BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 23

23

………“Anya ƙwaƙwalwarki na aiki da ƙyau kuwa? Kin san wacece Gwaggo a wajen mu? To muna mata kallone tamkar mahaifiya, domin tana bamu dukkan gata irin na uwa tun mahaifiyarmu na raye. Su kansu su Yaya da suke mata wani abun a yanzu babu abinda ke ɗawainiya da su sai asiri da ƴan uba sukai musu saboda su basa samun koda sakin fuska daga gareta, sai dai Alhmdllhi na gagara a garesu, ƴan uwana ma zan dawo da su hanyar da aka kautar dasu. Bari na tuna miki idan kin manta, shi wannan auren da kike takama da shi Gwaggo ce tai ruwa tai tsaki akan kowa har shi Shareff ɗin da uwarsa, dan haka kisa hankalinki waje guda, na tabbata tunda tace mu bata lokaci akwai abinda take shiryawa. Kema ina so ki kwantar da hankalinki Fadwa, kinga bake kaɗai bace ba, ba’a bukatar duk wani tashin hankali daga gareki yanzun, indai matsalar ƴar Usman ce dake gidanki, ki bamu ƙankanin lokaci, ba gidanki kawai ba, Nigeria gaba ɗaya zata bari, barin da har abada bazata sake waiwayowa ba ita da iyayenta. Sai dai hakan bazai faru ba har sai kin haɗiye komai yazama ba komaiba, inba hakaba tashin hankalinki na nufin samun cikar burin Usman na ganin ya nanama Shareff ita ya aura…..”
     Wani mugun tari ne ya sarke Fadwa, sai da Mamah ta bata ruwa tasha, hawayena sharara a fuskarta. “Mamah dan ALLAH kar kimin baki”. “Ba baki nake miki ba Fadwa, mun jima da fahimtar ƙudirin Usman na son haɗa auren ƴarsa da Shareff, a yanda su Yaya suka canja kuma komai zai iya faruwa idan har ya fiddo buƙatarsa a zahiri. Shiyyasa muke son amfani da zamanta a gidan naki tunda mijinki bayanan mu mata abinda zatama bar ƙasar gaba ɗaya har uban nata bazai sake sha’awar zuwa ba balle tunanin ƙulla wata alaƙa damu”.
     A hankali Fadwa ta sauke ajiyar zuciya. “To amma Mamah bana ƙaunar ganin yarinyar nan wlhy”. “Haka zaki daure na ɗan lokaci ne, kiyi kamar ma baki san da zamanta a gidan ba, dan so muke ta saki jiki sosai saboda shirinmu yay tasiri”. Har cikin rai bawai ta gamsu bane, dan ba ƙiyayyar wasa takeji a zuciyarta akan Anam ba. Dan kamar an raini zuciyarta da tsanar iyayen Anam ne tun tana ƴar karamarta, hakanne yay tasiri matuƙa tare da cakuɗuwa da kishi ya nunku akan Anam ɗin, dan ko yaya Amrah kan samu sassauci a wajenta duk da itama ba sonta take ba kamar yanda bata son mahaifiyarsu. Sosai Mamah ta zauna ta kara lallashinta da maganganu masu daɗi har ta ɗan huce, kwanciyarta tayi anan sai washe gari ta koma gidanta da yamma.

Aysha kawai ta samu, Anam bata dawo aiki ba. Itama Ayshan ƙin sake mata tayi, sai daga baya kuma mitagani oho mata saita fara janta da hira da tambayar jiya basuji tsoroba dai ko su kaɗai. Aysha bata da saurin fushi, duk da tsumewar da Fadwa ta shigo tana mata sai bata ɗaukesa komai ba. Kanta tsaye fuska da murmushi ta shiga bata amsar basuji ba saboda Yaya Khaleel yazo da wuri, shine ma yake sanar musu bazata dawio ba sai gobe. Murmushi kawai tai, daga haka ta canja hirar.
        Sai kusan ƙarfe bakwai Anam da Khaleel suka shigo, da alama bayan sun tashi aiki can gidan ya wuce da ita, sai da ya gama kimtsowa suka taho tare. Yanda Fadwa bata kulata ba. itama sai batabi takanta ba tai shigewarta ɗaki ta barsu suna gaisawa da Khaleel, tanaji suka zarce da hira bata fitoba sai ma tai kwanciyarta dan dama taci abinci wajen Mom abinta. Har tai barci Aysha bata shigo ba, sai da ta farka ta ganta kwance, dama Aysha a ƙasa takeyin kwanciyarta dan Anam bata iya barci ita da wani a gado, shiyyasa a ranar farko tai kwanciyarta a sofa, ganin hakan yasa Aysha jiya tace ta hau gadon ita zata kwanta a ƙasan dan Anam ɗin kasa barci tai. Alwala tayo tai nafilfilinta sannan ta dawo ta sake kwanciya.
     Koda sukai sallar asuba bata koma ba, shirin fita aiki tai har Aysha na mitar sammakon nata bata dai kulata ba. Lokacin da suka fice ita da Khaleel Fadwa bata fito ba ma. Sai mai aikinta da jiya tazo da ita daga gidansu ce keta faman aikin gyaran falon…..

__

           Yau kwanakin Shareff biyar kenan da wucewa ƙasar China. A zahiri tsakanin Anam da Fadwa babu mai shiga harkar wani. A baɗini Fadwa ta kasa jin zata haƙura da jiran shirin su Gwaggo. Dan kuwa kullum jin ƙarin tsanar Anam ɗin take a ranta musamman idan tana waya da Shareff ya tambayeta lafiyarsu. A yanzun ma har faɗa sukai dan yace taba su wayar su gaisa tace Aysha kawai zata bama wayarta banda Anam. Ya tambayi dalili tace saboda Anam ɗin bata isa ba.
      “Nasihar dana muku kafin na taho bata shigaba kenan? Fadwa miyasa kike son kawo min raini ne akan duk abinda na sharɗanta miki?”.
    “Ni laifina kawai kake gani ita bazaka bincika mitaiba. Yarinyar nan tunda tazo gidan nan sai dai taci ta kwanta tai wanka ta fita. Ko gaidani batayi, kai kallo ma ban isheta ba ina matsayin matar gidan. Ya kake so nayine Soulmate? Sai naita binta tana jana a ƙasa duk da ina sama da ita? Ai Aysha ba haka takeba, zata zauna muyi hira ta taya mai aiki aiki, kai kullum ma itace mai mana abinci, finta tai a gidan da ita bazata zauna ayi da ita ba. Shiyyasa tun farko nace ban yarda ta zaunamin gida ba amma kaƙi saurarata….”
     Ƙittt ya kashe wayar, hakan ya sake harzuƙa zuciyarta sai kawai ta fashe da kuka. Kuka taci har ta gode ALLAH. Tana cikin kukan sai gasu Sima tamkar an jehosu gidan har su huɗu. Anam na baranda zaune tana karatu suka wutota. Yanda basu mata sallama ba itama ko kallonsu batai ba dan ta gane Sima. Turus sukai suna kallon Fadwa da duk ta koɗe ta fita hayyacinta a kwana kaɗan, dama sun bar ganin posting ɗinta ne gaba ɗaya shiyyasa sukazo suga ko lafiya, dan bata cika zama gwanar kiran waya ba ita dama, ko kiranta kai sai ta gadama take ɗagawa.
       “Baby Fady kina lafiya kuwa?”.
Cewar Siyyah da tun randa suka kawo Fadwa ɗin bata sake tako gidan ba sai yau. Komai batace ba, sai wasu hawaye da suka sake gangaro mata. Da sauri Amal takai zaune kusa da ita ta rungumota jikinta tana shafa bayanta cike da lallashi, kusan mintuna uku Fadwa ta fara sauke ajiyar zuciya, hakan yasa Amal ɗagota. Tissue Sima ta ɗibo ta miƙa mata, babu musu ta amsa ta share hawayenta. Bibah da tunda suka shigo batace komaiba sai yanzu ta kalla Fadwa. “Baby Fady kinsa duk jikinmu sanyi, badai namijine ya fara nuna miki butulcinsu na cin moriyar ganga a yada kaurenta ba, kin ganki kuwa duk kin wani yamutse kin fita a kamaninki kamar wata mai ƴaƴa huɗu”.
     Baki ta buɗe zatai magana turaren ɗaya daga cikinsu dake ta faman hawa mata kai ya sata tashi da gudu tai toilet. Da kallo duk suka bita, sai da ta fara kakarin amai ne suka mike a zabure suka rufa mata baya. Da taimakonsu ta wanke bakinta, Sima na yatsine-yatsine ta gyara wajen.
   “Tabɗi babbar magana. Da alama dai Baby Fady cikine da ke”. Siyyah ta faɗa cikin riƙe baki. Sima ta ƙarɓe zancen da “Wane irin ciki kuma ana zaune ƙalau Shamsiyyah?”.  
      Fadwa da ta fahimci turaren Bibah ne ke hawa mata kai hanunta toshe da hancinta tace, “Bibah turarenki ne matsalata wlhy, buɗe Wadrobe ki ɗau wasu kayan ki canja a fidda waɗan nan karki kashen…..” bata karasa ba aman ya sake tahowa dole da sake mikewa da gudu tai bayi. Yanzu kam yi sukai kamar bazasu bitaba, sai daga baya cikin ƙunkuni Sima tabi bayanta ta taimaka mata. Kodan karsu cigaba da bautar kwashe amai dole suka takurama Bibah ta tashi tai wanka ta canja kaya. Daga haka aka samu sauƙi hankalin Fadwa ya samu nutsuwa harta kira mai aikinta ta kawo musu abinci da kayan ciye-ciye. Ta tambayi Aysha fa? Tace barci take. “Bakar yarinyar nan fa?”. “Ranki ya daɗe tana waje tun ɗazu kamar karatu dai take”. Baki Fadwa ta tabe, cikin bada umarni tace rufemin ƙofar falo bana bukatar shigowarta har sai ƙawayena sun wuce”. “Okay ranki ya daɗe an gama”.
     Bayan fitar mai aiki su Sima suka shiga tambayarta tana da damuwane ko kuwa cikinne ya maidata haka har yazam ba’a ganinta a online gaba ɗaya. Ranta a ɓace yake sosai da abinda ya faru tsakaninta da Shareff yanzu, ga damuwar hanata ɗaukar mataki akan Anam da su Mamah suketa famanyi har yanzun. Ita kuma tanajin cewa bafa zata iya juriyar zaman jiransu ba a halin yanzu tunda har takai mijinta na kashe mata waya dan ta faɗi laifin Anam. Su Sima ƴan amanarta ne da take kallo fiye da kowa a cikin ƙawaye. Bibah da Shamsiyya ƙawayentane tun na ƙuruciya sannan ƴan uwanta ta ɓangaren mahaifi. Dan haka kanta tsaye ta shiga zayyane musu dukkan damuwarta akan zaman Anam a gidan dama abinda take tsoro wanda dukan sunsha cemata dama suna zargin Shareff da Anam na soyayya ne tana gwalisesu.
      Dukan su kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa. Dan kowannensu akwai manufarsa a kanta tun ba yanzu ba. Fadwa nada ƙyau gwargwadon iko sun sani, mahaifinta nada arziƙi gwargwado shima sun sani. Sai dai Bibah ta fita ƙyau nesa ba kusa ba, hakama mahaifin Siyyah yafi na Fadwa arziƙi nesa ba kusa ba. Amma ta fisu abubuwa da yawa da suke ganin ya kamata ace sune ke da shi ba ita ba. Hatta su Sima data raini wayewarsu da ɗaukakarsu da kanta kowanne da nasa manufar….
Ta bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya idonta cike da ƙwalla. “Ina son kowannen ku ya bani shawara guda ɗaya akan matsalata domin kaina ya kulle ina neman mafita. Mafita ta gaggawa kafin matsalarmu da mijina tafi haka faɗi dalilin ta”……….✍

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button