BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 59

59

………Murmushi Dr Bilkisu tayi, cikin sigar lallashi tace, “Kiyi haƙuri dubawa kawai zanyi, dan idan yazam yaji miki ciwo ne ba’a ɗauki mataki ba nan gaba zaki iya fuskantar wata matsalar da ba’a fata. Gara tun yanzu yana a ɗanyensa a ɗauka mataki kinji ƙanwata. Badan Anaam taso ba ta bar Dr Bilkisu ta duba, dan sosai ta dinga lallaɓata da nuna mata illar rashin dubawar harta amince. 

   “Ya ALLAH”. Dr Bilkisu ta faɗa da sakin rigar Anaam ɗin takai hanunta saman goshi tana murzawa. Sosai ranta ya sosu, sai dai kuma ta fahimci matsalar daga jikin Anaam ɗinne. Amma duk da haka an nuna mata mazantaka da yawa da ƙawazuci.

   A tsorace Anaam dake kallonta tace, “Doctor wajen ya daina aiki ko?”. Murmushin da babu niyya Dr Bilkisu ta saki, ta girgiza kanta da kallonta. “A’a bai daina aiki ba ƙanwata, kawai dai anyi ɓarna ne da alama angon naki tsohon tuzurune halan shiyyasa ya gagara binki a sannu. Gaskiya yayi miki ɓarna da yawa da dole sai anyi ɗinki”.

   “Na shiga uku”.

Anaam ta faɗa tana fashewa da kuka. “A’a kinga kwantar da hankalinki baki shiga uku ba. Mata da yawa sunci karo da matsala fiye da taki ma a dalilin first night, ban san mike damun mazan ba da suke muku irin wannan zuwan haka, ko soyayyace ke ingizasu oho, koda yake suma iyaye akwai laifinsu, zaka kai yarinya buduwa gidan miji amma kaita tsumata da kayan mata. Sune suke saka gushewar hankalin mafi yawan mazan har su aikata mummunar ɓarna ga yarinya, a yanzu haka inada irin cases ɗin nan da yawa ga wata can ma kwana uku kenan da mata ɗinki har huɗu kaɗan ma ya rage ita mijin ya kasheta dan a sume aka kawo mana ita tana bleeding kamar mai haihuwa” (Iyaye wlhy da gaske matsalar nan tana cutar da yaranmu, maganar mai ɗinki da bleeding ɗin nan da nake muku ya faru a gaske ALLAH har kuka naima yarinyar, amma koda aka binciki mijin iya gaskiyarsa ya faɗa cewar ya fita hayyacinsa ta yanda ya gagara jin tausayinta balle tuna ita din virgin ce, koda yarinyar ma akaji ta bakinta daga baya akan ko tasha wani abu ne bata ɓoye ba ta sanar da irin kayan matan da aka dinga ɗirka mata har ji ta dingayi kamar ta jawo auren koma ta bashi kanta kafin a ɗaura. Ya ALLAH, iyaye mata a duba dan ALLAH a gyara, ƴarki budurwa ce bata san komai ba, koda ɗan kayan fruit kika gyarata da su zuma da mazarƙwaila sun wadatar ai, sai maganin sanyi da a kullum bana gajiya da tuna muku shine mafi muhimmanci kafin kikai ƴarki gidan aure ki tabbatar bata tare da imfection yafi maganin matar nan da za’a iya cutar miki da yarinya a dalilinsu. Dan mazan da yawa sukan kasa controling kansu ne harsu fatattaka miki yarinya a banza taje yoyon fitsari ya sameta. Dan waccan yarinyar da nake gaya muku sai da yakai ko fitsari bata iyayi da kanta saida taimakon robon fitsari tsahon wasu wattani. Shin riba akaci ko faɗuwa kenan?????????).

     Kuka sosai Anaam ta dingayi har ba’ajin sautin muryarta a yayin da ake mata ɗinkin, tabbas ita din ragguwace bata wasa ba. Ko yaya abu ya sameta ta dinga raki ke nan balle wannan da ya zame mata makafin ajewa a tarihi dan bata taɓa riskar azaba makamancin hakanba. Shareff yasha tarin ALLAH ya isa da inda tarasu za’ai waje guda buhu-buhu zai ɗiba ya kaima Mommy ajiya saboda tarihi????????.

    Sosai ya dinga kaikawo dan yana iya jiyo kukanta da kiran Abie da Mamie da take famanyi, har da wasu a ALLAH ya saka matan da take ambata da ja masa ALLAH ya isa. Sosai hankalinsa a tashe yake dajin ɗunbin tausayinta da takaicin kansa. Da yanada damar dawo da ciwon jikinsa da yayi ko zai samu sassauci a zucyarsa, dan itaɗin wata abace mai daraja a zuciyarsa da baki ko alƙalami ƙaryarsa zanawa. Ita ke kukan amma tare suke raba raɗaɗin a zuciya. Koda aka kammala Dr Bilkisu tasa aka kaita wani ɗaki danta huta yana shigowa ta fashe da kuka wai bata son ganinsa Dr Bilkisu ta koresa. Duk da haushinsa da Dr Bilkisu keji kasa daurewa tai sai da tai dariya. “Tunda patient ɗina bata bukatar ganinka jeka abunka mun sallamaka Alhaji Al-Mustapha. Dan gaskiya kai mai laifine mai girma a wajenmu ɗin”.

   “Gutun murmushi ya ɗanyi iya laɓɓa sai dai bai fitan ba. Ya jingina da bango hannayensa zube cikin aljihun wandonsa ya zuba mata idanu. Bargo taja ta rufe har fuskarta ita a dole bata buƙatar ganinsa ɗin dai. Dr Bilkisu ta janye daga kallonta tana ƙara sakin ƴar dariya itama. Inaga ka bata dama ta huce sai muyi magana a office”.

   Kansa ya jinjina mata kawai. Ta juya ta fita. Cigaba yay da tsaiwa a wajen har bayan minti biyu da fitarta sannan yabi bayanta, har sannan kuma Anaam bata buɗe fuskar taba ɗin.

    A office ɗin doctor batare data kallesa ba ta miƙa masa takardar data gama rubutu a jiki. “Taji ciwo ne, amma mun mata ɗinki. Na fahimci cewa ƙaramin jiki ALLAH ya bata, amma shekarunta sun kai ga hakan. Sai dai kuma yanayin halittarta tana buƙatar bi a sannu, domin masu irin yanayinta zakaga ko’a wajen haihuwa ana shan fama dasu matuƙa saboda jikinsu bashi da wani ƙwarin gaske, sauƙinta ma ita tanada wannan ƙaramin jikinne, da irin raɓo-raɓo ɗin nan take akwai matsala, hakan na nufin ko anan gaba za’a bita a hankali inba hakaba kullum zata dinga shan ɗinki kenan. A yanzu dai zan riƙeta anan gaskiya har zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ta samu nutsuwa yanda ya kamata saina baka ita da sharuɗɗa masu tsauri. Muna buƙatar waɗan nan drugs ɗin dana rubuta anan.”

    “Uhhim”.

Kawai ya faɗa yana miƙewa. Dr Bilkisu ta bisa da kallon mamaki, irin miskilan mutanen nan na bata tsoro, sai sun tafka tsiya ka rasa ta inda zaka auna yaya ma sukai. Kiji fa ta gama masa bayani akan kuskurensa ya bita da ‘uhhim’ kawai tsabar miskilanci. Bai san ta ɗaga masa ƙafa bane kawai saboda Dr Jamal. Amma da yaga yanda ake ruwan masifa yau, duk da kwarjininsa shima ya taka rawar gani wajen cika mata ido ko fushinta ta gagara nuna masa akan fuskarta.

    Pharmacy ɗin asibitin ya nufa domin sayo magungunan, sai da aka gama haɗawa zai ɗauka waya dan musu transfer yaji babu wayar a jikinsa, kansa ya dafe yana ambaton sunan ALLAH. Dole ya bar musu maganin akan zaije ya dawo. Ɗakin da take ya sake komawa, saboda yana son jin ko tana buƙatar wani abu. Samu yay tana barci a yanda ya suka barta, ya kai hannu ya yaye bargon data lulluɓe har kanta tare da kaiwa tsugunne gaban gadon. Duk da barci take kumburin idonta bai hana ya bayyana ba, ya saki murmushi yatsansa na kaiwa a saman idanun ya shafa, a hankali ya gangaro har saman fuskarta zuwa lips ɗinta. Yatsansa ya shiga zagayawa a kansu, kafin ya sake matsar da fuskarsa gab da tata murya ƙasa-ƙasa ya furta “Tabbas kin cika mai tsadar da tafi tsada tsada autar mata”. Ya ƙare maganar da manna mata lips ɗinta kiss

  Motsawa tai tamkar wadda ta jisa, ya sake sakin murmushi yana cigaba da kallonta. Tsahon minti biyu sannan ya miƙe tsaye, ɗan ranƙwafawa yay a kanta ya tsotsa lips din nata da sumbatar goshinta ya ƙara miƙewa. Kaɗan ya ɗalli lips ɗin da yatsansa. “Bari muga idan bakin tsiwar zai mutu”. Ya faɗa akan lips ɗinsa har yanzu murmushi bai bar fuskarsa ba….

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button