FARHATAL-QALB

FARHATAL-QALB 16

PG:16_

“A tsallaken unguwar nan ta gaba. Inda ake kira da Mahe janshan.”

“Oh okay nagane inda take fada Maa. Wajen gidan su Ibro me gadi. Mahe junction.”

“Oh okay nagane….. “

“Eh to.. Ta nan unguwar taku suke bi su karasa makarantar saboda yafu kusa. Tsallaka titi kawai zasuyi. Idan ta unguwar mu ne kuwa sai sunyi shatale tale.”

“Eh gaskia kam tanan din zai fi. Allah basu sa’a.”

“Aamin Yaa rabbi Hajia.”

“Secondary kenan?”

“Eh sakandire. Tana aji na daya na babbar sakandire. Sauran aji biyu ta kammala.”

“Allah sarki … Ashe ma ba wata babba bace. “

“Eh .. Daga yayan su sai ita. Dan akwai tazarar shekaru ma tsakanin su. Sai kaninta Najib. Shekara daya da wata biyar ne a tsakanin su ita da shi”

“Allah sarki. Allah raya su duka “

“Aamin Yaa Rabbi …”

“Maa! Abincin.”

“Idan na gidah kake so yana kitchen. Na Zayn kuma ya ..”

“Ah banason na akhi. Maa.”

Nadra na daga dinning ta kufce da dariya harda kyakyatawa. Itama Umma Hadiza ta murmusa .

“Ai haka suke . Basuda aiki se tsokanar yayan su “

“Allah sarki… “

Cikin haka sai ga sakkowar dan autan ta Moha daga sama. Sanye cikin kayan bacci yanata murmurza idanu

“Maaa .”

“Habibi…. Zo, Ka tashi?”

“Uhm…”

Da gudu ya rungumeta. Ta dora shi akan cinyarta .

“Baka gaysheta ba.”

“Ina wuni ?”

“Lapia kalau dan baby. Ka tashi daga baccin?”

“Uhm…”

“Me zaka ci? Oats da pancake ?”

“Nadra je ki masa reheating tun dazu daman na yi masa “

“Okay Maa.”

“Kayi brush?”

“Eh ..”

“Ka kuskure da mouthwash dinka?”

“Uhm uhm”

“Muje a kuskure. Monday dai insha Allah zakay resuming school. “

Riko hannun sa tayi suka hau saman tare. Daga kuskura bakin ta hada masa da wanka. Ta sauya masa kaya zuwa English wears. Riga da wando na jeans. Rigar spider man.

Sannan suka sakko tare. Ta zura bakar abaya ta yane kanta da mayafin abayar. Dayan hannunta kuma rike da jaka.

“Nadra ki hada masa komai. Ni zan tafi asibiti “

“Okay Maa “

“Hajia fita zaki yi?” Cewar Umma Hadiza. Ta miqe daga zaunen da take

“Eh nace miki inada tiyata dazu ko? Toh zan tafi yanzu ne. Lokacin ya kusa.”

“Allah ya temaka, Amin”

“Aamin Yaa rabbi. Bazan wani jima ba zan dawo insha Allah “

“To Hajia Allah ya bada saa yasa ayi aikin cikin nasara “

“Allahumma Aamin Hadiza.”

“Akwai abunda zaayi?”

“Kai babu gaskia. Sai dai.. ko..ko ko dauraye ledar abincin can kawai. Kuma dan Allah ki zauna kici abincin nan kafin a gama na rana kinji ko? Da wanda Zayn ya bari duk ki hade.”

“Insha Allah Hajia. “

“Yauwa, Sai na dawo “

“Sai kin dawo. Allah ya tsare hanya Amin.”

“Amin Yaa rabbi. “

Nan da nan ta isa ga wajen dinning area ta dauki ledar da aka jera abincin akai ta fita da ita wajen famfon wajen. Ta kada omo tayi masa sabi uku ta dauraye ta shanya. .

Ko data kammala. Abincin ta dakko na wajen Zayn dana kitchen din ta hade su waje daya tana kallo

Kayan dadi ne fal. Don wainar kwai ma fala fala har 3 masu nauyi. Nan da nan ta daddauki komi ta raba kashi 3. Taci kashi daya ta kora da ruwa.

Gyatsa tayi ahankali. Ta dora da hamdala tana kambama kyautatawa irin ta Hajia Hameeda da yaranta.

Yar tabarmar dake gefen sink ta janyo ta shimfida ta kishingida. Dake akwai ac a kitchen din. Sanyi mai dadi ya kama ciki da wajen sa. Nan da nan wani daddadan bacci ya shiga fuzgarta. Har dai yayi nasarar dauke ta. Ta shiga bacci tana sauke numfashi ahankali .


 Koda ya fita, Direct mota ya shiga ya tada ta ya tafi construction site dinsu. 

Nan dinma bai wani mayar da hankali sosai ba. Illa dai ya dudduba files ya kuma ciccike abubuwan da suka kamata hade da saka hannu a wasu ayyukan.

Ya kwantar da kansa ajikin kujera . Yayin ya kallon sa ya koma saman pop. Hankalin sa da nutsuwar sa suka tafi izuwa yanayin daya samu kansa dazu da Waheedah.

Ya rasa mai yasa gaba daya tunanin yanayin su na dazu ya kasa fita daga kwakwalwar sa. Zuciar sa na masa zillo. Yayinda ransa ke hasaso masa wasu tunanin na daban.

Wayar sa nata agajin dauka. Baki daya hankalin sa baya kai sam bai ji ba. Sai da akayi knocking kofar ofishin sau 3 tukun sannan ya samu kansa da dawowar tunani.

“Yes….”

Sakataren sa ne ya shiga ofishin . Cikin girmamawa yace da shi,

“Ranka ya dade. Me gidah wai yana kira baka dauka, Yace ka kira shi idan ka karasa abunda kake.”

“Okay tohm.”

Sakataren na fita, Zayn ya dau wayar sa da sauri yana dubawa. Tabbas mahaifin na su ya kira sa har sau uku bai dauka ba.

Cikin sauri ya kira shi ya na mai gyara zaman airpod din kunnen sa.

“Assalam Abiey… Eh! Barka da rana. Afuwan Abiey. Okay Ummimi? Alright zan je yanzu naga abubuwan da suka dace a sayo. Tohm. A huta lapia.” Yana gama wayar ya zurata a aljihun gaban rigar sa.

Tashi yayi daga kan kujerar ya fice daga cikin ofishin. Kai tsaye ya wuce wajen motar sa. Ya shige ciki ya nufi hanyar gidah kai tsaye.

Kan titin da zai shigar da kai kan hanyar zuwa gidan su ta baya . Wata mota ta mutu akan titin. Wadda ta haddasa go slow sosai. Gashi irin babbar gingimarinnan ce tafkekiya mai dauke da shanu aciki. Kuma motar zatayi U-turn sai ta tsaya chak ta lalace awajen.

Hakan yasa motocin da zasu shige . Da wanda zasu miqe da masu yin kwana duk sun tsaya chak. Ba dama ka juya ka canza hanya. Traffic din ya riga da yayi jamming .

Takaicin hakan yasa Zayn sakin siririn tsaki. Ya kara ac hade da saukar da kujerar sa tayi baya. Ya dan kwantar da kansa.

Wayar sa ya janyo yana duba mails. Chan ya koma kan Whatsapp . Group dinsu na dangin THE ADAMS FAMILY ya hada tarun sakonni fal.

Shiga yayi da niyar clearing ya ga hotuna rututu sunata turawa. Harda na Ahlam data turo bakin style din the bratz.

Nan danan ya danna button din clearing ba tare dayabi kan tattaunawar sa suke ba. Ya kashe datar ya ajiye wayar a agefe.

Cikin haka sai ga dandazon yan makarantar government senior secondary school shurah an ta so su. Sunata tudadowa.

Dake titin a tsaye yake chak saboda motar data lalace, Hakan ya sanya daliban samun damar wucewa hankulan su a kwance.

Waheedah da ke tafe tare da su Hindu Allah Allah take ta koma gidah. Saboda yadda kanta ke sara mata.

Tamkar ance ya dago. Ya samu kansa da sauke kwayar idanun sa akan…..

❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????

ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al’amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA

Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?

Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K’ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane

????????????????????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button