NOVELSUncategorized

DOCTOR NA’IM 3

Page 3
Washe garin ranar ya futo kamar kullum sanye cikin shigan likitoci Sauri sauri yk don Abba ne yake son ganinshi. Ya isa falon d sallama, da mumie sakina ya soma hada ido aikuwa ta wurga mishi uwar harara

Ya samu guri y xauna kusa d saleem yasoma d gaishe d abban. Sannan itama y gaisheta, a dakile ta amsa Wanda ko kadan hkn bai dameshiba
Abba ya soma mgn bayan yy gyaran murya. Toh alhmdllh kamar yadda a kwana kin baya mukayi mgn daku to ginin gidajenku sun kammala, kuma insha Allah nan da wata uku masu xuwa xan hadaku n aurar daku.
    Dg hk y mika musu mukallan gidan yace xasu iya xuwa su gani, dukkan ninsu suka karba suna godiya. Na’im jikinshi duk yy sanyi hk kawai yk jinshi wani sukuku.
     Abba ya danyi naxarinshi na yan mintuna kafun ya kira sunanshi likita. Y dago y kalli abbn cikin dashewar murya yace na am abba. A kwae wata matsalan ne? Aa ya fada yana girgixa kanshi
Abba yace komai yayi kenan? Ya kara amsawa d eh Abba b abinda xance mk sae Allah y saka maka d mafificin alkhairy y biyaka duniya d lahira kayi mana komae a rayuwa bamu taba kukan maraici ba mun gode sosae y karasa fada yana me maida hawayenshi.
Abba y daga mishi hannu y isa banason jin irin wannan magan ganun kuma yaya nane ai  bb wani bambanci tsakanin Ku dasu saleem, xaku iya tafiya
    Duk jiki a salube yk tafiyar yadda kafafunshi suke shaking baya jin xai iya karasawa inda y nufa don hk y zauna saman kujera gami d kwantar d kanshi
Abbas y xauna kusa dashi gami d dafa shoulder dinshi ka fawwalawa Allah lamuranka na’im shi kadai ne xai iya kawo karshen matsalolinka
  Ya dan dago yana kallon Abbas din, zaiyi mgn Abbas y daga mishi hannu basai kamun vayani ba nasan bb abinda yk damunka gajiya ce kawai. Tun kafun kaje gurin aikinma har gajiya ta soma xuwa
 
 Kakalo murmushi kawai yy don y gane mgn Abbas y fada mishi dukkansu uxuri yk musu don basu San meye takamaiman matsalarshiba kuma baisan ta inda xai soma fada musu ba donshi mutum ne dabae son fadar cikin shi
Mikewa yayi ya nufi side dinshi yana Jan kafarshi datayi mishi nauyi. Tana tsaye sanyeda xunbulelen hijab yayinda saleem ke tsaye saitinta hira sukeyi sosai irinta masoya kai d ganin su kasan suna matukar kaunar junansu. Wani mashi ya sokeshi a dai dai lokacin daya karaso gurin.
  Neehal d kamshin turarenshi y sanar d ita xuwanshi ta kasa kwakwkwaran motsi yanda duk t diririce yasa ta dan b saleem dariya yace ke ba wani nebafa yaya na’im ne
Na’im kuwa ko ta Kansu baibi ba y shigewarshi duk d yanda saleem yk t xolayarshi ammn Sam bai kula ba.
     Yana shiga falonshi y xube a kasan carpet kamar karamin yaro yasoma sambatu wayyo Allah mum. Mum xanso kiga irin halinda na tsinci kaena. Mum n fada tsaka me wuya. Ina ma Wanda y mutu yana dawowa, mum da xanso ki dawo kiga yanda n xama. Babu Wanda yasanta kowa bai santaba, kowa besan wace wannan zuhairanba. Mum don Allah ki fada mun waye ni? Menene asalina? Shin wacece wannan zuhairan d babu wanda yasan komai game da ita? y karashe mgnr yana xubar d hawaye 
Ya kusa minti goma yana sambatu kamar zautacce kafun dg karshe y shige bedroom dinshi y kwanta. Aikuwa xaxxabi me xafi y rufeshi
Wayarshi da tk falo tayi ringing yafi sau goma bai masan tanayiba. Saleem ma da suka gama hirarsu d neehal gaba yy don yasan halin na’im duk lokacin d ya ganshi a irin wannan yanayin to ranar kam b sauki inka takura mishi xaku iya yin batacciya.
 
A bangaren mummy sakeena kuwa tacika tayi fam hk kurum ta tsani ganin na’im bata kaunar t bude ido t ganshi a gidan gashi ynx alhaji ibraheem  don tsabar gata y dauki yarta daya tilo data dora duk wani buri nata akanta ya bashi. Ita kuma tayi alkawarin indae tana raye Siyama baxata taba auran na’im ba ( shirun d tayi tana nata shirin ne ta karkashin kasa bataso y xargi wani Abu shiyasa ta kwantar d kai)
Bayan futarshi ta kirawo siyaman a waya tace maxa ta shirya xata aiketa gidansu muslihu
Yan mintina kalilan ta futo shirye cikin doguwar riga blue black, dayake Siyama farace tas tayi kyau sosae kamar balarabiya. Ta samu mum dinta a falon ta. Tana ganin tilon yar tata tayi murmushi ita kanta tasan yar tata ta hadu b karya. Sai kuma taja tsaki tuno irin yadda abbanta yk Neman karyarwa d kyar tata daraja, don inya hadata d na’im y gama dasu tasan har cikin friends sai taji kunya ace kamar Siyama xa a yiwa auran sadaka komai ubanta yy wa mijin
Siyama t kwantar d kanta jikin mom din nata tace mum nifa ke nk jira ki bani sakon gara n tafi da wuri don n dawo d wuri kada yy na’im ya dawo yy mun fada
Tirkashi
Wannan mafari ne kawai

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button