BABU SO 65

sami haɗine na musamman daga hajiyar sudan,
ga kuma *_YERWA INCENSE AND MORE +234 809
521 5215 da miss xoxo tayo mata haɗi da sai ƴar
gata ke samunsa
!
_*. Hakama na kanti duk masu
tsadane da ƙamshi na musamman da aka zuba a
lefe. Ƙanan kayan nata taso sakawa, sai dai Ayshata hanata hakan, acewarta kayanmu na gida sunfi
mata ƙyau. Dole badan taso ba ta haƙura ta shirya
cikin skirt da riga na lass daya zauna mata a jiki
tamkar ka saceta ka gudu. Aysha tai mata ɗauri na
zamani daya saka ita kanta kasa rufe baki sai
faman kallon kanta takeyi a mirror da ƙyalla
hotuna da wayarta…..
A gajiye ya iso gidan bayan idar da sallar isha’i. Ya
fiddo ledojin daya shigo da su na fruits kashi biyu.
Sashen Fadwa ya nufa, ya sameta zaune a falo
ƙafa ɗaya kan ɗaya tanata cika da batsewa. Kallo
ɗaya yay mata ya ɗauke kansa dan ko sallamarsa
bata amsa ba. Ledar ya ajiye batare daya ce ko a
ba yay ficewarsa yana ƙwafa. Dan a yanda ta masa
ya bashi tabbacin tana kan sani taƙi ɗauka masa
wayarsa. Sashen Anaam ya nufa da ɗayar ledar
yanata faman furzar da hucin ɓacin rai……
✍