BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 58

58

……..Hanunta take ɗagawa daƙyar tana kai masa ƙananun duka, ya fara ƴar dariya da ƙoƙarin riƙe hannayen nata. Duk yanda yaso su koma barci hakan ya gagara, dan ƙorafinta na zafi da raki ya gagara tsayawa. Ga zazzaɓi mai zafi dake ƙara rufeta bayan sauka ya kamata yayi tunda tasha magani. Dole ya tashi zaune da ita a jikinsa yana ƙoƙarin son su haɗa ido amma taƙi yarda. Bai damu da hakan ba, dan yasan kunya dole ce. Shi kansa wani nauyi yakeji amma yana ta ƙoƙarin ganin ya fuske abinsa..

   “Faɗamin miye matsalarki kuma Noorii na?”.

Shiru ta kasa bashi amsa, sai ƙoƙarin son kauda kanta kuma take yaƙi bata dama. Dole ta buɗe baki muryarta a ɗashe irin ta wanda yaci kuka ya more, dan ko fita batayi da ƙyau. “Inajin zafi mai raɗaɗi, dan ALLAH ka kiramin Mamie ko ka kaini wajenta”.

    A ransa yace, (Ko ɗaya a ciki bazaki samu ba) a zahiri kam wayarsa ya ɗauka zuciyarsa na masa kaikawo akan waya dace ya kira. Har yai dailing number Dr Jamal sai kuma ya katse, text message ya tura masa. mintuna kaɗan kuwa sai ga kiransa. Kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗaga da miƙewa ya fice a ɗakin.

   “Malam ba kirana nace kayi ba, Nurse daka aminta da ita nace ka turamin”.

      Dr Jamal yay murmushi da shafa kai daga can, “Oh to ai ko asibitin ban fitaba shiyyasa nace bara na kiraka naji waye babu lafiya?”. Jimm yay na wasu ƴan sakkani, sai kuma ya furzar da huci a hankali ya furta “Juwairiyya!”.

  “Ayya ALLAH ya bata lafiya, mizai hana ka kaita asibiti kawai sai mu haɗu, dan gaskiya a iya hasashena ban san wace Nurse zan tura maka ba indai irin wadda nasan zaka buƙata ce. Amma Dr Bilkisu na tabbatar ta iso yanzu zatafi kulawa da ita da sanin matsalarta kai tsaye inma mune baka son mu duba maka ita..”

   “Kai ka sani”.

Ya bashi amsa a taƙaice da yanke wayar. Daga can Dr Jamal yay ƴar dariya da ajiye wayar ƙasan zuciyarsa na masa kaikawo amma yana turewa dan yayi alƙawarin mantawa da ita, zai cigaba da mata kallone kawai irin na ƙanwa kuma matar amininsa insha ALLAHU.

    Shawarar Jamal ta masa, dan haka ya taimakawa Anaam daketa hawaye har yanzu ta shirya, shima dai a gurguje yay nasa shirin. Duk yanda yaso tai taku daga bedroom zuwa waje ta kasa, ko bedroom ɗin ta kasa iya ƙarasa fitowa zafi kawai take ambata tana hawaye, gashi duk ta langaɓe masa kamar mara ƙashi a jiki. Dole ya ɗauketa gaba ɗayanta ya fito…..

   ★Ranta fes ta tashi yau kamar yanda ta kwanta sakamakon jin ƙwarin gwiwa daga sirrin su aunty Safarah. Gaba ɗaya cikin yaƙini da imanin maganin da suka batan yayi aiki take. Tana idar da salla cike da karsashi ta shiga kitchen da kanta haɗa breakfast. Hakan ba ƙaramin mamaki ya bama maman Abu ba. Sai dai bata iya cewa komai ba dan ta fahimci uwar ɗakin nata tana a farin ciki, tasan kuma yana da nasaba ne da abinda taga tanayi jiya. Sai taji inama zata fahimceta kuma ta isa ta bata shawara akan abinda take kallo ba komaiba. Taji sanda su aunty Safarah ke tabbatar mata maganin matane suka bata, ita kuma ta aminta da hakan saboda bata da ilimin banbancewa, ta sani Fadwa nada rawar kai da ɗagawa, dan duk wanda ya kwana ya tashi a gidansu yasan ita ɗin boss ce musamman akan ƴan aiki, to amma kuma duk da kasancewarta a haka ɗin bata taɓa tunanin ganinta da wani mugun hali da ya zarta waɗannan ɗin ba, tanaji a ranta kuma da wani zai fahimtar da ita abinda su aunty malika suka bata nada banbanci da maganin mata ƙila bazatai amfani dashi ba duk da bata san zuciyarta ba dai.

   Tana aikin gyaran sashen nata ita kuma tana haɗa breakfast mai rai da lafiya a kuma nutse, dan dama dai shiriritarta da son jiki ke hanata yi ɗin a yanda ya kamata bawai dan bata iya ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ƙamshi ya gauraye ko’ina, cike da nishaɗi ta kammala ta koma bedroom ta gyara jikinta. A yau zata kawo duk wani iskanci da jiji da kan Anaam a gidan nan, dan babban burinta tai gaba ta barta da mijinta salin alin.

   Ƙarfe takwas da wasu ƴan mintuna ta nufi sashensa dan tasan ya tashi zuwa yanzu, shi ba ma’abocin barcin safe baneba ma, amma a yanzu tunda yana gida ba aiki zai fitaba tasan ko yaya zai ɗan kwanta…..

   Fitowar Fadwa yayi dai-dai da fitowarsa ɗauke da Anaam daga sashenta. Babu shiri taja birki ƙirjinta na dukan tara-tara bama uku ba, shi sam baimaganta ba dan hankalinsa gaba ɗaya ya tafine ga kallon Anaam yana murmushi, saboda tsokanarta yake akan raguwace ita tana tuttura masa baki da kauda fuskarta gefe. Anaam ɗin kam sarai ta ganta, duk da halin da take ciki hakan bai hanata ganin wannan wata dama bace, ada taƙi yarda ta riƙesa, a yanzu kam saita saƙalo hannayenta a wuyansa duk biyu tana sake sakin kuka da cusa kanta a ƙirjinsa. Shiko da bai san dalilin yin hakan ba sai ya ɗan manna mata kiss a goshi da sakin siririyar dariya. A hankaki yake taku har zuwa wajen motar tasa, ya dureta ƙasa tare da jinginata da motar. 

    “Ina zuwa”.

Ya faɗa yana barin wajen, batace komai ba sai dai idanunta na satar kallon sashen da Fadwa dake binsu da kallo har yanzu kamar a birkice take. Da sauri Fadwa tai baya alamar bata buƙatar ya ganta, shima da yake ALLAH yasa hankalinsa ba wajen yake ba sai bai lura da ita ba ya wuce yanzu ma. Mintuna da basu fi uku ba ya sake fitowa hannunsa da key ɗin motarsa. Sake wucewa yay abinsa batare da yanzu ɗin ma ya ganta ba dai…

   A gaban idonta ya sake ɗaukar Anaam ya saka a mota, shima ya shiga suka fice gidan. Tai baya kamar zata faɗi maman Abu da itama komai ya faru akan idonta ta riƙota. “Hajiya dan ALLAH ki kwantar da hankalinki”. Maman Abu ta faɗa muryarta cike da damuwa itama. Da taimakonta Fadwa ta koma ciki, ta ɗakko mata ruwa amma sai ta hankaɗar da shi ya zube, wasu zafafan hawaye da sai yanzu suka sami damar fita a idanunsata suka shiga rige-rigen sauka a fuskarta. Maman Abu dai batai fushiba, takai zaune kusa da ƙafafunta a ɗarare ta sake faɗin, “Hajiya dan ALLAH karki ɗaga hankalinki, wannan kaɗanne daga halin maza idan suka ƙara aure. Amma inaga ki bincika kiji mike faruwa tukunna kamar zaifi. Koba komai kin jefa tsuntsu ɗaya da dutse biyu. Na farko dai zaki san mike faruwa, na biyu kuma zaiji kunyarki idan fitar bata da wata babban dalili da farar safiyar nan. Amma idan na shiga hurumin daba nawa ba kiyi haƙuri..”

   Idanu Fadwa ta sake rumtsewa da ƙarfi zuciyarta na wani irin zafi da raɗaɗi, dan tabbas abinda Shareff yayi ya sake zuzuta zafin daya sauka mata lokaci guda, kishi ya rufe idonta ta kasa ji a ranta wata matsalace ta sakasu fita gidan da safen nan bawai lafiya ba…..

   Waya ta ɗauka da sauri ta fara laluben layin aunty Safarah. Bata tsaya ko gaisuwa ba ta sakar mata kuka. 

   “Subahanallahi Fadwa lafiya kuwa?”.

  “Aunty Wlhy maganin beyiba, yanzu fa da safen nan ya fito ɗauke da ita suna farin cikinsu da dariya suka bar gidan nan. Alhalin jiya babu wani kusanci makamancin hakan tattare dasu. Aunty na shiga uku idan hankalinsa ya koma kan yarinyar nan. Jiyafa taimin alwashin indai ya fara kasancewa da ita saina zama ƴar kallo….”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button