AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 75-76

??75 and 76??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Bayan angama daurin auren, abban amal yacewa abban afham to yanzu ya zaayi maganar kai amarya amal gidanta “

abban afham yace “kowane lokaci suka tashi sukaita domin yasan komai daren dadewa afham zai dawo, abban afham yaci gaba dacewa “zan dafe duk wata kafa tafitar da kudina, tayyada bazai iya fitar da koda sisi bane daga cikin kudina sobada haka idan yaji matsuwar rashin kudi zaidawo”

Abban amal yace “to shikenan ajirashin harya dawo sai a kai masa matarsa”

Abban afham yayi godiya sosai, sannan sukayi sallama ya wuce office dinsa, yau daikam yacika burinsa,
Har bayan yazauna yafara aiki, yatuna dabai gayawa umman afham batun auren ba wayarsa yadauko yakirata yasanar da ita komai dayake faruwa, saida tamsa kuka a wayar,
Ransa yasoma baci da sauri ya kashe wayar,

Aneesah tana zaune a falo tatayar da kanta sama, momy tafito daga cikin dakinta tana hawaye takaraso gurin aneesah,

Ganin da aneesah tamata yasa tatashi zaune tana tambayarta ” momy lafiya kuwa “
Momy tace “an daura auren afham da amal, yanzun nan abbanki yakirani yasanar dani”

Aneesha taji gabanta yafadi, kafin tafara magana hawaye suka soma sauka kan kuma tunta tace ” taya za a daurawa mutum aure baya gari, wannan wlh amal aka cuta, Allah sarki amal” takarasa maganar tana kuka,

Momy ta katse mata kuka dacewa “kitashi kije kikara afham kiji koda ke zaki samesa, domin ni tun jiya nake kiraan wayarsa a kashe,”

Aneesha ta share hawayenta tace “nima tun dazu nake neman wayata bansan inda na jefa taba”

Momy tace “tashi kishiga dakinki mana kiduba”

Aneesah ta mike tsaye tace “toh momy” tana karasa maganar tanufi dakinta,

Duk saida tayiwa dakin kaca kaca amma bataga wayarba,
Haka ta hakura tabi lafiyar gado ta kwanta domin tagaji, bacci yadauketa zuciyarta cike da tunanin dan uwanta afham

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button