BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 61

WASHE GARI.

           Sai wajen takwas yabar gidan zuwa asibiti batare da yabi takan Fadwa ba, tun da suka baro asibiti jiya suke tafka rigima da ita, dan kuwa ya mata tatas akan abinda taima aunty mimi, ya kuma tabbatar mata inhar ta ƙara sai ya mata abinda bata taɓa zato ko tsammani ba daga garesa.
Gargaɗinsa ya sakata kwana kuka, ta kira gwaggo halima kuma ta hanyar wayar mmn Abu data kira wayar cikin masu aikinsu aka haɗata da maman, zayyane mata komai tayi, suka haɗu sukaita zagin su aunty Mimi wai asiri ne ke cin Shareff ɗin. Amma zata ɗauka mataki ta saurareta.

  Ya iske Anaam ɗin na toilet tare da Dr Bilkisu tanayi sit bath. Yana iya jin rakin da take zubawa daga nan, ya girgiza kansa kawai da kaiwa zaune a bakin gadon yana murmushi. A haka Aysha ta shigo hanunta ɗauke da flask ɗin tea. Gaisheshi tayi, ya amsa yana kallon flask ɗin.
     “Daga ina?”.
“Yaya gidan Dr Bilkisu mukaje amso ruwan zafi anan cikin asibitin”.
  Bai sake cewabkomai ba akan hakan. Itama saita ajiye flask ɗin.
    “Kunyi barci dai babu wata matsala ko?”.
  “Eh Yaya. Ai da yake a magungunan nata kamar akwai masu saka barci harma makara tayi sallar asuba.”
       Bai samu damar bata amsa ba suka fito Anaam na tafiya da ƙyar. Suna haɗa ido ta dalla masa harara dan duk wannan dai bala’in shine yaja mata ai. Shi dai kallonta kawai yake murshi na neman suɓuce masa, tana tafiya kamar wata ƴar kaciya. Doctor ce ta katsesa daga kallon nata. Ya ɗauke kai suka gaisa. Baƴani ta ƙara masa na cewar zatama sallamesu amma sai zuwa anjima kaɗan dai haka akwai abinda zata ɗan jira a kawo mata da zata bama Anaam ɗin.
    A taƙaice ya mata godiya yana maida hankalinsa ga Anaam daketa faman sauke ajiyar zuciya daga kwancen da take ta juya masa baya. Tai musu sallama ta fice tana faɗama Aysha taba Anaam ɗin abinci amma ta fara da tea mai zafi. Kamar jiya dai koda Aysha ta haɗa abincin shine ya karɓa. Cikin bada umarni yace ta tashi zaune. Taso sharesa, sai dai a yanda yay maganar ya tilastata tashi dole bakinta a sama. Yi yay kamar bai ganta ba. Ya miƙa mata shayin ta amsa kamar zata fasa ihu. Sai da ta gama shanye tea ɗin tas sannan ya miƙa mata abincin, amma sai tace ta ƙoshi. Bai saurareta ba ya fara ɗiba yakai bakinta, ta kalesa kamar zatai kuka.
     “Nifa Yaya nace na kos…”.
  Ta kasa ƙarasawa saboda kallon daya wulla mata cikin tsakkiyar ido. Idanunta ta lumshe tsigar jikinta na tashi, dole ta buɗe bakin ya zuba mata. A dai-dai nan Dr Jamal ya shigo. Da alama ma shigowarsa asibintin kenan. Sun gaisa ya tambayi mai jiki, bai jimaba ya fita yanama Shareff dariya da shaƙiyanci da ido. Bai dai kulasaba shi dai.

      Karfe kusan sha ɗaya aka basu sallama. Zuwa lokacin yaje office ɗin Dr Jamal ya dawo. Aysha ta tattare kayansu shi kuma ya kama Anaam ɗin da taso botsare, sai dai ya hana hakan ta hanyar tabbatar mata zai ɗauketa. Dole ta nutsu tana tura masa baki. Yay murmushi kawai da sumbatar wuyanta. Mintsininsa tai ya dafe wajen yana ɓata fuska shima. Sai ta saki dariya da masa gwalo………✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button