BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 5

Typing????

 *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
       _(Miya kawo kishi?)_     *_Bilyn Abdull ce????????_*

Ƙarshen free page

05

………..Sun jima a ciki yana nunama Abie abubuwa, yanda yaketa faman bayani da murmushi saika rantse bashi baneba. Dan har dariya sukeyi tare da Abie. Kiran sallar la’asar ne ya fiddosu, hakan yayi dai-dai da shigowar ɗaya daga cikin ma’aikata office ɗin, sannan kuma dai-dai da farkawar Anam data sha barci hankali kwance sanyin ac ya gama ratsata.
        Shigowar ma’aikacin mai suna Abeed tazo masa a bazata, dan hankalinsa gaba ɗaya nakan system ɗin gabansa, sai sallamarsa da buɗe ƙofa ne a lokaci guda suka shiga kunnensa. Da sauri ya ɗago idanunsa batare daya amsa sallamar Abeed ɗin ba ya kai dubansa gareta. Anam da bata san mike faruwaba duk da itama taji sallamar tai yunƙurin miƙewa tana laluben veil ɗinta da nufin ɗan lulluɓama jikinta. Abie ya riga ya shige toilet ɗin cikin office ɗin ɗaura alwala tunkan sallamar Abeed….
       “You are vary stupid!! Zaka shigo min kai tsaye”.
A yanda yayma Abeed tsawar da jefa mata rigar suit ɗinsa dake a jikin hanger ba shi Abeed ɗin ba hatta ita sai da ta zabura. Da sauri ta ɗane kujerar baki ɗaya ta ƙudindune kanta dan sam bata ƙaunar tsawa a rayuwarta. Cikin rufewar ido da manta Abie na’a office ɗin ya sake dakama Abeed tsawa da cigaba da masa masifa. Shi dai yay ƙasa da kansa dan bai san laifinsa ba anan har yanzu, tunda ya san ya yi sallama ya kuma yi knocking….
        “Get out!!”.
Ya sake faɗa a tsawace. Da sauri Abeed yay baya da rufe ƙofar. A fusace ya maida dubansa ga Anam da ke leƙosu ta cikin rigarsa. Ya watsa mata wata uwar harara, cikin gargaɗi mai kaushi,
      “Idan kika ƙara fitowa da wannan ƴan iskan kayan saina kashe fuskarki da marukan da bazata ganuba. Stupid girl! An faɗa miki nan muna buƙatar sune”.
    Baki ta tura gaba duk da ta mugun tsorata da yanayinsa. “To ni Yaya MM wannan duk sune kayana ai, kuma ni su na iya saw…….”
    Ganin ya yunƙuro zai tashi ta miƙe da sauri ta koma bayan kujera fuska a kwaɓe. Ƙwafa yay da sake watsa mata harara. Abie dake tsaye da ga bakin ƙofa yana kallonsu tun ɗazun basu lura da shi ba yay murmushi, domin kuwa wasu abubuwa masu ban mamaki ya hango a cikin ƙwayar idon ɗan nasa, ya girgiza kai kawai da ƙarasowa ciki. Sai lokacin Shareff ya lura da shi. Ƙasa yay da kansa dan shi gaba ɗaya yama manta Abie na’a office ɗin. Miƙewa yay sum-sum ya nufi toilet batare da ya yarda sun haɗa ido da Abie ba. Shima baice masa komai ba sai binsa da yay da kallo kawai. Anam dake a laɓe sai da taga ya shige sannan ta fito, cikin taɓe fuska ta ƙaraso inda Abie yake tana faɗin,
     “Uhhm Abie ALLAH Yaya Shareff baida kirki, yanama staff ɗinsa ihu bai masa komaiba kuma”.
    Nanma murmushi kawai Abie yay baice komai ba. Zata ƙara magana Ya Shareff ɗin ya fito tai saurin komawa bayan Abie ta ɓuya. Sai dai hakan bai hanata ganin hararar daya watso mata ba.

★★★★★

         Washe gari su Abie suka wayi gari da shirin kai kuɗin auren Ya Shareff, wanda dama yana ɗaya daga cikin dalilinsa na zuwa Nigeria, dan data Anam ne kawai turota zaiyi tunda yasan akwai mai iya mata komai ai. Ita dai Anam bata san mike faruwaba ma, dan ta jima bata tashi a barcin safe ba kasancewar daren jiya tunda aka ɗauke wuta ta kasa komawa barci saboda zafi, duk da kuwa Mom ta kawo mata fan ta kunna mata saboda tsaki data dinga zubama su Husna kamar wata dangin tsaka, sai dai kuma fahimtar iya gaskiyarta ne yasa Ikram zuwa ta faɗowa Mom ɗin. Ganin akwatuna har set uku a falon Mom masu shegen ƙyau da tarin kayan sa rana ya sata tambayar Ya Khaleel first born ɗin Mom. Shima dai saurayine zangarere da shi dan yana shekara ta 26 a duniya. Khaleel ƙyaƙyƙyawa ne shima kuma nutsatstse. Sai dai akwai tsare gida da rashin son raini harma yafi Shareff zafi, dan shi Shareff inhar baka shiga gonarsa ba babu ruwansa da kai, sannan yana da sakewa da jama’a fiye da Khaleel. Shine na uku a haihuwa a gidan. Dan sanda Mom ta auri Abba haihuwar Mommy biyu ne. Daga Shareff sai Maheer da take goyo. Duk da Shareff ya bama Khaleel shekaru sosai hakan bai hana ƙaunar juna shiga tsakaninsu ba, dan tunda ya dawo daga Indonesia bashi da wani aboki a gidan kamar Khaleel. Da taimakonsa ya san wajaje da yawa daya manta, sannan tun a baya idan yazo hutu dama shine abokin yawonsa saboda nutsuwar yaron na birgesa. Yafi Maheer hankali sosai da sanin ciwon kansa, dan yanada himma da ƙwazon nema duk da ko maganar aure bayayi ma.
       Duk ɗaurewar Khaleel suna ɗan shiri da Anam, sai dai itama ba wani sake mata yake ba dan miskilanci a jininsa yake. Kamar bazai tanka mataba yanata aikin danna wayarsa sai kuma ya kalleta. “Kayan auren Yaya Shareff ne”.
      “Ya mi?! Dama aure zaiyi!?”.
A yanda tai maganar ya tilastashi sake dubanta da ƙyau, haka kawai yaji dariya ta taho masa. Amma sai ya gimtse.
       “Kinada matsala da auren nasa ne Granny”. (Dan haka yake kiranta mafi yawan lokaci).
     “Kuji Ya Khalel ɗin nan da wani magana. Ni ina ruwana da wani aurensa da har zai zamar min wani damuwa. Ai sai dai nai murna zai tafi can ya barmu mu huta matan ta kwashi baƙin hal……”
     Jin ta gagara ƙarasawa yasa Khaleel fashewa da dariya, dan dama dai tun ɗazun ya lura da Shareff daya fito daga bedroom ɗin Mom. Ita kuma sam ALLAH baisa ta lura ba sai yanzun da yaƙe ƙoƙarin baro corridor ɗin baki ɗaya dan dama kamar ya ɗan tsayane yana sauraren su, amma a zahiri waya yake dannawa. Duk da ba inda take yayo ba da gudu ta afka ɗakin barcin su harda murza key.
     Shiko dama daba inda take yayo ba harara kawai yawatsama Khaleel da faɗin, “Dalla tashi muje ka zauna kana abu kamar wani yaro”.
         Har yanzu dai dariya ƙunshe a bakin Khaleel ya miƙe. Idonsa na duban ƙofar da Anam ta shige. Suna ƙoƙarin fitowa yace, “ALLAH my best yariyar nan sam bata da wayo har yanzu. A hakan wai kuma ta kammala karatu. Bayan rashin wayon ƴan fari a jikinta harda taɓarama na ganin ita kaɗai ce a gaban su Mamie. Jiya fa harda kuka ta dinga yima su Mon wai zafi saida aka kawo fan aka kunna mata”.
      “Mom ɗince ta biye mata mtsoww ”.
Ya faɗa cikin halin ko in kula. Shi dai Khaleel yace, “Gara dai da aka kunna mata dan bata saba da zafin nan bane namu. Su da suke fama da dusan ƙanƙara ma wasu lokutan dan tsabar sanyi. Kaga ko tazo nan dole ta shiga wani yanayi dan kano ogace ta zafi..”
      Komai bai ƙara cewaba yay gaba Khaleel ya bisa.

     Kasancewar da Mom da Aunty Amarya sai wata ƙanwar Momy da yayarta za’aje yasa Anam maƙalema Mom sai taje. Mom bata hanata ba, dan ita tanada sauƙin kai sosai shiyyasa suke zaune lafiya da Mommy tsahon shekaru, duk da dai itama Mommy ɗin bawai tanada faɗa bane ko rikici, kawai dai ta tsani Mamie ne saboda tun farko akan hakan Gwaggo ta ginata, ta riga ta nuna mata shi Abie ɗan uba ne a cikin su Daddy duk da kuwa ba itace ta haifesu ba. Sai kuma ta kasance mace mai son komai ace itace sama da kowa, sannan a wajenta ake neman komai, a ganinta bazai yiyu ita matar farko a gidan ba, sannan mijinta shine babba ace wata a matan ta fita. Fin da Mamie ta mata kuma ya ƙara ƙiyayyar, itako Mom Abbah bai kai Daddy ba gaskiya, sai dai na waje bazai taɓa fahimtaba kasancewar ana ganinsu kansu a haɗe a koda yaushe kuma suna gida ɗaya ne.
      Kasancewar matar da Shareff ɗin zai aura ɗiyace ga gwaggo halima (ƙanwar daddy), kuma mahaifinta yaya a wajen mommy gawurtaccen ɗan siyasa mai muƙamin babba a jihar ta kano gidane katafare suka iso. Komai yaji na more rayuwa. Fadwa shine sunanta, ɗiya ga Alhaji Sadiq Dakata. Mahaifinta kamar Yayane ga Mommy. Dan da mahaifiyarsa, da Mahaifiyar Mommy da gwaggo duk uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Zumincine mai ƙarfi a tsakaninsu, dan haka ita da Gwaggo suka zaɓama Shareff Fadwa matsayin mata tunkan ya dawo gida Nigeria. Sunyi hakane a cewarsu dan kar Abie yay tunanin basa auren Anam. Da farko dai Shareff bai maida hankali ba duk da baice baya sonta ba. Sai da Mommy ta masa jan ido sannan ya ɗan ke kula Fadwa ɗin. Fadwa ƙyaƙyƙyawar yarinya ce gwargwado kuma ƴar gata, sannan kuma sele (celebritie) a social media, musamman tictok da istagram harma da twitter. Idan zan zauna fayyace muku wacece Fadwa zamu cinye labarinne a kanta. Kuje zuwa dai lokaci zai nuna muku ainahin Fadwa Sadiq Dakata.
     Sun sami tarba ta girma da girmamawa. Inda babu kunya Fadwa ta fito tare da tarin ƙawayenta da suka cika gidan kallon kaya tun a gaban su Mom. Yayinda su Abie ke can suna tattaunawa da su Alhaji Sadiq domin tsaida rana. Dama dai shine yace baya son aita jeka ka dawo, su haɗo komai rana ɗaya su kawo har sadaki sai kawai a tsaida ranar ɗaurin aure.
        Su dai su Mom wannan abu ya sakasu jin lallai akwai gyara a lamarin wannan amarya, duk da kuwa ƴar gida ce dan sun san wasu a cikin halayenta saboda kowa yasan ƴaƴan gwaggo Halima basu da ƙwaɓa. har cikin rai suna jin tausayin Shareff ɗin kasancewarsa bai wani cika zafi da yawan magana ba a mafi yawan lokuta. Amma sauran ƴan uwan Mommy da yake ƴan uwansune suma sai basuji komaiba a lamari, dan kuwa dai basu nuna a fuska ba sai dai in sun barma ransune suna nuna normal ne a zahiri.
       Fadwa tasan labarin Anam a wajen Mommy da Gwaggo da mahaifiyarta. Sai dai bata santa a zahiri ba sosai saboda gwaggo halima ba shiga duk abinda ya shafi su Abie take ba, tasha jin sunzo ƙasar tabi duk hanyar datai mata ta toshe haɗuwarsu sai idan wata fitinar suka shirya da su gwaggo shima ita kaɗai take zuwa babu ƴaƴanta. Hakan yasa yaranta basu wani san Abie ɗin bama balle ƴarsa, shima kuma bawani gama sanin ƴaƴanta yay ba tunda bata bari su raɓesa. Hakan yasa Fadwa bata nuna damuwarta da ganin Anam tare da su Mom ba. Amma dai yanda Anam ɗin ta zama miskila a wajen tana kallon komai ya ɗan ja hankalin su Fadwa da ƙawayenta gareta. Har takai babu kunya Fadwa na tambayar su Mom ina suka samo Anam ɗin?. Murmushi kawai Mom tai da faɗin “Itama ƙanwarki ce”. Daga haka ta tsuke bakinta duk da tambayar bin ƙoƙwanto da ƙawayen Fadwa ke cigaba da jefamasu Mom ɗin. Aunty Amarya dama bata tanka ba dan ita bata da farin jini a garesu kasancewarta kishiyar Mommy.
     Har dai suka baro gidan Fadwa da ƙawayenta basu san matsayin Anam ba. Ita kuma ta miskile ko ruwa bata sha ba a gidan har suka taho. Gwaggo halima ma duk da taga kamanin Abie a jikin ta kuma tasan sun zo bata tanka ba bata nuna komaiba.
Anam ma sai da suka ɗakko hanyar gida ta fara yima su Mom mitar Fadwa da ƙawayenta masu shegen rawar kan tsiya da nuna wayewa. Murmushi kawai Mom da Aunty sukeyi dan mota ɗaya suke su uku, ƴan uwan Mom ma na nasu su biyu.
      Bayan sun iso gida kowa yaji ainahin watan bikin a bakin su Abie. Nan da watanni biyu. Sauran yaran gidan nata murna duk da wannan ba shine karon farko da za’ai biki ba. Anyi bikin Rahma dake bima Khaleel, da Binta ƙanwar su Shareff dake bima Maheer. Yanzu Aysha ce a layi kuma sa’ar Anam ce dan watanni ta bama Anam ɗin kawai, itace ɗiyar Mommy ta biyar daga ita sai autoci su twins. Ga Anam kam babu dalili ta wani tsume sai kallonsu take da taɓe baki, har bayan magrib babu fara’a a tare da ita. Rashin walwalar tata yasa koda Aysha ta tambayeta. Sai tace ba komai.
     Sai bayan magrib suna hira duk kusan yaran gidan a falon aunty Amarya, gaba ɗaya hirar tasu ta ta’allaƙa ne akan shirin biki. Sai dai Anam taƙi tako tanka sai faman game take bugawa a waya. Sai dai kuma kunenta duk yana a garesu ne. Jin sun cigaba da damunta ta tashi zaune tana wani taɓe baki da harar Nusaiba mai gwada rehearsal na rawan da zasuyi wai a wajen dinner….
     “Kun wani dage sai tsara events kuke bayan amaryar ma ko aji bata da shi mtsoww!!”.
   Lokaci ɗaya falon yay tsit duk suka juyo suna kallonta. Hussaina ta ɗan waro ido da ƴar tsiwa tace, “Aiko dai aunty Fadwa nada aji gata ƙyaƙyƙyawa ƴar babban gida bama son jealous”.
       “Jealous!!. K! Hussaina dani kikeyi wai! kowa ma? Ni Juwairiyya ce zanyi jealous ɗin wancan farin ƙasan mai kama da ƴar tallan kasuwa. Baki da hankali”.
      A yanda take maganar a fusace yasa Hussaina tsorata, dan in tsiwa takeji Anam kakartace a iyawa. Amma shirun nata badan tsoron bane kawai, harda wanda idonta ya hango ya shigo falon ne yasa tai shiru. Anam kam da sam bataji ko sallamarsa ba sai faman faɗa take da sule Fadwa iya gaskiyarta. Tsaki ta doka da fisgar tab ɗinta dake hanun Hashim da nufin barin wajen, karaf idonta ya sauka a kansa. Yana tsaye tamkar an dasashi ya kafeta da manyan idanunsa masu razana wanda ya shiga gonarsa. Sosai gabanta ya faɗi, amma da yake ƴar gagiyar bata yarda aga gazawarta a fuska ba sai ta ɗaukesu cike da wani irin sallo da kaɗasu kamar mai harara ta nufi hanyar kitchen domin bi ta baya, dan tana shakkar bi ta gabansa tunda a ƙofar falo yake tsaye. Duk da bai nuna yama ji abinda tace ɗin ba hakan bai hana su Aysha ƙara nutsuwa ba.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button