BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 61

61_*

……..Aunty mimi ta ɗan jima wajen doctor Bilkisu sannan ta dawo, sai faman murmushi take, a ranta kuwa faɗi take (ƴan banza kukace da bakwa son juna. Yanzu kuma ina ƙiyayyar taje harda ɗinki?). A zahiri kam zama tai tana kallon Anaam daketa faman sinne kai taƙi yarda su haɗa ido sam. “Wai nikam na zama surukarki ne halan Mamana? Tun ɗazu sai wani sissinemin kai kikeyi daga ke har mijin naki wani abu ya faru ne?”.
Dariya Aysha ta sanya. “Ummie surukartace ke mana, ba ɗanki take aure ba”.
Dariya itama Aunty Mimi ta sanya da faɗin, “Bayan haka ma akwai dai wata a ƙasa ma”. Anaam ta ballama Aysha dake ƙara kwashewa da dariya harara. Sai kuma ta koma ta kwanta tare da lulluɓe har kanta tana murmushi.

   ★Da shirin tafiya massallaci daga can ya wuce asibiti ya fito. Har yayi niyyar ficewarsa sai kuma ya shiga wajen Fadwa. Samunta yay tayi alwala. Yanzu kam ya ɗanga sassauci a fuskarta, sai dai ba'a sake masaba yanda aka saba. (Idan ka biye ta matan nan baka da maraba da ball ɗin ƙwallonsu) ya ayyana a ransa. A fili kam sai ya juya kamar zai koma yana faɗi,

      “Zanje masallaci, daga can zan wuce asibiti”.
    Muryarta a dasashe batare data kallesaba tace, “Bara nai sallar sai na jiraka nima zanje na dubata”.
  Yanji daɗi har cikin ransa. Dan haka yace, “Okay”. yana ficewa. Da kallo ta bisa, ta sauke ajiyar zuciya da taune lips ɗinta ta haɗiye abinda ya tokare mata maƙoshi. Batai niyyar zuwa ba, Mamanta ce ta kirata tace taje, kuma ta saki ranta duk wani fishi da takeyi ta dainashi hakan zai bama shirinsu damar tafiya yanda suke so.
        Maimakon yin sallar magrib ya shigo sai da yay isha’i, ya iske ta cikin shiri dan haka basu ɓata lokaci ba suka fito mmn Abu biye da su da abincin da Fadwa ta sakata shiryawa wanda tayine saboda maigidan. Sai dai kuma Gwaggo halima tace mata ta ɗaukesa ta kaima Anaam ɗin, itama kuma sai ta yarda da hakan tunda da wuya yace zaici a yanda yake kan dokin zuciyarnan. Shiru motar babu mai magana har suka fito daga layinsu. Ya harba motar saman babban titi.
Ɗan kallonsa tai ta gefen ido. Har yanzu fuskarsa ciɗin-ciɗin babu alamar fara’a, sai tuƙinsa ma yake tamkar bai san da zamanta a motar ba. Idonta ya ciko da ƙwalla ta maida kanta gefe tana ƙoƙarin haɗiyesu. A wajen masu saida fruits ya tsaya ya sayi laida biyu yasa a baya, ya kuma tsayawa ya sayi gasashen kifi shima ya saka a baya.
    “Sorry na saki jira”.
  Kanta ta girgiza masa.
“Babu komai”.
Bai sake cewa komai ba ya tada motar sukai gaba.
     
         ★Suna kallon film a wayar Aysha suka shigo, Aunty Mimi kuma nakan sallaya tana addu’a dan ta idar da sallar isha’i ne. Sam Anaam bata kawo a ranta ganin Fadwa ba. Sai da Aysha ta ambaci sunata sannan ta ɗago. Kallon juna sukai cikin ido. Kowanne ya janye lokaci guda. Aysha ta sauka a gadon da sauri ganin Shareff na kaiwa zaune kusa da Anaam ɗin yana nunama Fadwa kujera.
     “Kun daiyi salla ko? Da kuka zauna kallon film?”.
     “Eh Yaya munyi”
Cewar Aysha. Oganniyar kam tayi kicin-kicin da fuska sabida wani takaici taji na ganin Fadwa. A tunaninta kawai ya kwashe sirrinta ya faɗama Fadwar ne….
    Murmushi yayi da ɗan leƙa fuskar tata. “Har yanzu fushin ne autar mata?”.
  Cin dauriya da son cusama Fadwa baƙin ciki ta saki ɗan murmushi. Cikin disashiyar muryarta da tura baki tace, “Ni nace ina fushi ne dama?”.
“Uhm-uhm fa, bayan ɗazun har ana jeramin ALLAH ya isa da juyamin baya”.
     Da sauri ta saci kallon Aunty mimi, sai taga sallama ta sake kabbarawa da alama shafa’i da wutiri zatai, ganin idon Fadwa a kansu sai ta sakeyi murmushi da ɗan kallonsa. Sai dai batace komai ba ta janye dan kallonta yake cikin wani yanayi daya saka tsigar jikinta tashi lokaci guda. Shima murmushi yayi idonsa akanta ko ƙyaftawa bayayi kamar ma ya manta Fadwa na tare da su fa a wajen, ga Aysha kuma da aunty Mimi.
     “Kar dai a sani yarda babu komi aje can ana kuka a bayan idona. Dan naga ke kam baki raina abin kuka”.
    Cikin ɗan tura baki tace, “Kuka ai rahama ne”.
“ALLAH?”.
Ya faɗa cikin sigar tambaya da ƙoƙarin ɗago fuskarta.
    Murmushi tai da ture masa hannu tana kauda fuskarta gefe. Yay ƴar dariya kawai da jinjina kansa.
Fadwa daketa ƙoƙarin danne hawayen da suka ciko mata idanu ta ɗan dubi Anaam. “Ya jiki? ALLAH ya ƙara afuwa”.
    Ciki-ciki ta amsa mata, batare data yarda ta kalleta ba. Dai-dai nan Aunty Mimi ta idar da salla, Shareff ya juya yana gaisheta. Amsawa tai da kulawa tare da duban Fadwa data ɗauke kai bata da alamar gaishetan ita. Murmushi kawai aunty Mimi tayi “Fadwa kuna lafiya ko?”.
Yitai kamar bataji ba, Shareff ya kalleta cikin ɓacin rai a ɗan kausashe yace, “Kina cikin hankalinki kuwa? Itace zatama gaisheki?”.
       “Nagafa tana salla ne shiyyasa”. Sai ta juya tana gaisheta. Tsaki yaja mai ƙarfi, yayinda Murmushi ya suɓucema aunty mimi ta girgiza kanta kawai tana amsawa.
  Aysha kanta sai bataji daɗin yanda Fadwa ɗin tayiba. A ganinta koba komai yaci Fadwa ɗin ta danne ta amsawa Aunty Mimi cikin daɗin rai tunda har ta karya ƴancinta ta fara gaisheta, tunda ita ta kasa banbance dai-dai ta gaisheta matsayin babba gareta kuma ƙanwar mahaifiyarta. Sai dai batace komai ba saboda Yayansu. Shiru ɗakin yayi zuciyar Shareff a ɓace. Amma sai ya danne a bisa uzirin suna asibiti, sai dai yaci alwashin taka mata birki dan bazai ɗauka wannan banzan halin ba.
       Fadwan ce ta katse shirun ta hanyar tura musu basket ɗin da ta shigo da shi. “Ga abinci nan ALLAH yasa zaki iya ci, bansan a asibiti kike ba sai yanzu da Soulmate ya faɗa da an miki wanda zai fi dacewa da mara lafiyan ai”.
        Banza Anaam tai mata, sai bayan wasu sakanni tace “Ayya” a taƙaice taja bakinta tai shiru.
    Matuƙa ran Shareff a ɓace yake dan har fuskarsa ta nuna hakan, amma tsarinsa na ƙin yankema mutum hukunci cikin fushi ya sakashi yin shiru. Aysha ma kai kawai ta girgiza. dan ta fahimci inhar a haka Fadwa tace zata rayu a zaman aure lallai zata wahala. Domin fidda kishin mace ƙuru-ƙuru a ƙasar hausa tamkar gogama kanta baƙin fenti ne ga mijin dama kowa, domin al’ummarmu kanyi hukunci da zahiri ne a kowanne al’amari musamman akan kishin gidan malam bahaushe. Aunty mimi kam murmushi kawai tai ta maida hankalinta ga Aysha.
Anaam dai kwanciyarta tai ta juya musu baya ma, a ranta tana ayyana saita koyama fadwa hankali wlhy, dan abinda taima aunty mimi ya matuƙar sosa mata zuciya. Aunty mimi suna hira ita da Aysha shi yana faman latsa waya fuskarsa a murtuke. Sai ya kasance ita kaɗaice shiru, sai kuma hakan ya sosa mata zuciya har ƙwalla na cika mata ido, kiran wayarta da akai ne ya kawo mata sassauci ta miƙe tabar ɗakin. Anaam ta rakata da harara, amma sai gilashin idonta ya sirrantasu, juya kwanciyarta tai itama zuciyarta na tauna da raɗaɗin abubuwa kala-kala, sai dai taji sassauci a ranta a yanayin da Shareff ɗin ya nuna ɓacin ransa ga Fadwa kan abinda taima aunty mimi, tasan kuma bawai ya barta hakanan ba zasuyi mai dalili idan sun bar asibitin.
       Shigowar Dr Jamal ce ta saka fuskar Shareff sassautawa. Ya gaishe da Aunty Mimi da juyawa kan Anaam da tambayarta ya jiki sannan suka gaisa da Fadwa da shigowarta kenan. Aysha ma gaidashi tayi. Jan hanunsa yay suka fita, kusan mintuna goma sha biyar sannan suka dawo. Batare daya zaunaba yacema Fadwa ta tashi su tafi dare nayi.
    Fakar idon aunty Mimi yayi ya ranƙwafa kan Anaam ya sakar mata kiss. Zai ƙara na biyu dakai hanunsa saman ƙirjinta tai saurin buge hanun tana waro idanu waje harda ƴar zaburarta. Tsaye ya miƙe yana dariya, sai ko suka haɗa ido da aunty Mimi. Juyawa yay da sauri ya fice yana cigaba da dariyarsa…..

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button