FARHATAL-QALB

FARHATAL-QALB 10

PG:10_

××××××.      

××Bayan anyi addu’oin bude taro da addua. An kuma karanto jadawalin da za’ayi acikin taron. Mai girma mai babban taro bayan an bashi dama. Nan ya fara bayani cikin kwarewa da kuma yi bisa tsarin dakkan dakka wato daki daki,

“The term “sickler” is often used by medical practitioners to refer to children and adults with a diagnosis of sickle cell disease (SCD) .Noun. sickler (plural sicklers) One who uses a sickle; a sickleman (medicine, informal) A person who has sickle-cell disease.) A hausan ce muna cewa:. Ma’anar cutar sikila,

“Cutar sickler tana nufin mutum yana dauke da sinadaran haemoglobin guda biyu marasa kyau (ba lafiyayyu ba) a jikinsa. Ma’ana dai ya gaji gurbatattun sinadaren haemoglobin daga wurin mahaifiya da mahaifi

“Yadda ake samun cutar sikila: Ana samun cutar sickler ne daga wurin iyaye (uwa da uba). Uba shi kadai ba zai iya haifar da/’ƴa mai sickler ba, haka ma uwa ita kadai ba za ta iya haifar da/’ƴa mai sickler ba. Dole sai da gudunmawar kowanne daga cikinsu (uwa da uba). Kowane mutum yana da sinadaren haemoglobin a jikinsa nau’i biyu. Zan yi magana a kan haemoglobin A da kuma haemoglobin S kawai saboda su ne suka fi yawa. kowane mutum yana da daya daga cikin wadannan Haemoglobin ɗin:

(1) Haemoglobin AA (HbAA)

(2) Haemoglobin AS (HbAS)

(3) Haemoglobin SS (AbSS)

“Wanda HbAA yana da lafiyayyun haemoglobin guda biyu. Mai HbAS yana da lafiyayyen Haemoglobin guda daya da kuma wanda ba lafiyayye ba (ba mai kyan ba) guda daya, Mai HbSS yana da haemoglobin guda biyu marasa kyau.
Mai HbAA lafiya kalau yake. Ma’ana ba shi da ciwon sickler. Mai HbAS shima lafiya kalau yake, ba shi da ciwon sickler, amma zai iya haifar da/’ƴa mai sickler idan ya auri mai HbAS. Don haka, HbAS shi ake kira da ‚carrier‛

“Mai HbSS, shi ne yake da ciwon sickler: lokacin da za a halicci mutum a cikin mahaifiyarsa, uwa tana ba da gudunmawar haemoglobin guda daya, sannan uba ma yana bada gudunmawar haemoglobin guda daya. Idan uba ya bada gudunmawar haemoglobin maras kyau (HbS) sannan uwa ma ta bada gudunmawar haemoglobin maras kyau (HbS), to tabbas dan da za’a haifa, zai kasance sickler ne (HbSS). Kuna ganewa ko?”

“Eh…” Suka hada baki wajen amsa shi.

Ya sake gyara tsayuwar sa kafin ya cigaba da cewa,

” Ga dai yadda za ta kasance idan aka yi aure.

Iyaye (Uwa da Uba)

Yanayin ‘Ya’Ya

AA da AA AA a kowane Lokaci
AA da AS AA, ko Kuma AS
AS da AS AA ko AS ko SS
AS da SS AS ko kuma SS
SS da SS SS a kowane lokaci
AA da SS AS a kowane lokaci
Don haka, idan ana so a kauce wa cutar sikila, to kada a yi aure tsakanin.

‘AS’ da ‘AS’,

‘AS’ da ‘SS’,

‘SS’ da ‘SS’.

” Kun fahimce ni ko?”

“Mun fahimta dakta.”

“Toh akwai Alamomin cutar sikila: Suna bayyana ne tun yaro yana karami a mafi yawancin lokaci. Alamomin sun hada da: kumburin ƴan yatsu, Ciwon kashi mai tsanani, Dashewar jiki (karancin jini) Kankantar jiki da sauransu

“Sai kuma wasu daga cikin illolin ciwon Domin shi ciwon sickler yana haifar da illoli daban–daban, kamar:
Yawan rashin lafiya akai–akai kamar ciwon kashi, ƙirji, ciki da sauransu
Shanyewar barin jiki (stroke)
Ciwon koda
Rashin zuwa makaranta ko kuma yawan tangardar karatu
Yawan karancin jini
Shaye–shaye
Saurin mutuwa (mutuwa lokacin kuruciya da sauransu). Ba wai ana nufin su mutu kafin lokacin su ba. A’ah ba haka nake nufi ba. Ina nufin wahalar da suke sha su kuma zo su rasu wasunsu da karancin shekaru. Sannan akwai bangaren

“Maganin ciwon sikila: Babban maganin ciwon sickler shi ne kada a yi aure idan akwai yiwuwar a haifi da mai sikila. Kuma ana iya gane haka ta hanyar yin gwajin genotype. Amma idan ciwon ya samu, to hanya daya ce wadda ake iya maganin wannan cuta., Kuna saurara ko?”

“Eh… To Marka kinji dai ko?” Cewar najan Isubu. Ta juya kofar kunnen Marka tana gaya mata.

“Ina ji ai.”

“Yauwa ai na gayan ki.”

“Uhm….” Marka ta juyar da kanta gefe kawai tana harare harare.

“Yauwa hanyar ita ce, dashen baargo, A turance muna kiran sa da: (Bone marrow transplant), shi wannan dashen bargo yana tare da irin tasa matsalolin kuma ba kowane lokaci ake yin nasarar warkewa ba. Sannan kuma yana da tsada matuka da gaske… Dan cikin kaso dari bebi kashi daya ne ke yi ba. Kuma acikin kashi dayan. Rabi da kwata ba sa rayuwa. Ragowar ne nasara wani lokacin. Domin shi sauki ko akasin sa ai daga Allah ne…. Ina fatan kuna tare da ni?”

“Muna sauraron ka Dakta.”

“Yauwa to: Ana ba wa masu sickler wasu magunguna domin samun saukin rashin lafiya akai-akai. Shi yasa ake so masu sickler su dinga zuwa wajen likita lokaci zuwa lokaci, koda babu abin da suke ji na rashin lafiya… Domin dik cutar da ake kokarin takatsantsan da ita ana bin ka’idoji da tsare tsare da dokokin da likita ya gindaya to babu shakka wani kaso daga cikin cutar zai ragu. Musanman idan ana hadawa da addu’oi ana kuma fawwalawa Allah lamurra.. Sannan inason sanar da ku wasu daga cikin: Abubuwan da suke tayar da rashin lafiya ga masu ciwon sikila sune’:

“Zafi mai tsanani
Zazzabi (ko na malaria ko kuma wani abu daban, Motsa jiki mai yawa
Bacin rai. Da sauransu, Don haka yana da kyau a kaucewa wadannnan abubuwan. Sai daga karshe, Ciwon sickler yana saka rashin lafiya akai–akai, yana hana jin dadin rayuwa, sannan kuma yana sanadiyar mutuwar mutum yana karami. Ana iya kaucewa ciwon idan aka bi shawarwarin likitoci ta hanyar yin gwajin genotype… Na hada ku da girman Allah kada ku aurar da ‘yayayen ku haka sakaka ba tare da anyi gwaje gwaje ba. Mu likitoci mumu ka san wahalar da suke sha.

“Wadannan mutane masu lalurar sikila ababen tausayawa ne ga duk wanda yake tare da su. Dan Allah a rage yawan yaduwar wannan ciwon ta hanyar yin gwaji. Idan an gwada komai kalau to shikenan sai ayi auren . Idan kuma an samu akasin haka to fasawar auren itace mafi alkhairi. Saboda idan an haifi yaran ma su zasu yita shan wahala. Iyaye yan sannu ne. Sai dai suyi wahala da jikin su day kuma dukiyar su. A zamanin baya kai bai waye ba. Haka iyayen mu sukayi auren su suka hayayyafe mu. Amman Alhamdulillah yanzu kai ya waye. Cutar nata yaduwa. Allah ya temaka zamani ya zo da abubuwan gwaji da zaa debi jinin ka agano kanada cuta kaza ko babu. ?

“Abunda ya saka kenan. Kungiyar mu ta ma’aikatan lapia da ke wakiltar reshen karamar hukumar shurah. Muka tsaya tsayin daka wajen ganin munyi da gumin mu da aljihun mu wajen yaki da wannan cuta. Kuma Alhamdulillah mun samu nasarar Allah aciki komai ya tabbata kamar yadda muka tsara. Zamu debi lokaci wajen yiwa dukkanin al’ummar unguwar nan gwaji dan tsare rayuka daga fadawa halakar wannan cuta mai sanmatsi. Muna kuma fatan zaku bamu hadin kai muyi wannan tafiya tare. ?”

“In shaa Allahu!”

“Toh Masha Allah . Duka Duka anan zamu dakata. Zakuma mubi gida gidah mu dau kidayar yawan su. Ta hakane sauran ma’aikatan mu zasu rarrabu su kuma yi wa kowanne gidah gwaje gwaje da kuma abubuwan da suka dace. Mungode kwarai da ara mana lokutan ku da kuka yiyyi. Munyi farin ciki, Mun kuma ji dadi. Allah kuma ya hadamu a ladan duka. Amin.! Malam a yi mana adduar rufe taro. “

Malamin ya hau kan dan tudun ya shigaa janyo addu’oin rufe taro. Aka karasa. Jami’an suka shigaa bin gidah gidah suna daukar sunayen su da kuma adadin yawan su. A ranar aka fara dibar jinin wasu daga ciki. Sati biyu zasuyi su kammala komai.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button