BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 28

28

………..A haka aka shiga shirye-shiryen bikin Maheer, Anam da Aysha. Yayinda kwanakin dawowar Shareff da ba’a sanar da shi komaiba ke kusantowa. Asabar ɗin daya rage saura sati uku biki Anam da Aysha acan gidan suka yini ana shirye-shirye da tsare-tsare. Anam dai ba shiga sabgar duk wani shirye-shirye take ba, su Fadwa ne dai ƙirjin biki keta kaiwa da kawowa duk da ango Maheer bawai yana ko leƙowa yaji yanda abubuwan ke tafiya ba ne, dan shi ƙiri-ƙiri nunawa yake baya son auren nan. 
        Haka itama Anam Muzzaffar yayi tafiya dan tunda aka fara maganar auren ma bata gansa ba, a wayama sai jefi-jefi dan baya ƙasar yaje wani aiki mai muhimmanci a yankin larabawa.
Washe gari lahadi Khaleel ya dauketa ita da Aysha kamar yanda yay mata alƙawari zuwa wajen tela. Kayanta takai na ɗinki, Mom ce ta bata su takai ɗinki kusan kala goma sha biyar. Kayane masu ƙyau da tsada har tana mamakin miyasa aka banbantata da Aysha, dan telan nata ma na musamman ne saboda Mommy taƙi yarda Aysha ta kawo nata nan. Bayan sun zaɓi ɗinkunan da take so ya gwadata ya faɗa misu bill ɗin kuɗin. Accaunt number ɗinsa Khaleel ya amsa, ya saka masa rabin kuɗin rabi yace sai ya kammala aikinsa. Daga nan gidan wata ƙawar Mom suka nufa ƴar sudan. Har Khaleel ɗin suka shiga ciki, yanda aka tarbesu ya bada tabbacin Khaleel ɗan gida ne. Sun ƙara tabbatar da hakanne lokacin da wata ƴar budurwa ta kawo musu abinsha tana ta faman sinne kai na kunya, yayinda Khaleel ke faman jifanta da wani kallo. Cikin yanayin tuhuma Anam ke kallonsa tana murmushi, yay murmushi kawai da ɗauke kansa gefe.
“Uhm to lallai ALLAH ya sanya albarka Yaya Khaleel, amma auntyn tamu fa tayi dan kun dace”.
Salute ɗinta yayi, hakan ya sakata kwashewa da dariya Aysha na tayata, dan ita ta kasa cewa komai tunda ba wasa yake da su ba. Fitowar matar hamshaƙiya ƴar gayu ya saka Anam haɗiye dariyarta. Suka gaidata cike da girmamawa itama tana amsa musu da kulawa cikin hausarta da bai gama nuna ba. Khaleel dake faman sinne kai ta kalla, “My son wacece a cikinsu?”.
Anam ya nuna, kansa a risine yace, “Itace wannan Mama”.
“Masha ALLAHU, ALLAH ya sanya albarka. Kace mata insha ALLAH bazai gagara ba, nima zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zan shigo dan maybe zuwa laraba mu fara, kaga zamu samu kwana goma sha bakwai kenan”.
“To shikenan insha ALLAHU zan sanar mata”.
Daga Anam har Aysha babu wanda ya fahimci inda zancen ya dosa. Sai dai ganin akan Anam ɗin ake magana ya tsaya musu a zukata. Ƙagara sukai su fita suyi tambaya. Amma sai matar ta tsaresu akan sai sunci wani abu. Su kaɗai suka ɗanci snacks. Shi dai Khaleel ruwa kawai yasha dan kunya. Ganin haka tasa budurwar nan mai suna Suhaima tai musu packaging ɗinsu dan harda gasashshen nama.
“Yaya Khaleel mufa kun samu a duhu.” Anam ta faɗa dai-dai suna shiga mota. Murmushi yayi yanama motar key, cikin basarwa yace, “Akan mi?”.
“Komai ma”.
“To kuyi addu’a ALLAH ya haskaka muku”. Daga haka yaja bakinsa yay shiru. Duk yanda sukaso jin ƙarin bayani bai basu fuska ba har suka iso gida. Kasa haƙuri Anam tayi sai da ta tambayi Mom. Kai tsaye Mom tace mata gyaran jiki na bikin amare za’ai mata dan taga duk tayi duhu. Murmushi kawai tai dan da gaske itama ta fahimci tayi duhun ko dan fitar da take kullum ne oho. Daga haka bata sake bin ta gyaran jiki ba.

Yau litinin da tai dai-dai da saura kwanaki goma sha ɗaya biki. A yau ake saka ran saukar su Mamie Nigeria sai dai Anam bata san da hakan ba. Hasalima ta tashi ne da ɗan zazzaɓi. Wajen ƙarfe sha biyu Muzzaffar yay kiranta a waya. Yanda yaji muryartane ya sashi ruɗewa yace zai zo ya kaita asibiti. Amma sai taki acewarta tasha magani. yata lallaɓata amma taƙi yarda dole ya barta dan yasan mutuniyar tasa ƴar tutsu ce. Koda sukai sallama ma sai ta kashe wayar gaba ɗaya ta gyara kwanciya. Wani barcin ne ya sake awon gaba da ita saboda maganin da Aysha ta bata tasha. Bata farka ba sai kusan uku. Alhmdllhi zazzaɓin ya sauka dan hakata samu tai wanka ta ɗanci abinci. Bayan sallar la’asar tana waje zaune ita da Aysha sai ga kiran Muzzaffar, kai tsaye ya sanar mata gashi a ƙofar gida. Murmushi kawai tai ta yanke wayar, dan zuwa yanzu kam Muzzaffar ya samu wani gurbi na musamman a zuciyarta duk da sun jima nesa da juna dan baifi kwana uku da dawowa ƙasar ba. Yau ne ya fara zuwa gidan suyi hira, dan haka sai da Aysha ta fita tayo masa iso, anan inda suke zaune da Aysha saman kujerun roba ya zauna. Aysha ta shige ciki ta kawo musa ruwa ta koma domin basu dama…
“Da alama zazzaɓin nan yaci amanar ango da yawa harfa kin rame dama gaki ba auki ba”.
Veil ɗinta taja ta ƙara rufe fuskarta tana murmushi. Shima ya murmusa cikin ƙara sanyaya murya yace, “ALLAH da gaske nake madam. Kodai aje asibiti?”.
“A’a ni naji sauƙi fa”.

“Kin tabbata?”.
Kanta ta jinjina masa. Murmushi ya sakeyi mai faɗi da shafa sajen fuskarsa. “Alhmdllhi ALLAH ya ƙara lafiya to”
“Amin ya rabbi.”
Shiru sukai na wani ɗan lokaci kafin ta saci kallonsa. Ganin ba ita yake kallo ba ta maida idanunta ƙasa ranta fal mamakinsa, dan babu rawar kan nan tasa, kuma bai kirata Beauty ba ko sau ɗaya. Murmushi yayi da gyara zamansa. “Madam nifa da magana nazo a bakina yau”.
Fuskarta ta ɗan buɗe sai dai bata kallesa ba. Ya cigaba da faɗin, “Juwairiyya gaskiya nima aure nake so”. A karan farko ta ɗago kai ta zuba masa dukan idanunta dake cikin gilashi. A hankali ya lumshe nasa ya sake buɗewa. “Wannan kallo ai sai kisa na gagara faɗar abinda ke raina”.
A yanda yay maganar ya sata sakin siririyar dariya. Hakan yayi dai-dai da buɗe gate da maigadi yayi motar Khaleel ta shigo. Su duka basu maida hankali ba, sai ma dariyar da yake tayata shima yana ɗan duban fuskarta da take kaudawa gefe, yanda yaketa ƙara ƙoƙarin son ganin fuskar tata sai yake ƙara bata dariya harta kasa dainawa….

 “Alhamdulillahi lallai yau jama'ar gidan nan zasusha surprise na ganinka Yaya fiye da yanda ƴan can gidan suka sha”. Khaleel ya faɗa yana kashe motar. Bai saurari amsaba ya buɗe gefensa ya fito, zagayawa yay ya buɗe masa fuskarsa ɗauke da murmushi.

Badan glass dake rufe da idanunsa ba babu abinda zai hana aga tsantsar ɓacin ran dake cikinsu. Tuni sun kaɗa sunyi jajur, duk wani annurin dake saman fuskarsa na farin cikin dawowarsa cikin zuri’arsa ya ɓace ɓat. Cike da izzar da fushi ya haddasa ya zuro ƙafafunsa ƙasa ya fito, hakan yayi dai-dai da juyowar Anam dake shirin ɗagama Khaleel hannu.. Hannun nata da numfashinta a tare suka maƙale, ƙirjinta yay wata irin bugawa da batasan dalili ba. A hankali laɓɓanta suka motsa ta ambaci sunansa…
“Yaya Shareff”.

Duk da akan laɓɓa tai maganar hakan bai hana Muzzaffar gane sunan wa ta kira ba, juyawa yay shima a hankali. Cikin dariya Khaleel ya ɗago musu hannu da faɗin, “Surprise”.
Murmushin yaƙe ta saki, mamakinta na sake bayyana akan fuskarta, ta miƙe a hankali kamar wadda ƙwai ya fashema a ciki ta nufesu, hakan yasa shina Muzzaffar miƙewa fuskarsa da murmushi yabi bayanta……….✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button