BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 31-35

Page 3⃣1⃣ to 3⃣5⃣

Haka jiddah ta raya wannan dare tana kuka..da ta tashi da safe kuwa fuskar nan tayi jajirr abinka ga farar mace,,idanuwan nan sunyi luhu luhu..a sanyaye take komai dan har yanzu zuciyarta bata dena mata zafi na tafiyar ammar ba…

Zaune yake a gaban abban shi fuskar nan a daure..sai ya dawo sak ammar din dana sani mara son wasa,,domin kuwa yayi tinanin abban shi zai goya mishi baya daya ce baya son tafiyar,,,abban ne ya fara magana cike da fushi…ammar kenan kai bakaji kunyar tunkara ta da wannan maganar ba kalleka fa shekara 22 sai yanzu ka gama scondry skul sa’annin ka duk tun yaushe suka gama saboda kai bakason cigaba kome?to wannan karon babu fashi gobe jirgin ku zai tashi da yamma ka gama duk wani shirinka dole ka tafi,,kai kafi so ka zaunj a gari kana yawo da abokan banza ana maka gata amma kai baka gani baza ka gane gata ake maka ba tukun sai nan gaba idan kayi hankali,,,tafiya kam ba gudu ba ja da baya na gama maka komai…ka tashi kaje ka cigaba da shiri,,,tun da ya fara fadan kanshi na sunkuye amma fa ji yake kamar zuciyar shi zata fashe saboda takaicin tafiyar shi,,,tashi suka yi duka kowa yayi dakin shi,,,da sauri umma dake labe tana jin duk yanda suka yi itama ta shige dakinta,,,waya ta dauka ta kira laraba ringing biyu ta dauka cikin farin ciki umma ta fara fesa mata duk halin da ake ciki,,dariya itama kwashe dashi sannan tace,ai na fada miki idan har kika yi haka dole yabar gidan tunda abbansa yana son yaga yayi karatu kafin nan da 5yrs din ai mun gama abinda zamuyi mun kara gaba,,,aikuwa dai laraba akwai ki da basira,,,kin mantani kenan umma wai dan ma nayi sanyi kenan,,,,to shknn jibi kizo da sassafe akwai magana tunda shi abban nasa ba zama zaiyiba,,,to shikenan…

Inna asabe da lami zaune a gaban na bakin rafi..lami ce zata fara fada mashi abinda ke tafe dasu,,,da sauri bokan yace mun riga mun sani tun shigowar ku dajin nan,,,yar mijinki ke baki matsala me kike so a mata a haukata ta ko a kashe ta,,,da sauri lami tace aa boka so mike a lalata rayuwarta ta koma kaman karya yanda al’umma zasu kyamace ta ta koma abin kyama,,,,katseta bokan yayi tare fadin ba yanzu ba,,,domin kuwa yanzu ba aljanin da zai iya zuwa ya rabeta dan tana ibada kuma ko yaushe cikin karatun qur’ani take duk aljanin da yaje kusa da ita kuwa yanzu to lalle sai ya kone,,,,inna asabe ji tayi kamar ta kurma ihu dan takaici taga samu taga rashi,,da sauri tace to yanzu boka ya zamu yi,,,,,cikin daga murya yace zan baki wani magani kullum ki zuba mata a cikin abinci indai tana ci to a hankali zata fara daina ibada zai saka mata kasala to a wannan lokacin ne zamu aiwatar da shirin mu a kanta,,,,amsa lami tayi tare da fadin mun gode boka,,kudi inna asabe ta ciro ta ajiyemai a gabanshi,,sannan suka fita….tafiya ce me nisa sosai tsakanin gurin da bakin titi,,inna asabe ke cewa lami,,to yaya zan bata maganin tunda kullum ne,,,mtsw lami taja tsaki kafin tace ta inda aka hau ai tanan ake sauka…nuna mata zakiyi komai ya wuce ta yafe miki ke inta kama har kuka kiyi ta yanda zata yarda kinyi nadama to ke kuma kinga kin samu hanyar yi mata komai tunda zata yarda dake,,,,tabbas shawarar ki tayi lami muje gidan dae….

atm card din daya bata ne a hannun ta ga kuma wayar a gefe..duk wannan basu take bukata ba tafi bukatar shi a kansu lokaci daya haka kwatsam…kuka ta kara fashewa da shi tana mai fadin allah ka kawomin dauki a rayuwata,,sallamar inna asabe ce ta katse mata kukan da takeyi…abin ya bata mamaki inna asabe da sallama bata kara jin mamaki ba sai da taga inna asabe ta leko tana fadin sannu jiddah ya gida,,da sauri ta mike ta fito waje dan kuwa har yanzu bata gama gyara gidan ba,,,kuma tana kara mamakin inna asabe,,zo nan jiddah taji ance daga bayanta cikin tattausan lafazi,,juyawa tayi ta nufi kofar dakin indainna take a tsaye,,,jiddah”da sauri ta dago kanta ido ta zare ganin inna asabe ido jajirr da alamu tasha kuka,,cikin muryar kuka ta fara magana jiddah ki yafemin na zalunce ki na cuceki tun kina karamar ki,zubewa tayi bisa gwiwarta tana mai kara fadin ki hakuri jiddah ki yafemin ko zanji salama a raina ina cikin kunci kada in mutu da hakkin ki a kaina ki yafemin dan allah jiddah tare da fashewa da kuka mai ban tausayi,,,,da sauri jiddah ta dago ta tana fadin inna kefah uwata ce bai kamata ki tsugunna a gabana ba wallahi na yafe miki,,,ngd jiddah cewar inna asabe allah ya miki albarka yata ta kaina,,bakomai inna komai ya wuce,,to jiddah jeki kwanta ki huta kema zatayi musu inna asabe tace lallaifa saidai ta kwanta,,ba yanda zatayi ta juya ta shige dakinta tana mamakin abinda ya faru ayau,,,inna asabe kuwa dariyar mugunta tayi kafinta tace yaro bai san wuta ba sai ya taka…..

yanzu aka fara

masoya novel dina kuyi hakuri da jina shiri kwana2 hakan ya faru ne saboda wasu dalilai amma yanzu zaku rinka ganin shi akai akai kamar yadda muka fara

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button