BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 58

   “Kinga nutsu ki saurareni Fadwa. A yanzu haka gani tare da Aunty (Gwaggo halima) kuma duk tana jinki, dama nazone zan amsa sako da zamuje wani waje saboda ke”.

   Sunan maman ta fara kira cikin kuka, Gwaggo Halima da tun fara bayanin Fadwa wutar kanta ya ɗauke saboda shi babba duk inda yake babba sunansa, tuni zuciyarta ta hasko mata wani abu ya shiga tsakanin Shareff da Anaam kenan, dukan kokarinsu na hana faruwar hakan bai yuwuba kenan, taja numfashi. “Fadwa kinga nutsu kuka ba naki baneba. Karki damu damun bayanin komai na riga na sani domin ni na aiko su Safarah wajenki dama nace ne karsu faɗa miki. Yanzu ki jira zamu kiraki ina zuwa…”

  Kafin tace wani abu aka yanke wayar, ta zube a bakin gado da sake fashewa da kuka mai cin rai….


   Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso asibitin, yanzu dai taso nuna jarumtar hanashi taɓata amma ina hakan bai yuwu ba. Dan taku biyu kacal ta nema zubewa tamkar ta fasa ihu dan zafi. Dole dai ya ƙaraso ya ɗauketa.

   “Ni dai Yaya ka saukeni zan iya”.

Ta faɗa tana sharce hawayen dake ambaliya akan fuskarta saboda hango Dr Jamal dake nufosu alamar yasan da zuwan nasu. 

  Murmushi yay da kashe mata ido ɗaya “Da wannan tafiyar tonamin asirin ne zaki iya?”. 

   Idanunta ta rumtse kunyar duniya a kanta, dan gani take kowa zai iya sanin miya faru da ita ne. Da taimakon Dr Jamal suka sami ganin Dr Bilkisu a sahun farko. Ganin Anaam taƙi amsa tambaya ko guda ɗaya a gaban Shareff daya tsatstsareta da ido yasa Dr Bilkisu kallonsa da ɗan murmushi. “Alhaji Al-Mustapha ko zaka ɗan bamu wajene dan naga patient ɗin tawa kasancewarka tare damu ya hanata cewa komai”.

    Ido suka sake haɗawa da Anaam. Tai azamar janye nata da tura masa baki. Mikewa yay yana murmushi batare da yace komai ba ya fita. Ko’a bayan fitar tasa ma sai da Dr Bilkisu ta sha fama sannan Anaam ta amsa mata wasu daga cikin tambayoyin nata tana faman sinne kai, a yanda ta fahimci ta kasa zama da ƙyau tai hasashen abinda Anaam ɗin ke faman ɓoyewa. Batace komai ba ta taimaka mata zuwa gadon da suke duba marasa lafiya, ganin tana neman ɗage mata doguwar riga ta riƙe da sauri tana girgiza kanta………..✍
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button