BABU SO 22
22
………Kiran Gwaggo ne ya shigo tamkar tasan mike faruwa. Kamar bazata ɗagaba sai kuma ta ɗaga. Tai shiru taƙi magana. Ban san mi Gwaggon tace daga canba ta tunzura baki da faɗin, “Naji ina kwana”. Amsawa Gwaggo tai daga can sannan ta shiga gaya mata abinda yasa ta kirata. Ajiyar zuciya Fadwa ta saukea hankali da fara share hawayenta. Kamar tana a gaban Gwaggo ta jinjina kanta da yin ɗan murmushi tana mikewa bayan ta yanke wayar. A gurguje ta faɗa banɗaki tayo wanka, ko busar da kan batai zaman yi ba ta saka hula da doguwar riga ta fice. Kitchen ta shiga, ta dafa shayi da soya kwai ta haɗa kayan a tray. Sashesa ta nufa, dan dama jiya ya kwana a sashenta ne saboda ta ya buƙaci hakan. Babu kowa a falon, ta ajiye tray ɗin a centre table ta nufi bedroom ɗinsa. Shigowarta dai-dai da fitowarsa wanka. Yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Zuwa tai ta rungumesa tana kwantar da kanta a gadon bayansa. “Kayi haƙuri mijina na tuba, na fahimci nayi kuskure bazan sake ba”.
Shiru kamar bazaice komai ba, dan yasan wannan ba kalaman Fadwa bane wanine ya bata su akan harshe. Sai dai kuma shi ba mutum bane mai son zurfafa zargi, dan haka ya kamo hanunta ya zagayo da ita gabansa. Idanu suka ƙurama juna, sai faman sakar masa murmushi take, shiko tasa fuskar kadaran kadahan. “Nace fa kayi haƙuri”. Ta faɗa cike da shagwaɓa tana girgiza masa hannu. Cikin ɗan turo numfashi waje yace, “Okay fine ya wuce”. Rungumesa tai, kafin taja hanunsa zuwa gaban mirror. Da kanta ta shafa masa man a jiki tana masa duk wani salon kwarkwasa dazai sashi cire komai a rai kamar yanda Gwaggo tai mata huɗuba. Ta ɗan samu ya biye mata badan komai ba sai dan yana son su rabu lafiya. Yayi ƙyau cikin kananun kaya ga ƙamshi data feshesa da shi na tashi suka fito falo. Zama yay idonsa akan breakfast ɗin data ajiye….
“Inaga ki kirasu mu karya gaba ɗaya, dan ina son nayi magana da ku”. Kamar zatai gardama sai kuma ta haɗiye, cikin taushin murya tace, “Amma ƙwan iya naka na soya anan fa”.
Yanda ta amsa ɗin shima ya sashi tausasa nasa harshen dan yana son su rabu lafiya. “Kiyi haƙuri ki soya musu suma, dan yau tamkar baƙi suke anan”. Maganar Gwaggo tasata amsawa, sai kuma sanin halinsa. Juyawa tai ta fita a sashen gaba ɗaya, ya bita da kallo harta fice. Mintunan da basu gaza goma sha biyar ba ta kammala soya ƙwan ta leƙa ta kirasu batare data yarda tako dubi sashen da Anam take ba. Itama dai Anam ɗin bata ko kalleta ba sai Aysha ce ta gaidata da tasowa ta rungumeta. Anam ta taɓe baki da sake juyar da kai tamkar bata gansu ba.
Su suka fara shiga falon ita kuma tana biye da su a baya. Yana zaune a inda ta barsa, sai dai yanzu waya ce a hanunsa. Koda ya amsa musu sallama kuma bai ɗago ba.
“A haɗa a dining ne?”. Ta faɗa tana kallonsa. Ɗan ɗagowa yay ya kalleta ya maida kansa, “No barsa mu zauna nan zaifi balance”. Kai ta jinjina masa. Aysha da Anam suka shiga gaishesa. Ya amsa musu da ɗan sauƙaƙa murya batare daya dubi kowacce a cikinsu ba. Saboda kar Anam ta zauna a kusa da shi Fadwa tai saurin jan hanun Aysha ta zaunar, sai ya zam sun sakashi a tsakkiya, ita kuma inda Anam take zaune sai yazam sunyi facing juna ita da shi. Haka kawai taji abun ya bata dariya, dan tana lura da sanda Fadwa taja hanun Ayshan. A zuciyarta tai dariya, a zahiri kam babu ɗigon fara’a a fuskar tata.
Aysha ta haɗa mata shayin da ajiye mata gabanta dan taƙi taɓa komai, a hankali tace mata ‘thanks’. Ba wani iya cin komai tai sosai ba har yanzun, dan haka koda Aysha tace a saka mata ƙwai kanta ta girgiza mata da nuna mata bread ya isa. Ɗagowa yay suka haɗa ido, lokaci ɗaya tsigar jikinta ta tashi. A hankali ta janye idanunta daga cikin nasa, shima nasan ya janye batare da yace komai ba. Fadwa kam bama ta nuna tajisu ba, sai Aysha ce tace “K kullum a baki iya cin abu ba bazaki koyama kanki ba?”. cikin yin ƙasa da murya tace, “Ni bana sonsa ne fa”.
“To k dama indai abinci ne ai komai bakya so”.
Hararar Ayshan tayi, batare da ta sake cewa komai ba ta cigaba da juya cokali a shayin tana tsakurar bread ɗin. Ɗagowa kam bata sake yarda tayi ba balle ta haɗa ido da shi har suka kammala. Ita da Aysha suka tattare wajen, suka kwashi kwanikan zuwa sashinta. Kasancewar yace su aje su dawo basu ɓata lokaci ba suka koma. Fadwa suka samu zaune a jikinsa, shigowarsu kuma bai sa ta jaye ba, sai shine yay mata nunin ta zauna da ƙyau da ido. Ganin yanda fuskarsa take babu wasa yasa ta matsawa sai dai ranta bai so haka ba. Oho wadda take dan itan ma bata san tanai ba, dan koda suka shigo Anam bata yarda ta kalli ko sashen da suke ba. A ƙasa suka zauna, ya fara addu’ar da MANZON ALLAH yace muyi a duk sanda muka samu kammu a irin makamancin zama haka kafin ya ɗaura da nasiha a garesu, da ga ƙarshe ya ƙare da gargaɗi mai cike da kurarin tabbatar musu in har yaji wani abun ɓacin rai daga garesu su duka ransu sai ya ɓaci, kowacce ta kama kanta, su su girmama matarsa a matsayinta na Yaya a garesu kuma matarsa, itama ta riƙesu a matsayinsu na ƙannenta kuma ƴan uwansa. Daga ƙarshe ya rufe da jawabin zaman Khaleel a gidan, sai dai shi kwana kawai zai ringa zuwa yayi sai kuma cefane da duk wasu buƙatun gidan su nemesa. Daga haka ya sake rufe taron da addu’a yana miƙama Anam kuɗi, kamar tace a’a amma sai ta amsa tayi godiya, itama Aysha kamar na Anam ɗin ya bata. Cike da zumuɗi ta amshe abinta tai godiya, daga nan ya sallamesu.
Koda suka koma ɗaki Anam kwanciyarta tai tunda yau babu fita aiki, Aysha kam tai zaman lissafa kuɗinta dayin budget ɗinsu cike da farin ciki duk da dubu goma ne kawai. Barcinta da yay nisa ya saka har Yaya Shareff yabar gidan bata sani ba, koda Aysha ta fito masa rakkiya wajen mota dan da Fadwa zaije har airport cike da makirci Fadwan ke tambayar ina Anam. Aysha tace, “Barci take aunty ko’a taso ta?”. “A’a ki barta kawai kar’a tadata kanta yazo yana ciwo ko”. Duk yana jinsu, sai dai baice komai ba. Sai da Aysha taga fitar motar tasu sannan ta dawo itama ta kwanta dan barcinne a idonta.
A gidan su yaja kusan awa biyu, yay sallama da kowa sannan Khaleel ya ɗaukesa shi da Fadwa zuwa airport, basu wani jima suna jiraba jirgin da zai kaisa abuja ya keta hazo. Khaleel ya ɗakko Fadwa dake hawaye yana mata ƴar dariyar tsonar shagwaɓar tata. Ganin ya nufi hanyar maidata gidanta tace ita dai ya kaita can gidan zata ɗauka abu wajen Mommy, idan ma yanada wani uzirinne ya barta zata maida kanta gida kawai. Bai ƙiba ya canja hanaya.
Duk yanda Mommy da Fadwa suka so ayi maganar zaman Anam ɗin Gwaggo tace ba yau ba, ransu yaso fara ɓaci, sai dai Gwaggo ta nusar da su gaggawa ba tasu bace. Ita dai ta koma gidanta koda wasa karta nuna rashin son zaman Anam ɗin a gidan daga nan har zuwa sanda zata sanar musu abinda ta ƙulla. Fadwa bawani ta gamsu bane, dan haka batama gama sauraren Gwaggon ba ta figi handbag nata tai ficewarta. Duk da kallo suka bita, Gwaggo ta taɓe baki tana duban Mommy.
“Idan baki tashi tsaye akan wannan surukar taki ba to lallai ina tabbatar miki nan gaba kaɗan sai tasha kanki. Dan hatsabibiyar yarinyace da kanta kawai ta sani, halinta dana uwarta bashi da banbanci”.
Wani bahagon numfashi Mommy taja da ƙarfi tana duban Gwaggo tamkar mai son samo ƙarin bayani akan fuskarta, Gwaggo ta taɓe baki tana miƙewa. “Kinga ni jeki kafin mijinki da shi bai rabo da zargi yasan kina nan, nima kwanciya zan ɗanyi barci bai isheni ba jiya da dare”. Da kallo kawai Mommy ke binta hartai shigewarta bedroom. Itama tashin tai cike da rashin zaɓi ta fito dan tasan Gwaggon tayi hakane dan gujema kowace irin tambaya daga gareta.
Gwaggo dake laɓe jikin ƙofa tana leƙen Mommy ta taɓe baki, cikin ƙara yamutse fuskarta da tsufa ya gama nuna kansa tai murmushi mai cike da ma’anoni masu yawa da fahimtarta sai dai ALLAH.