sambarka da fatan saukarta lafiya yake. Gwaggo harda ƴar rawarta. Shi dai Shareff tuni yama bar musu gidan, sai yamma ya dawo suka fita salla da su Daddy. Bayan sun dawo ma tare da su yaci abinci. Ya ƙara tattauna batun tafiyarsa da su, daga karshe suka sakko masa zancen matarsa fa? Nan zata dawo da zama ko gidansu tunda dama ba daɗin jikinta take ji ba dan suma labarin ciki har yazo musu.
      Ajiyar zuciya ya ɗan sauke. Kansa a rissine yace, “Da dai tayi zamanta kawai acan ɗin, nayi magana da Khaleel zai koma kwana acan, Aysha da Anam sai suje suma su tayata zama tunda bawani abu suke anan ɗin ba”.
       Abba dake murmushi yace, “Hakan ma yayi to. ALLAH ya baka sa’ar abinda zakaje dominsa. Ya kuma dawo mana da kai lafiya”.
      Da amin suka amsa shi da Daddy. Daga haka suka cigaba da tattauna wasu batutuwan daya shafesu da kuma tafiyar tasa.

            ★★★
    Anam bata san mike faruwa akan komawarsu gidan Yaya Shariff ba sai washe gari, dan bata wani bama maganarsa ta jiya muhimmanci ba. Koda taji batun cikin Fadwa kuma batace komai ba. Tadai saka albarka a sa ranar Maheer da akace wata huɗu.
      Da yamma ta dawo aiki Mom ke sanar mata ta haɗa kayanta ita da Aysha zasu je su taya matar Shareff zama kafin ya dawo. Cikin waro idanu da mamaki take duban Mom. “Mom ni kuma? Kin san fa yanda matar nan tabi ta tsaneni ga Gwaggo da Mommy da Mamah a gefe…”
      “Anam duk na kawoma Abbanku irin wannan misalin, amma ya nuna min sun riga sun gama yanke hukunci. Kinga sai kibi umarninsu kawai ALLAH ya kaɗe fitina”..iyayenmu????????????ZAFAFA BIYAR

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button