BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 53

Typing????

 *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
       _(Miya kawo kishi?)_     *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

53

………Da sallama ta shigo ɗauke da madaidaicin tray mai ƙyau, a samansa  madaidaiciyar butar shayi ce da kofinta ɗaya, sai tea spoon da sugar a ƙaramin bowl. Sai kuma plate dake rufe da robar ruwa ɗaya duk da tasan za’a iya samun ruwan a sashensa. Kaɗan ya juyo daga kallon tvn da yake ya ɗan dubeta, sai kuma ya ɗauke da amsa sallamarta akan lips. Gaba ɗayansu haushinsu yakeji dan kowacce da kalar laifin datai masa, sai dai yafi ganin sassaucin na Fadwa akan wannan tsiwatacciyar yarinyar da har yanzu maganganunta na ɗazun basu daina masa zafi a zuciya da ruhi ba.
      Ita dai da bata san yanayi ba ma koda ta gama zuba shayin ɗan ɗagowa tai ta dubesa da zata saka sugar. A taƙaice yace, “biyu” ya cigaba da kallonsa. Baki ta ɗan taɓe itama ta jefa masa biyun ta saka cokali. Plate ɗin datai warming sauran naman jiya daya kawo da dare ta zubo a ciki ta buɗe masa, sai sauran meatpie ɗinta da shima dai baiyi komaiba kasancewar a fridge yake shima dai tayi warming ɗin nasa.
      “Bani waya a bedroom”.
Ya faɗa dai-dai tana ɗagowa alamar ta kammala aikinta. Ganin yanda yake tsume-tsumen fuska ta wuce salin-alin batare da tace komai ba. Babu jimawa ta fito da wayar a hannu. Harya fara cin abincin hankalinsa rabi a tv. Nanma dai tana bashi tai ficewarta tabarsa.
       Motar da bata san kota wacece ba take shigowa gidan. Bata san wani a gidansu da motar ba, dan haka tai wucewarta batare da maida hankali ba dan maybe baƙin Fadwa ne kona mai gidan…

     “Kinga kallon da yarinyar can taima motarmu ta watsar kuwa Sakina?”.
     Hajiya Luba ƴar uwa ga Mommy kuma mahaifiya ga Bibah ta faɗa idonta akan Anaam dake shigewa sashenta. Aunty Sakinar ma kallon nata take, tai ƙwafa da ɓalle murfin motar ta fita. “Yaya Luba ba dole tai mana kallon banza ba tunda wanda ya kawota gidan ya nuna mata tafimu, yo ta fimu mana tunda ya zaɓeta sama da umarnin uwarsa ma”.
    “To aikuwa zasu ci ubansu daga shi har ita, dan zamu sauke mata abinda ke kanta yanda uwarta ta mallake ubanta mu anan AL-Mustapha yafi ƙarfin haka. Jiba yanda take yawo da wata ƴar iskar shiga dan ALLAH”.
        “Duk dama ta samu ai ke dai Yaya Luba, muje dai”.
Wanda ya kawosu babban ɗan Aunty Sakina ɗinne, ya girgiza kai duk zuciyarsa babu daɗi, dan shi dai baiga abinda yarinyar tayi ba suke cusa mata wannan zagin, shikam harma ya fara tausayin Yaya AL-Mustapha wlhy.

      Suko sashen Fadwa suka fara nufa, a falo suka sameta zaune tana shan lemun fata, mai-aikinta zaune daga ƙasa itama. Kallon sukeyi na wani horro film sai dai sam hankalin Fadwa ba gaba ɗaya yake akan film ɗin ba. Maman Abu ta miƙe tana musu sannu da zuwa. Da ƙyar suka amsa mata, bata damuba ta nufi kitchen ɗakko musu ruwa dan ba yau ta saba da halinsu ba tunda sanda tana can gidan su Fadwa ɗin ma suna zuwa babu kalar wulaƙancin da basa gani su masu aiki a wajensu su a dole ƙanen masu gida (Karku manta suma ƙanen uba suke ga Fadwa, kuma ƙanen uwa ga Shareff).
       “Baki da lafiya ne?”.
   Aunty Sakina ta faɗa idonta fas akan Fadwa. Kanta ta girgiza mata kawai. Baki aunty Sakinar ta taɓe. Hajiya Luba ta karɓe da faɗin, “Ciwo ya wuce baƙin cikin miji da kishiya mai kama da karuwai, k yanzu nan Fadwa har waccan ƴar tsefatar yarinyar ce zata razanaki ki koma haka firingau-firingau ido luhu-luhu. Kuka kenan kika zauna kinayi kamar wata sakara?”.
     Hawayen da taketa riƙewa ne suka silalo mata. Aunty Sakina da Hajiya Luba suka ɗauki sallallami da tafi kamar waɗanda sukai gamo. Ita dai Fadwa kanta a ƙasa tana hawayenta.
  “A to wlhy aiki ya ganki kuwa, yima kishiya kuka. Kishiyarma wadda bata wuci a sati ki kaɗa shegiya ba tabar gidan saboda ke ɗin shashashar ce kika zauna kinamata kuka. To bara kiji, idan zaki dawo cikin hankalinki ki dawo, a duk zuri’armu babu sakarai. Balle ke da mijin nan naki tako ina jininki ne, da ubansa da uwarki uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, da ubanki da uwarsa iyayensu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Gaba da baya aka tsaga jikinku jini iri ɗaya za’a gani, itako fa miye haɗinsa da ita banda ɗiyar ɗan uban ubansa, dalla malama sharemin waɗan nan banzayen hawayen ki tashi ki rakamu sashen shegiyar”.
     Hawayen Fadwa ta share, sai dai kuma tuna yana gidan yasa ta kasa tashi. “Aunty yana nan fa a gida”.
    “Shi wa ɗin?”.
Cewar Hajiya Luba.
“Shareff! Yau bai fita aiki ba wai hutu ya ɗauka harna sati ɗaya”. Ta ƙare faɗa da rushewa da kuka tabbacin abinda ke cin zuciyarta kenan tun ɗazun.
     Cikin riƙe baki Aunty Sakina tace, “Iyee wato sati guda, amma uwarsa nacan ko sau ɗaya baije ya gaisheta ba. Shiko dai Al-Mustapha yayi asara. Aini namaji daɗin samun nasa a gidan zanfi jin daɗin cin uban shegiyar yarinyar a gaban nasa sallamamme kawai. Tashi muje ki kaimu, kuma karna sake ganin waɗan nan hawayen banzar kema shashasha”.
     
      Anaam na kwance cikin kujera tana buga game suka faɗo mata ko sallama babu. Da farko tayi kamar ta share dan Fadwa ce ta fara shigowa, sai dai ganin su Aunty Sakina ya sa ta tashi zaune tana danne sosuwar da zuciyarta tayi akan shigo mata kai tsaye da sukai. Ta san aunty Sakina dan sun taɓa zuwa gidanta ita da Aysha. Daga Hajiya Luba har aunty Sakina bin falon suke da kallo baki a taɓe, sai dai acan ƙasan ransu razani ne na gaske, dan ko makaho ya shigo ya laluba yasan annunama duniya yariyar ƴar gata ce…..
       Cigaba da game ɗinta tai domin basu dama su gama kalle-kallen, saiko da sukai iya iyawa sannan suka juyo gareta.
    “Oh lallai, ga ƴan iska sun shigo ko?”.
Aunty Sakina ta faɗa murya a sama. A karan farko Anaam ta saki murmushi, ta ɗago idanunta dake cikin gilashi tana kallonsu, cikin hausarta dabai gama nuna ba ta gaishesu kamarma bata fahimci harzuƙowar aunty Sakinar ba..
          “Uhm lallai kam Shareff ka amshi ruwan dafa kanka. Wato k a dole ƴar bariki”.
     Sarai ta fahimci abinda Hajiya Luban ta faɗa, dan kuwa zuwa yanzu Alhmdllhi hausa ta fara zauna mata a brain da harshe da ƙyau saɓanin farkon zuwanta. Amma sai tai kamar bata fahimci komai ba, fuskarta da murmushi ta miƙe tana faɗin, “Aunty ku zauna Please bara na kawo muku ruwa”. Bata jira cewarsu ba ta nufi kitchen.
     “Babbar br uba kai. Wai wannan yarinyar tana nufin bama tajin mi muke faɗa ko mi?”.
   Fadwa da batace komaiba tun shigowarsu tana kuma daga tsaye dan bata zauna ba tace, “Hummm! Tana jin komai sarai iskanci ne kawai fa Aunty. Ni dama kun barta dan ALLAH kawai….”
        Harara Hajiya Luba ta zuba mata. Shigowar Shareff a bazata ta saka Fadwa haɗiye abinda zata faɗa babu shiri da risinar da kanta ƙasa, wani yawu mai kauri ya wuce muƙut a maƙoshinta ƙirjinta na bugawa.
        Idanunsa ya janye a kanta da ƙarasowa cikin falon hannayensa duk biyu a cikin aljihun wandonsa.
   “Oh dama kana gidan?”.
Aunty Sakina ta faɗa tana hararsa.
Duk da sarai ya jita sai bai amsa ba, sai da yakai zaune cikin kujera da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ya dubesu. “Barkanku da safiya aunty kune a gidan namu?”.
     Sosai ransu ya sosu da salon rainin wayonsa su duka. Sai dai kafin wani yace wani abu a cikinsu Anaam ta fito ɗauke da tray shaƙe da kayan ciye-ciye da ruwa da lemo. Itama dai ta ɗanji wani iri na ganin nasa, amma saita fiske abinta ta ajiye tray ɗin a gabansu tana murmushi. “Aunty ga ruwa to….”
        A matuƙar harziƙe Hajiya Luba ta tura tray ɗin da ƙafarta tana ballama Anaam harara. “Tunda shine ya kawomu ba, k ki kama kanki wadda ta haifeki ma a tafin hanunmu take balle ke kanki…”
     “Juwairiyya bani lap-top dana bari a ɗakinki”. Shareff ya katse hargowar Hajiya Luba tamkar bai ji mima take faɗa ba. Tsamm Anaam ta miƙe batare da tace uffan ba, ba kuma ta kalli sashen da Shareff ɗin yake ba balle Fadwa ta ɗauka wayarta ta wuce bedroom.
         “Oh ke ko ga mahaukata suna magana dole ka sata aika. K! Fadwa shaƙomin ƴar iskar yarinyar can na nuna mata wacece ni dan ubanta”.
     Muƙutt Fadwa ta haɗiyi yawu da ƙyar a karo na biyu domin jin umarnin Aunty Sakina tamkar saukar aradu bisa kai. Ta ɗan saci kallon inda Shareff ke zaune a harɗe har yanzu kai kace baima san wainar da ake toyawa a falon ba. Kanta ta girgiza a hankali, so take tayi magana amma ta kasa motsa lips ɗinta sai kawai ta juya da sauri ta bar falon ma gaba ɗaya. (Tabbas Fadwa nada kurari da hayaƙi, amma kuma tanada tsoro bata cika iya jure hatsaniyar faɗa ba. Idan mai karatu bai manta ba kokuma ya lura da ƙyau zai fahimci Anaam ta fita tsiwa, saboda a lokuta da dama takan takaleta faɗa amma a ƙarshe Anaam ɗin ke tsigeta itako sai tai laƙwas. Tabbas a cikin raunanan halayanta wannan yana ciki rashin juriyar hatsaniya, a wani fannin kuma zamu iya kiransa haƙuri????).
      Daga aunty Sakina har Hajiya Luba baki suka saki uwa sakatar sakarai dan al’ajabin Fadwa. “Oh ni Sakina ato lallai Fadwa kema kin cika asararriyar yarinya, to kodai ba Al-Mustapha ɗin kawai aka shanye ba harda ke ɗin kema?”.
     Maimakon samun amsa daga Fadwa data fice sai Hajiya Luba ce ta amsawa Aunty Sakinar. “A to ga halama kin gani kuwa Sakina. Ƙanƙanuwar yarinya ke juya gida miji da kishiya duka a tafin hanunta.”
       Ƙololuwar ɓacin rai kam Aunty Sakina takai, musamman biris da su da Shareff yayi. Tsabar wulaƙanci ma sai latsa wayarsa yake yana ɗan girgiza ƙafarsa da yay crossing. Anaam dake danne dariyarta da jinjina tsaurin idon mutumin nan ta ƙaraso ɗauke da lap-top ɗin a hannu. Gabansa gab ta matsa, ta miƙa masa harda takardun data haɗo da su. Idanunsa dake akan wayar ya ɗago yana kallonta, ta ɗan tura baki gaba tana son dangwarar da kayan bisa cinyarsa ya riƙo hanunta. Fuska ta ɗan narke da ƙyaƙyƙyafta idanu tai ƙoƙarin janye hanunta………✍

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button