BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

[7/1, 6:00 PM] My Data sim number: DUBU JIKAR MAI CARBI

        ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

FREE PAGE 1

 Babban gida ne mai ɗauke da ɓangare daban-daban har kusan sashen mutum goma sha biyu. A taƙaice za mu iya cewa gidan gandu ne da ya haɗa Kakanni, 'ya'yaye da jikoki. Garin Ɗangwauro yana ɗaya daga cikin ƙanana ƙauyukan da ke cikin ƙwaryar Kano, Allah ya azurta su da noma, kiwo da kasuwansu. Gidan Malam Muhammadu mai dogon Carbi sanannan gida ne a kaf cikin garin Ɗangwauro. Tun daga titi idan ka tambaya za a kai ka har cikin gidan, sakamakon gida ne gidan yawa don wani lokaci mutane na yi masa laƙabi da gidan 'Ya'ya da yawa.

Gidan Mai dogon Carbi cike yake da mutane sakamakom wayar gari da suka yi da rasuwar rashin wannan Dattijo mai yawan shekaru, ba iya gidan ba hatta garin Ɗangwauro ya girgiza da rashin wannan Dattijon mai dogon zamani. Yaya Babba da Inna Furai sune matan wannan Dattijo da ya rasu mutuwar ba ƙarmin taɓa su ta yi ba.

Bisa ga al’adar Malam bahaushe a ranar da aka yi mutuwa mutane sun fi nuna damuwarsu ta hanyar koke-koke, kukan ma yana taƙaita yawancin bayan ankai mammaci. Hakan ce ta faru a gidan Mai dogon carbi domin an fita da gawarsa a yi mata sallah yara da Manya sai kuka suke yi.

A gefe ɗaya Hali dubu na hango rakuɓe sai muzurai take lokaci-lokaci tana share hawaye, sai dai cikin zuciyarta haushin mutanen gidan take ji saboda ta lura babu wanda yake bi ta kanta don ya rarrasheta, duk kuwa da irin gursheƙen kukan da take yi. Kallonsu ta fara yi tana ayyana irin abin da za ta yi domin ta janyo hankulansu kanta. Tun da ai ita gani take kamar ta fi su jin mutuwar koda suna yawan faɗa da Mai dogon carbi amma kafin ya rasu, ai ita ma Kakanta ne.

Sumi sumi sumi ta tashi da yaƙunannan hijabinta ta bi hanyar soron gidan tana waiwaye, sai da ta je soron ƙarshe daga shi sai fita Hali dubu ta ɗora hannuwa biyu akanta ta dawo cikin gidan da gudu tana cewa, “Wayyo Allah! Wayyo ni na shiga uku na lalace.” Lokaci ɗaya hankulan mutanen gidan ya dawo kanta, da sauri aka yi carko-carko a kanta masu jero tambaya na yi. Zuciyarta ƙal don ko ba komai ita ma za a rarrasheta kamar yanda aka saka su Yaya Babba ana basu haƙuri. A fakaice take satar kallonsu tana sake sharce hawaye amma ta yi biris babu wanda ta tankawa duk irin tambayoyin da mutane suke yi mata. Baba Munkaila ne ya shigo ya hango cincirindon mutane a tsaitsaye da sauri ya ƙarasa wurin, ganin Hali dubu a zaune ya sa ya ja guntun tsaki sannan ya buga mata tsawa, “Ke lafiya kike yi wa mutane ihu?” Kamar sabuwar Marainiya haka ta ɗago shanyayyin idanuwanta ta kalle shi sai kuma ta waiga ta saci kallon ƙofa ta kuma duƙunƙune kanta cikin alamun tsoro da firgici. Kamar haɗin baki dukansu suka kalli bakin ƙofar suna neman ƙarin bayani, babu abin da ta furta musu sai ma kuka da take yi tana nuna musu ƙofar da ɗan yatsanta. Baba Munkaila tsawa ya sake buga mata ya ce, “Me ye a cen ɗin?” Hali dubu ta kuma kallon ƙofar ta rushe da kuka tana cewa, “Baffa ne!” Cikin haɗin baki duka suka ce, “Baffa kuma? Wane Baffan?”

Bata bi ta kansu ba sai kawai ta baje a wurin ta fara wata irin birgima tana cewa, “Wayyo Baffa ne ya tafi ya barni!” Takaici ne ya rufe Baba Munkaila domin ya san za a rina don ya tabbata ganin Dubulliya tana wannan kukan ba banza ba. Cikin faɗa-faɗa ya fara yi mata magana amma ko gezau ba ta motsa ba. Can gefe ya hango wata igiyar dabbobi ai kuwa bai yi wata-wata ba ya fara tafka mata, tana jin shigar bulala ta tashi ta yi cikin gida ta gudu.

Can ɗakin Yaya Babba ta shiga ta haye ƙarshen gado tana kuka, ga haushin Baba Munkaila ya tsinkata a cikin mutane. Tambayar duniya Yaya Babba ta yi amma Dubuliyya kanzil! Bata ce da ita ba. Sai ma ta yi zamanta a nan domin duk duniya babu abin da tafi tsana kamar taron jama’a a gidansu. Domin ba ƙaramin takura take yi ba, dalilinta na haka kuwa ta yanda za ta ji mutane na bata ji ko kuma ta cika rashin ji kamar ƴar aljanu. Tana daga kwance dabara ta faɗo mata ta yanda za ta kore jama’ar gidan ta ruwan sanyi domin ta san yanda danginsu suke sai a kusa arba’in da mutuwar da sauran baƙi tsiraru. Saboda haka Baffa mai dogon Carbi ya saba musu tun yana raye, idan suka zo taro baya barin ƴan uwansa su koma a kwana kusa. Wannan dabara tata ba ƙaramin daɗinta ta ji ba don har sai da ta murmusa saboda farin ciki. Kamar wacce aka tsirawa allura haka ta zabura da sauri ta fice daga ɗakin Yaya Babba, ita kanta Yaya Babba ba ƙaramin daɗi ta ji ba kasancewar duk duniya babu Jikarta da take so kamar ita sakamakon Marainiya ce gaba da baya.

Dubu tana fita ta yi garau da ita kamar ba ita ta sharɓi kuka ba, nan fa mutane suka fara yi mata tsiya, har da masu cewa dama ita zuma ce sai da wuta. Wasu kuma su ce gara da ya yi mata haka ga shi ta ware ta fara harkokinta. Shiru ta yi babu wacce ta tankawa sai dai duk wacce ta yi magana tana auna maganar tata a mizani domin ta san irin hukuncin da za ta yi mata.

Tun da Magriba ta doso Dubulliya ta fara haɗa kayan aikinta a fakaice cikin hikima da basira, ba tare da wani ya fahimci halin da take ciki ba. Sakamakon babban gida ne kowa da wurin da yake nema ya kwanta saboda ko ina a wadace yake hakan ne ya sa Yaya Babba bata damu ba da Hali dubu ta ce za ta sashen Baba Munkaila ta kwana a cen.

DA DADDARE

Da daddare gidan ya yi tsit ban da kukan tsintsaye da ƙananan dabbobi babu abin da yake tashi, sai munsharin  bacci da yake tashi daga ɗakunan daban-daban. Dubuliyya tana daga sashen Baba Rufa'i cikin ɗaya daga cikin ɗakunan ƴaƴan gidan. Sai da ta ci baccinta ta more sannan ta farka cikin talatainin dare ta ji gidan tsit kowa ya yi bacci sannan ta saci jiki ta zaro kayan marigayi Baffa ta saka rigarsa da babbar riga har da hula ta naɗa rawaninsa ta ɗauki zabgegen carbinsa ta maƙala ta fito, hasken farin wata ne ya haska mata hanyar da za ta rinƙa bi har fice daga sashen gabaɗaya. Can wurin da ya zamewa Marigayi Baffa mai carbi wurin alwala can ta je ta tsugunna, daga nesa idan ka hango Dubu a tsugunne sai ka rantse da Allah Baffa ne, sai da ta waiga hagu da dama sannan ta taƙarƙare ta fara zabgo kaki irin yanda Baffa yake yi, Baba Sule da ke kwance cikin baccinsa ya fara jin alamar kaki tamkar yanda mahaifinsu yake yi duk asuba. Fakare ya yi yana zare idanu, yana cikin wannan yanayin ya sake jin an yi kaki har da irin tarin tsofaffin nan da Baffa yake yi. Janyo wayarsa ya yi yana dubawa ya ga ƙarfe biyun dare, nan take ya hau murza idanu yana sake kasa kunne. Dubu kamar ta san ana sauraronta ta kausashe murya sai ka rantse da Allah Baffa ne yake magana ta fara cewa, "Tabbas rayuwar barzahu daɗi gare ta." Baba Sule ya waro idanu wace cikinsa na karta masa, don ya tabbata hatta dabbobin gidan da suna magana za su ce sun shaida maganar Baffa ce cikin daren nan.

Dubu na tsugunne ta ji alamun tahowa wata zuciyar ta ce mata ta tashi ta ɓuya, wata kuma ta ce ta zauna ta ci gaba da abin da take yi. Tarin Inna Furai ta ji ta saci kallonta ta hangota da ƴar buta a riƙe za ta je banɗaki. Dubu wani kakin ta sake yi tana daga tsugunne, hasken farin wata ne ya hasko mata mutum durƙushe da fararen kaya da rawani tamkar marigayin mijinsu. Gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa ta fara motsa baki cikin addu’a don a zatonta mugun gamo ta yi.

Ɗauke kai ta yi don ma kar ta ci gaba da kallon wurin da Dubu take ta ci gaba da tsoratata, sai da ta kusa da wurin da Dubu take ta ji muryar marigayin mijinsu raɗau a kunnenta yana cewa, “Wato ita dai rayuwar barzahu daɗi gare ta. Babban daɗin idan ka kawo ziyara tsohuwar rayuwarka sai kuma ka tafi da matarka.” Inna Furai na jin haka ta dafe ƙirji tana ja da baya jikinta har tsuma yake ta ce, “Yau na haɗu da zazzagar rayuwa ni Furaira. Allah na roƙeka karka jarrabe ni ta wannan fannin.” Dubu na jin haka ta miƙe tsaye tana gyara zaman babbar rigar jikinta ta sake kausashe murya ta ce, “Wuni ɗaya har na yi abokai miliyan ɗaya da ɗari biyar a cikin Fatalen har da masu tashi sama. Ƴan sama jannati ku zo ga wani naman mun samu, kuma daga yau mun fara ɗauka kenan a gidan nan. Duk wanda ya wayi gari ya ga likkafani a jikin kayansa shi za mu yi wa ɗaukan amarya.” Inna Furai tuni fitsarin da take riƙewa ya samu sukunin tsiyayowa, sakin butar hannunta ta yi jikinta na tsuma donma bongon da ke bayanta ya tokareta.

Dariya ce ta so ƙwacewa Dubu amma ta maze ta ce, “Ƴan uwana ƴan sama Jannati! Ku zo na fara samo muku ƴar uwa.” Inna Furai ta saki salati tana cewa, “Yau na haɗu da zazzagar rayuwa shi kenan tawa ta zo ƙarshe.” Dubu sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta fara takowa gaban Inna Fuarai ta ce, “Idan kina son fansar kanki sai kin sake shayar da ƴaƴanki tamkar yanda kika shayar da su suna jarirai, tun daga kan Larai (Ita ce babbar Ƴar Inna Furai) har zuwa kan Sabi’u (Shi ne autanta) idan kika kuskurewa haka tabbaci haƙiƙa sai mun zo ido biyu mun tafi da ke babu wanda ya isa ya hana.”

Baba Sule tuni cikinsa ya ɗuri ruwa yana son fita domin ceton Matar Mahaifinsa tsoro ya cika masa ciki, bai gama tsinkewa da lamarin ba da ya ji an fara kiran yan sama jannati. Dubu don ta ƙara razana Inna Furai ta sake dakushe murya ta ce, "Ki isarwa da mutanen gidan nan saƙona muddin suka ci gaba da kwanaki sai na yi musu ɗauki ɗaiɗai. Shi kuma na ɗaki da yake laɓe yana sauraronmu, shi kuma ɗauke shi za mu yi gabaɗaya." Dubu na cikin magana sai gani ta yi Inna Furai ta zube ƙasa. Gabanta ne ya faɗi ta ji fargabar kar tsohuwar mutane ta mutu a hannunta. Da sauri dubu ta waiga sai kuma ta kurma ihu tana maƙe murya ta zunduma ihu, sannan ta zuba a guje ta yi cikin gida. Ta nufi ma'ajiyar kayan Baffa ta lallaɓa ta shige ta kwanta.

Ihun da Dubu ta yi ba ƙaramin razana Baba Sule ya yi ba da jim kalaman da da aka ce za a ɗauke shi matuƙar ya saki hannun matarsa. Yana daga gefen gado da sauri ya matsa ya kama hannuwan matarsa ya riƙe ƙam, don kar a neme shi a rasa. Cikin bacci Sahura ta fara masifa da yake Allah ya yi ta masifaffiyar macece. Tana jin ya riƙo mata hannu ta ce, “Don Allah sakarni Uban ƴan naniƙa.” Da yake bacci ya hau kanta bata kuma tanka masa komai ba.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button