BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 69

Chapter 69 69
…………“Soulmate! Please ka s……”

Da sauri ya ɗaga mata hannu, da karkaɗa mata yatsarsa manuniya lips ɗinsa na rawa alamar gargaɗi. Sai dai ya kasa furta komai saboda takaici.
Dole ta dakata jikinta na wani irin tsumar
tashin hankali, hawaye rige-rigen sakko mata
sukeyi.
Har zai shige ya sake juyowa “Ku kuma na
baku minti ɗaya tak, ku kwashi tarkacenku ku ficemin anan kafin na fara ɓallaku ƴan iska!!”.
Ai har turereniya ake na fita tsakanin Amaal da Siyyah, dai-dai nan Bibah ta fito daga bedroom ɗinsa fuskarta a lulluɓe yanda bai ganta da ƙyau ba. Da gudu itama ta fice. Kansa dake sara masa ya dafe da sauri, jin jiri na neman kwasarsa ya dafe bango da sauri yana ambaton sunan ALLAH, da ƙyar ya iya ƙarasa kai kansa cikin ɗakin ya zube a kujera yanajin raɗaɗi da ƙunar zuciya…..
Fitowar su Amal da gudu daga sashen
Share! ɗin ya saka Anaam da Aysha kallon
juna baki buɗe, Aysha ta zunguri Anaam
“Blood jeki kiga mike faruwa? Naga oganiyar
tasu ita bata fito ba”.
“A’a blood babu buƙatar haka, wannan
tsakaninta da mijinta ne ai. Dama su nafi buƙatar yaci ubansu, amma ita matsalartace ita da shi”.

“ALLAH k banza ce, wlhy idan kece hakan ta
faru a kanki ba ganowaba har dariyama sai
tayi zamanyi”.
Dariya Anaam ta saki da kaima Aysha duka.
“Kefa wlhy muguwa ce”.
“Babu wani mugunta, dan ALLAH kije”. “Okay ina zuwa”.
Ta faɗa da nufar sashen maigidan. Hango Anaam yasa da sauri Fadwa dake ƙoƙarin fitowa komawa ciki, bedroom ɗinsa ta nufa da ƴar sassarfa. Zuwa yanzu ya miƙe yana cire kayan jikinsa, shigowarta baisa ya juyo ya kalleta ba, hakan ya ƙara sanyaya jikinta, amma sai ta danne ta ƙarasa gabansa. Tasanshi mai saurin karayane da ganin hawaye, dan haka ta fara matsosu. “Soulmate dan ALLAH ka saurareni na maka bayani. Wlhy ba…..”
“Get out of my room!! Idan ba hakaba duk
abinda nai miki ke kika saya stupid!!”. ya
dakatar da ita a matuƙar tsawace. “Please Soulmate n…”
Saukar lafiyayyen mari a saman fuskarta ya hanata ƙarasawa. .
Cak Anaam dake ƙoƙarin shigowa ta tsaya, ba ƙaramin harbawa ƙirjinta yay da jin ƙarar marin ba. Wani irin ihun kuka mai ƙarfi da Fadwa ta saki, ya sata toshe kunenta, da sauri ta juya ta fice zuciyarta na bugawa da sauri-

sauri. Shiko baiko nuna yasan Fadwa tanai ba ya shige bathroom abinsa. Hankali tashe Fadwa ta fita zuwa sashenta dafe da fuskarta datai jazur abinka da fara. Mamanta ta fara kira tana kuka, sai dai ba’a ɗaga wayarba, sai kawai ta koma kiran Mommy.
Mommy dake zaune ta kalla wayar taja tsaki, haka kawai takeji a ranta ƙofari Fadwa ta kawo mata. Kamar karta ɗauka sai kuma dai ta ɗaga takai kunne batare da tayi magana ba. Maimakin sallama da kuka ta fara cin karo, Fadwa dake kiran ta shiga uku ta shiga zayyanoma Mommy cewar Share! ya mareta, dan kawai ƙawayenta sunzo Anaam ta tunzuroshi. Dama kwana biyun nan babu abinda yake mata sai wulaƙanci akan Anaam
ɗin…. “Mari!!?”.
Mommy ta faɗa a razane.
Kuka Fadwa ta sake mashe mata da shi,
hakan yasa Mommy yanke wayar da sauri.
Aysha ta kira, cikin sa’a kuwa wayar na’a
hanunta ta ɗaga.
“K faɗamin, mike faruwa Yayanku ya mari
matarsa? Akan ƴar iskar yarinyarnan ne ko?”. Aysha da dama yanzu Anaam ke faɗa mata
cikin tashin hakanli ta taɓe baki. “Wlhy Mommy babu ruwan Anaam. Ƙawayenta ta kawo suna masa wai gyaren sashensa shine

ya shigo ya samesu, harda su Shamsiyya”. “Shine dan bata da kunya ta kirani tana
kawomin ƙararsa, to lallai ya kamata a
wannan gaɓar na takama yarinyarnan birki
dan na kula neman maidani ƴar isaka takeyi.” Aysha tace, “To Mommy bakece ke biye
mataba da su Gwaggo. Kamarma itace kika haifa bashi Yayan ba. Ita Gwaggo Haliman ma ba tanayin komai bane dan ɗiyarta, ki duba akan auren Anaam yanda kika biye mata kuka hau kansa kukaita zagi gashi kinaji kina gani Abba ya hanashi zuwa ki gansa ma amma ita kullum tana waya da ƴarta. Kuma wlhy yanzu kusan kullum su Aunty Malika suna gidan nan kawo mata magani anata zubama Yaya a
abinci….”
“Na shiga uku, magani kuma Aysha?”.
“Wlhy Mommy da gaske nakeyi, to duk
kusancinki dasu Aunty Malika matsayinsu na
ƴan uwanki dasu ake haɗa kan cutar da Yaya,
jiya bakiga abubuwan da suka kawo mata ba
harda zoben mallaka wai bazai sake kallon
wata mace ba a duniya sai ita sai abinda tace
masa ko ke albarka, na rasa yaushe suka
ɗinke da Gwaggo Halima haka har suke abu
batare da ke kin sani ba keda Gwaggo”. “Na shiga uku, ni halima zataci amana ta
haɗa kai dasu Malika a sabautamun yaro

saboda ƴarta tayi farin ciki?….”
Fitt Anaam ta ƙwace wayar daga hanun
Aysha ta kashe. “Blood kinada hankali kuwa?
Ya zaki faɗama Mommy irin wannan
maganar?”.
“Ya bazan faɗa mataba Anaam. Kin san ko
suwaye su aunty Safarah? Wlhy rashin faɗar shine mafi munin kuskure dan hatta ke da kanki sai sun sabauta rayuwarki, ɗan sauran zuminci kuma da muke tattali su ɓarar mana da shi. Ita kanta Fadwa ɗin taimakonta nayi, dan wata ƙungiya garesu ƴan baza’a zauna da kishiya ba, inma an zauna da ita saita koma tamkar babu ita a wajen miji, kina tunanin a hankali bajan ra’ayinta zasu cigaba dayi ba harta koma cikinsu. Koba komai ita ɗin jininmu ce, yana da ƙyau muyi duk yanda ya dace domin ta dawo hayyacinta. Yaya baya son yanke hukunci cikin fushi, amma tunda kikaga yau yakai da marinta to idan takaisa maƙura komai zai iya lalacewa”.
(Aysha kenan, dan ma bakisan akan sani ta zubar da ciki ba akan makircin kakarku) Anaam ta faɗa a zuciya, a fili kam saita kai zaune tana mai dafe kanta…..
A ɓangaren Fadwa kam Mommy na yanke waya kiran Gwaggo Halima na shigo mata.

Sabon kuka ta ɓarke da shi tana zayyana mata
abinda ya faru, harda kiran Mommy datai
amma ta yanke mata waya…
“Kan ubancan, mi Nafi ke nufi Share! ya
mareki ya mari banza?. A to lallai idan tace wannan layin zamubi ni da ita bazatai mana ƙyau ba. Ai dama su Malika sun tabbatar min abinda yafi hakama zai iya faruwa saboda Nafi maciji ce da fuskar tana. Aiko zan tabbatar mata Share! bai mareki a banzaba dan wlhy saina rama miki”. Ta yanke wayar.
★Sai da Gwaggo ta gama sauraren Mommy data isa sashenta a rikice tsaf sannan ta saki murmushi irin nasu na tso!in makirai. Domin kuwa anzo gaɓar da ta jima tana jira kenan. Kallon Mommy tai da dafa kafaɗarta. “Nafisa Halima zata iya fiye da haka domin wannan ƴar tata. Jikina ya fara sanyi da al’amarinta tun lokacin zubewar cikin Fadwa. Karki manta itace ta fara kawo shawarar a sami malamin dazai aiki akan Mustapha da yarinyarnan ta wajen Usman. Abinda yasa naƙi yarda a lokacin na tabbatar idan muka biye mata wataran zata haɗo wani abin a bama Share! yaci a zuwan dan ana son rabashi da Zuwaira ne. Ki tuna Halima ƙudace, domin samun biyan bukatarta rai ba’a bakin komai yake ba.

Tunda kuma ta haɗa kai dasu Malika to komai zai iya faruwa da Mustapha ciki harda rabashi da ke kanki uwarsa, dan kuwa ke shaidace, nice na haɗa auren Halima da Sadiqu, amma gashi nan babu mai cin dukiyarsa daga ita sai ƴaƴanta sai wanda ta zaɓa a dangi. Gasu Muhammadu nan ƴan uwanta tasan yanda zata samesu gefe ta kalallame ta dawo wajenmu tana nuna mana tana tare damu. Kin dai san duk son da Halima zatamana bai kai ya na ƴan uwanta ba tunda ba haihuwarsu nayi ba. Kuma kodan wannan dukiyar dake zagaye da Mustapha ai Halima bataso zaunawa ba tunda tasan yanda ta mallake Sadiqu dolene itama ƴarta ta mallaki Mustapha yanda koke kanki bai isa yaji maganarki ba, danni tawa mai sauƙice kwana nawa ya rage ALLAH na tuba”.
Kalaman Gwaggo ba karamin hautsuna zuciyar Mommy sukai ba. Gaba ɗaya tama rasa ina zata kama ta riƙe a wannan gaɓar. Shigowar kiran Gwaggo Halima ya saka tunaninta katsewa. Ta dubi Gwaggo, “Itace fa take kirana”.
“Ɗaga muji mizata faɗa, nasan dai ƴar tata ta kirata itama ai”.
Dagawa Mommy tayi, ta saka hansfree yanda itama Gwaggo zata iya ji. Daga can Gwaggo

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button