BABU SO 57
Sabon ragwanci da raki ya ƙara ɓarkewa a toilet yayin yake taimaka mata wajen samun nutsuwa dan ya fahimci wannan itace masalaha ta farko daya kamata ya bata agaji da ita. Kuka take masa sosai irin wanda yafi na farko dan a ɗazun wahala ta hanata yin kukan. Yanzu kam saita samu damar ɓarje guminta wajen yinsa fiye da abinda takeji. Rashin ƙarfin jiki ya tilastata sallama masa dole yana jujjuyata a yanda yake so cikin ruwan zafin. Koba komai ta ɗanji sassauci, sai dai hawayeta sun gagara tsayawa dan su kaɗai ne abinda take iyayi wajen nuna irin raɗaɗin da takeji da galabaitar da rayuwarta da yayi. A cikin ruwan ya barota ya fito, ya kintsa gadon ta hanyar canja bedsheet sannan ya koma fito da ita. Har cikin rai tausayi take bashi, duk da ya fahimci rakinta ne gaba-gaba wajen sake girmama narkewar tata. Koma dai minene ai shi ya takaloma kansa tunda yasan hali. Tun yana hasashen zatai haƙuri tai shiru sai saɓanin haka ya biyo baya, dan kuwa ƙiri-ƙiri ta hanasu barci sai gabanin asuba da ɓarawon yaci galaba a kanta. Kansa ya girgiza kawai, dan bai taɓa sanin darun yarinyar nan da rikicinta yakai faɗin haka ba sai a yau. Rashin barcin da wuri ya jawo musu makara. Bai fara tashinta ba sai da ya idar da tasa sallar, abinda yake gudunne kuwa ya faru, dan rikice masan ta farayi da kuku wuwu. Haka kawai yake jin nauyi da kunyarta shi kansa, domin yasan dai magana ta ƙare tunda a daren jiya ta gama ganin ƙarshen girmansa duk da matsayin ƙanwa da take da shi a garesa. Da farko ya lallaɓata har tai salla, ganin fa bata san zuru ba ya rumtse ido cike da borin kunya ya balbaleta da masifar da bata kai ciki ba, dan da ƙarfin hali yake yinta kawai….
“Kin isheni fa da kuka. Idan baki rufamin bakinki da kukan banzar nan ba ALLAH yagalgalaki zanyi da safen nan, dan na fahimci kukan naki harda na rashin ƙoshin dalilin yinsa…”
Kukan ta sake fashe masa da shi tana duƙunƙune kanta cikin bargo, dan hatta muryarsa razani take saka mata a zuciya. Tsoronsa takeji mai girma da tsananin shakkarsa. Ta cigaba da hawayenta batare da barin sautin kukan na fita ba sai dai yana jin yanda take jaa da shaƙar ajiyar zuciya tamkar zata shiɗe. Tashi yay ya fita, mintuna kaɗan sai gashi da kofin shayi. Yasan halin butsutsunta, dan haka ya ɗaure fuska cikin bada umarni yace ta tashi. Duk yanda taso zama da ƙyau domin shakkarsa ta gagara hakan, dole sai jinginata yay da jikinsa zuciyarsa na raya masa akwai matsala kenan. Da kansa ya bata tea ɗin tana sha da ƙyar, ko rabi bataiba tace ta ƙoshi. Bai barta ba har sai da ta ƙara sha, ya bata paracetamol dan jikinta akwai zazzaɓi. Kwanciya yay da sakata jikinsa yana shafa bayanta, sai kuma ya sumbaci kanta dake a ƙirjinsa da ƙara rungumeta da ƙyau, cikin lallashi ya fara magana a kunnenta…
“Kukan ya isa haka to mai tsadar tsada uhhmyim. Ko kina so a dinga kiranki raguwa ne? Jarumar mace bata irin wannan rakin da kike yi ai. Bakinki taf da tsiwa amma sai ragwantaka”.
Kukan ta sake fashe masa dashi da son turesa a jikinta amma bata da ƙarfi, yay murmushi da sake sumbatar kanta. “Oh ashe kinada sauran ƙarfi ma na wani zauna kallonki, bara na sake komawa kawai ko zan ƙara farauto baby na uku, dan insha ALLAHU jiya dai na samar da biyu da zakiyi tukuyci da su………✍