BABU SO 59
Duk yanda mmn Abu ta lallaɓata akan ta koma ciki ta kasa motsawa, dan haka harya dawo gidan tana a wajen zaune ita bamai rai ba ita ba sumammiya ba, har yanzu kuma su Gwaggo halima basu kiratanba. Bai shigo ciki da mota ba, dan haka har ya ƙaraso bata san da shi ba. Yay tsaye yana mata kallon mamaki ganin hawaye share-share akan fuskarta dan ma wasu sun jima da bushewa…
“Baki da lafiya ne?”.
Ya faɗa yana kaiwa tsugunne gabanta da ɗago fuskarta daya riƙo haɓarta da hanunsa na dama. Maimakon amsa sai kawai ta sakar masa sabon kuka. Sosai hankalinsa ya tashi, dan zuciyarsa ta fara ayyana masa ko wanine ya mutu ma.
“Ya salam, wai mike faruwa? Wani ne ya mutu ina magana kin mun shiru?”.
Hanunsa tai ƙoƙarin turewa zata miƙe ya maidata ya zaunar. “Fadwa….!”
ya faɗa aɗan tsawace
“Ni ka ƙyale ni!!”.
Ta faɗa a matuƙar tsawace itama da fisge duka jikinta ta shige ciki a fusace.
Kallo ya bita da shi ransa na sosuwa da mamakinta, shi yarinyar nan takema tsawa wai?. Kallonsa yakai ga Mmn Abu dake tsaye kanta a ƙasa idonsa cike da matuƙar ɓacin rai. “Mi’aka mata?”.
“Nima Alhaji ban saniba, tun ɗazun dai na sameta tana kuka anan lokacin da zaka fita da Hajiya Amarya”.
Ɗan jimm yay na tunani yana idonsa akan Mmn Abu ɗin har yanzu. Komai baice ba yay wucewarsa sashensa yana jan tsaki. Akan kwanikan abinci da aka ajiye ya fara sauke idonsa, kenan idan lissafinsa yayi dai-dai Fadwa taga fitarsa da Anaam shine take wannan haukar. Ƙaramin tsaki yaja da girgiza kansa kawai ya shige bedroom. Bai jimaba ya fito. Sashen Anaam yaje, ya ɗauka mata abinda za’a buƙata ya sake ficewa a gidan batare da yabi takan Fadwan ba.
Tun a hanya ya sayo dukkan maganin, koda ya dawo asibitin har lokacin tana barci, ya ajiye kayan ya nufi office ɗin Dr Jamal. Saida suka fito yin sallar azhar ya ɗan leƙa Anaam, har lokacin barci take, dan haka Dr Jamal yasa wata Nurse shiga ta zauna da ita saboda Shareff yace masa zaije wani waje daga nan tunda yaga ba yanzu zata farka ba….
Barci tasha sosai, sai kusan biyu da rabi ta farka. Jinta take kamar ana mammatsa mata ƙasusuwa, ga ɗinkin da akai matan nayi mata kamar a takure babu dai daɗi. Nurse ɗin nan ta taimaka mata zuwa bayi kamar yanda ta buƙata. Harda kukanta wajen yin fitsari, wani haushin Shareff na ƙara zuwa mata a maƙoshi. A daddafe ta sake fitowa da taimakon Nurse ɗin, tai salla jiri na ɗibarta na yunwa da rashin jin daɗin jiki. Ta idar da sallar tana addu’ar ya shigo da sallama Aysha biye da shi ɗauke da basket, Aunty Mimi a bayansu. Batai niyyar ko kallonsa ba, sai dai jin muryar Aunty Mimi da Aysha ya sakata ɗagowa da sauri………✍
End of book