Labaran Kannywood

Daga karshe Angon Halima Atete ya bayyana a gurin Dinner Day 4 da Daurin Aure

Fitacciyar Jaruma a masana’antar kannywood Halima Atete wadda ake zaton a kaf matan dake masana’antar ta fisu Kudi, jarumar an daura Auren ta ne a yau Lahadi 27-11-2022.

Tun a satin daya gabata ne aka fitar da katin daurin Auren,cikin yardar mai kowa mai komai anyi shagali da bishasha a gurin bikin.

Halima Atete ta bawa masana’antar kannywood Babbar gudunmawa wadda baza’a taba maye gurbin ta ba, Jarumar tayiwa kanta fada tabi sahun sauran matan da suka shiga daga ciki a wannan shekarar ta 2022.

Daruruwan “yan uwa da Abokan Arziki ne suka sami damar halartar taron bikin hade da daurin Auren, haka ma a cikin Abokan sana’ar ta ta fim.

Ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakken bidiyon yadda shagalin ya kasance anan kasa,kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button