BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 43

Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

43

……..Shine ya amsa sallamar tata, da ɗan ɗagowa yana kallonta. Ta ƙaraso zuciyarta na mata zogi irin wanda aka san kowacce mace da kishi ke saka mata. Amma sai ta dake ta sakarmasa murmushi kamar yanda shima yake mata. Ɗan sumbatar gefen fuskarsa tai da bashi side hug. Nanma murmushin ya ɗanyi da lumshe mata ido irin na godiya…
     Anam taji wani irin tsammm a jikinta, dan tunda aka kawota gidan sai yanzu ne suka haɗu da Fadwa, wani irin ƙululu yazo ya tokare maƙoshinta akan abinda Fadwa tai masa duk da bawai kallonsu take ba. Amma sai ta dake ta fasa ɗagowar datai niyyar yi, goran ruwan ta ɗauka ta ɓalle bakinta, ta tsiyaya rabin glass cup data haɗo da shi ta ɗago ta miƙa masa fuskarta a tsuke…
    “Gashi”.
  Idanunsa ya ɗago ya kalleta, tai saurin janye nata saboda haɗuwa da sukai cikin na juna, sai ta ɗan tura baki gaba jin ya haɗa hanunta da kofin duka ya riƙo, kafin ya zare kofin yana faɗin, “Thanks” a samman lips ɗinsa…
     Ta gefen ido Anam ta dubi Fadwa datai wani zaman ƙasaita tamkar bata ganta ba, lips ɗinta ta ɗan cija na kasa a ranta tana ayyana (Tabbas bana son mijinki bakuma zan zauna da shi ba. Amma kafin nabar gidan nan saina tabbatar miki zama birin wasana a tsakkiyar kasuwa kamar yanda nai alƙawari tunda naga haka kike buƙata) A zahiri kam sai ta saki lallausan murmushi, dai-dai ya gama shan ruwan ya miƙa mata kofin sai akan idonsa. Idanunsa ya ware da ƙyau yana mata kallon mamaki, amma saita kauda kamar bata gansa ba. “A saka yogurt ɗin?”. Ta faɗa a hankali kamar mai raɗa.
     Kallon Fadwa ya ɗanyi, ganin idonta a kansu itama fuskarta kamar da ɓacin rai amma ta dannesa da murmushi ta ƙarfin tsiya ya sakashi dubar Anam da itama tata ke bayyanar da murmushi har yanzun. “Bari na kammala aikin nan zan sha”. Ya faɗa yana maida kansa ga lap-top ɗin…
      “Okay” ta faɗa a taƙaice da komawa kujerar gefansa ta zauna, har ƙafarta ta naɗe zuwa saman kujerar, hakan ya bama zaman nata damar facing ɗinsa, amma saita maida hankali wajen buga game a waya kamar yanda itama Fadwa dake zaune ta ɗayan gefensa ƙafa ɗaya kan ɗaya itama kujera daban, hankalinta ke kan waya tana duba Comments na mutanenta.
     Aikin yake sai dai lokaci-lokaci yakan ɗan kalla kowaccensu ta gefen ido, dariya suke bashi, dan kowacce ta tsume ita a dole hankalinta nakan wayane bata damu da ƴar uwarta ba, amma a zahiri babu ɗigon walwala akan fuskarsa. Kusan mintuna 17 ya kammala abinda yakeyi, system ɗin ya ajiye da furzar da numfashi yana ɗan lanƙwasa yatsun hannayensa daya haɗe waje ɗaya. Kallonsa Fadwa tai, ta saki ɗan murmushi da faɗin, “Waldon sir!”.
      “Thanks you dear”.
   Ya amsa mata yana sauke ƙafafunsa dake kan centre table ɗin suma ya zauna da ƙyau. Duk Anam najinsu, amma tai biris abinta. Yay ƴar gyaran murya da sake zama serious, hakan yasa itama Anam ɗagowa ta dubesa. Bai yarda ya kalla kowaccensu ba, cikin bada umarni ya fara karanto addu’ar da MANZON ALLAH ya horemu dayi a yayinda wani zama ya haɗamu makamancin hakan, kafin ya ɗora da faɗin, “Ina son ku bani dukkan hankalinku nan.”
    Babu wasa a cikin umarninsa, dan haka duk suka sake nutsuwa kowacce ta ajiye wayar hannunta, sai dai Anam bata canja daga yanda take zaune ba, dan taji daɗin zaman. Itama Fadwa dai tana yanda take ɗin sai muskutawa datai yanda zatafi sakewa da ƙyau.
     “Da farko zan fara da godema UBANGIJIN daya haɗamu a ƙarƙashin wannan inuwa, hikimarsace hakan kuma rubutaccene daga taskarsa tun kafin zuwanmu duniya. Gaba ɗayanku ina horanku da bani haɗin kai na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin gidan nan, ina kuma tuna muku tsoron ALLAH a cikin zaman da zamuyi. Ku dukanku matsayi ɗaya gareku a gareni, fatana ku cicciɗani da bani goyon bayan tsaida adalci a gareku. Ban yarda wata ta haɗa da shirka ko zalinci ba a wannan zaman, duk wadda tai hakan bazan yafe mata ba. Fadwa dake zan fara dan kece babba, duk da a shekaru na tabbatar zakuyi sa’anni koda tsiran zai-zama kaɗanne. Ki riƙe girman da ALLAH ya baki waje zaunar da adalci a gidan nan garemu baki ɗaya, kin fita sanin ilimin zaman gidan nan, kin fita sanin abubuwa akaina a yanzu zaki iya nusar da ita idan kikaga bata fahimta ba cikin sauƙi. Duk wata fitina da zata taso zan iya fara hukuntakine matsayin babba dan haka sai ki kiyaye”.
     Cikin danne komai dake a ranta ta jinjina masa kai da sakin murmushi. “Insha ALLAHU zaka sameni fiyema da yanda kake so a gidan nan Soulmate. ALLAH ya bamu zaman lafiya”.
     “Amin ya rabbi” ya faɗa yana maida dubansa ga Anam da duk take saurarensu. “Juwairiyya!”. Ɗago idanunta tai ta ɗan kallesa batare data amsa ba. Shima bai damu da amsawar tata ba ya cigaba da faɗin, “Ina fatan zaki bani haɗin kai wajen wanzar da zaman lafiya a gidan nan kema, sannan ki ɗauka Fadwa matsayin babba a gidan nan ku zauna lafiya, saɓanin hakan ba yana nufin zan hukuntata bane ita kaɗai, har dake zan haɗa domin matsayinku duk ɗayane a gurina. Abinda baki fahimtaba daya shafi gidan nan ko ni zaki iya zuwa gareta ta sanar miki”.
      Kanta ta ɗan jinjina da faɗin, “Insh ALLAH”. A ƙasan maƙoshi.
     “Bana son jin wani abu saɓanin abinda nake fata a gareku, dan yanzu ba da bane, a cikin gidana kuke ƙarƙashin ikona ku duka, zan iya ɗaukar kowanne irin mataki akan duk wadda ta shirya bani matsala ko raina ƴar uwarta. Mu dukammu jini ɗaya ne ku dinga tunawa da hakan a duk sanda shaiɗan ya bijiro muku da wani abu a zuciya ko wasu a cikin dangi. Dan na tabbatar a yanzu kowanne zai iya zama ashana da fetur ɗin cinnama gidana wuta adalilinku, kuma bazan amince ba, zan ɗauka mataki akan duk wacce ta bada wannan fuskar a cikinku da su wanda zasu iya kasancewa zagaye daku wajen haddasa min fitina” Bai jira amsarsu ba ya cigaba da faɗin, “Akan kwana, idan aka cire kwanaki bakwai miye tsarinku?”.
       Anan dai Fadwa ce kawai ta amsa, Anam kam dai shiru tayi. Fadwa tayi matuƙar danne raɗaɗin da takeji ta maye gurbinsa da murmushi, “Ni dai a nawa shawaran Soulmate kwana bibbiyun is ok ai ko?”.
   “Okayyy!”
Ya faɗa cikin ɗan jan y ɗin da maida dubansa da Anam, taƙi cewa komai, taƙi kuma yarda ta kalla kowa. Sai dai tana jin idanunsa masu kaifi a kanta, kanta ta sake duƙarwa da tura baki gaba dan ita kam kunya ma maganar ke bata, fahimtar hakan da yayi ya sashi ɗauke idonsa da faɗin, “Hakan yayi kawai. Duk mai girki itace zata ciyar da kowa na gidan nan abincin dare, zakuma muci tare anan. Na cire safiya da rana ne saboda mafi yawan lokaci ina fita da wuri, na rana kuma bana gida kowa zata iya ra’ayin kanta amma zata bama maigadina tilas. Sai dai a weekend zakuyi har na safe kamar dai gobe”. Ya ƙare maganar yana kallon Fadwa..
       Sam hakan baima Anam daɗi ba itama, amma batai magana ba. Fadwa dai ta amsa masa da “ALLAH yasa haka shi yafi alkairi”. Ya amsa da amin batare daya damu da rashin cewar Anam ɗin ba dan yasan a komai yanzu baƙuwace dole suyi mata uziri na kunyar zaƙewa akan wasu abubuwan har zuwa sanda zata zama ƴar gida. Daga haka ya rufe taron da addu’a. Anam ta fara miƙewa da nufin tafiyarta dan barcine cike da idonta har goma saura…
      “Bani yogurt ɗin”.
  Ya faɗa cikin katseta da bada umarni yana ƙoƙarin canja chennal a tv. Bata da zaɓin daya wuce dakatawar duk da idonta har lumshewa sukeyi. Amma hakan bai hanata ɗan tura baki ba dajin kamar ta saki kuka. Miƙewa Fadwa tai tana faɗin, “To ni bari naje na kwanta, sai da safenku”. Ta ƙare maganar da matsowa ta ɗan sumbaci gefen fuskarsa kamar ɗazun sannan ta fice tanama Anam ɗin saida safe itama.
       Sosai hakan ya soki zuciyar Anam, harta kasa amsa mata, ɗagowa yay ya ɗan kalleta yaga fuskarta kicin-kicin. Glass cup ɗin data cika da yogurt ɗin ta miƙa masa. Tsaii ya ɗanyi yana kallonta batare daya amsa ba, sai hakan ya ƙara tunzurata, ta ɗago idanunta dake cikin gilashi ta kallesa. Saurin janyewa tai tana ɗan yamutsa fuska. “Yaya dan ALLAH ka amsa zanje na kwanta barci nakeji”.
         Bai amsa ɗin ba, bai kuma daina kallonta ba, saita sake dubansa a marairaice kamar zatai kuka. Ɗan murmushin daya tsaya iya laɓɓa ya saki batare data gani ba, amsa yay da sake maida hankalinsa ga television ɗin. Ƙara miƙewar tai yunƙurinyi.
     “Ki jira na gama ki tafi da kayan”.
Ya faɗa batare daya kalleta ba. Ai kamar ta ƙwala kuka taji, amma sai ta koma ta zauna batare da tace dashi komai ba, jin sosai barcin na rinjayar idonta ta naɗe har ƙafafunta a kujerar kamar ɗazun. Kallonsa ya cigaba dayi yana shan yogurt ɗin da cin dubulan ɗin kaɗan-kaɗan har aka kammala hirar da yake kallo a tashar ta NTA da wani babban ɗan siyasa na jihar ta kano. Ya juyo da tunanin itama kallon take sai ya samu harma tayi barci. Kafe fuskar tata yay da kallo na wasu sakkanni kamar mai nazari, sai kuma ya kai hannu ya zare gilashin nata a hankali. Tashi yay ya fita, bai jima sosai ba ya dawo da keys ɗin sashenta a hanunsa ya ajiye…
        Motsawa tai, taɗan buɗe ido kaɗan saita gansa dishi-dishi, da farko ta zata yanar barcin data fara ɗaukarta ce, sai ta rumtse idon ta sake buɗewa amma still taji raunin ganinta a bayyane. Cikin sauri ta kai hannu ta shafa fuskarta, jin babu glass ɗinta ya sata kai hannu ta fara laluben cinyarta zuwa kujerar, dan falon babu fitila mai haske ya kashe. Hanun ta janye da sauri saboda sauka da yay a gurbin da bashi tai hasashen kaiwa ba. Shiko tamkar bai jitaba yay biris. Cike da borin kunya ta sauka a kujerar tana ƙara duddubawa, saida ta tabbatar dai ba gani zatai ba sannan ta dubesa fuska a tsume, sai dai shakkarsa bai hana bayyana cikin tsumewar tata ba.
     “Yaya MM gilashi na fa?”.
“Kin bani ajiya ne?”.
“Toni inma ban bakaba dai ai a falonka ya ɓata”……….✍

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button