EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL-HABEEB HAUSA NOVEL

EL–HABEEB????

©️Oum Hanan

HASKE WRITER’S ASSOCIATION????
(Home of expert & perfect writer’s)

Bismillahir Rahmanir Raheem.

Da sunan ALLAH mai rahma mai jin k’ai tsira da amincin ALLAH su k’ara tabbata ga shugaban mu ANNABI MUHAMMAD sallallahu alaihi wa alihi wasallam.
Yadda nafara wannan book din lafiya ALLAH ya bani ikon gamawa lafiya.
Duk wanda yaci karo da wani gyara ko kuskure a cikin book din nan ya nemeni ta wannan number 09139964697 k’ofa a bud’e take nagode.

Writer of
DANA SANI
SURAYYAH
NIDA YAH SAYYADINMU
HAD’IN ALLAH
D’AN BASAJA
KAUTHAR
DR SAIF
KALLON KITSE
WATA SOYAYYAH

No 1.

Shimfid’a.

    Kwanciyar shi ya k'ara gyarawa a faffad'an gadon nashi wanda yaji tausasan shimfid'u na alfarma a karo na ba adadi yana k'ara k'ank'ame pillown dake rungume a k'irjinshi cikeda shauk'in samun nasarar dayayi a yau d'in nan zata bud'e masa fuskarta yagani, har wani tsuma yake yana sakin lallausar murmushi akan kyakkyawar fuskarshi tareda k'ara ware manyan manyan idanunshi dan yaji dad'in ganin fuskar tata saidai kash kafin takai ga bud'ewar kamar wanda aka mintsina yayi saurin tashi daga nannauyan barcin dayake zumbur ya tashi zaune yana wuwwurga idanunshi gefe da gefenshi dako ina na d'akin tamkar wanda yake neman wani abu. Kanshi ya dafe da duka hannaye biyun cikeda b'acin rai tareda rufe idanunshi gam yana sauke numfashi wannan masifa dame tai kama? ace sama da shekara biyar yana wannan mafarkin daya rasa ta inama zai fassara shi kullum ta ALLAH saidai idan bai kwanta ya rufe Ido da sunan yin barci ba  ya zamar masa kamar k'aidah ne idan baiyiba bayajin dad'i abin ya zamar masa bala'i ya rasa ta inda zai b'ullowa al'amarin shin wannan yarinyar dake zuwa masa wacece ita? meye alak'arta dashi datake addabar rayuwarshi haka? a ina take? a ina zai ganta? matacciya ce ko rayyaya? meyasa take zuwa masa cikin barcinshi ta hanashi sukuni? tarin tambayoyin da har yagaji dayiwa kanshi su batare da har yanzu yasamu amsarsu ba to waye ma zai amsa masa su? bayan ba wanda yasan yanayin mafarkin, sosai yake k'ara hango kyawawan idanun yarinyar wanda su kadaine suka bayyana a fuskarta sai tudun dogon hancinta da shima ya kasa b'oyuwa ta cikin bak'in mayafin data rufe fuskar tata dashi. Wasu irin idanuwa ne farare k'al masu mugun kyau da shek'i ga wani k'yalli da cikin k'wayar idanun nata keyi kamar wadda hawaye suka fara tarar mata a ido, dad'in dad'awa kuma yanayin shape d'in idanun nata da bai tab'a ganin makamantan su ba saboda yadda ubangiji ya tsara mata su.

A hankali ya bud’e idanunshi da launinsu ya d’an fara canzawa kad’an cikeda damuwa ya sauka daga kan gadon ya nufi wata k’ofa wadda nake kyautata zaton bathroom ne dama boxer ne kawai a jikinshi hakan yasa kai tsaye ya wuce ciki da alamu wanka zaiyi.
Mintuna k’alilan ya fito daga bathroom d’in ya d’aure k’ugunshi da babban towel sai k’arami dake saman kanshi wanda yake goge sumar kanshi zuwa fuskarshi da cikin kunnuwan shi, wajen k’aton mirror dake cikin bedroom d’in ya nufa wanda yake shak’e taf da manya manyan turaruka masu masifar k’amshi da mayuka masu matuk’ar tsada sama sama ya shafa lotion ya taje lallausar sumar kanshi da zagayayyen gemunshi ya shafa musu mai sannan ya nufi wata k’atuwar clothed ta jikin bango wadda ta kusan mamaye duka bangon ya bud’e kayane gasu nan iya ganin mutum shaddoji ne voil, yadika, suits da sauran k’ananun kaya na kamfanunuwa kala kala da sukayi fice a duniya, jeans ya d’auko dark blue da riga body hook mara nauyi light blue ya shirya cikinsu sosai kayan sukayi mugun amsarshi wajen takalma yaje wanda suma gasu nan lodi lodi tamkar shagon siyar dasu farin boot ya d’auka ya zauna gefen tamfatsetsen gadon ya saka yaje wajen ajiyar agoguna ya d’auki wani bak’i k’irar kamfanin Gucci ya d’aura, wajen mirror yakoma ya feshe jikinshi da sanyayan turaruka masu matuk’ar k’amshi da sanyaya zuciya daga nan ya fice daga bedroom d’in bayan ya d’auki wayoyinshi.
Kai tsaye cikin gidan ya nufa dan yasan Ummi nacan na jiranshi musamman yau daya d’anyi late ba kamar lokacin daya saba shiga gidan ba da safe.
Da sallama ya shiga makeken falon wanda yaji kayan k’awa masu tsada tako ina sai k’yalli da walwali yake ga k’amshin turarukan wuta had’i da air freshener spray da aka k’ara dashi. Cikakkiyar dattijuwa mai cikar kamala na hango kan d’aya daga cikin kujerun falon tasha adonta cikin wani dakakken lace blue black da torch d’in pink na fulawoyi wuyanta da kunnenta zuwa hannayenta sunsha gwala gwalai sai faman walwali suke, kallo d’aya zakayi mata kaga tsantsar kamannin su da wannan saurayin daya shigo babu ta inda ya barota daga zaunen datake zaka iya ganin tsayin datake dashi kamar yadda shima yake dogo sosai har d’an rank’wafawa yayi daga sama.
Tun shigowarshi falon fuskar matar ta washe da fara’a shima dolenshi ya d’an saki fuskar sakamakon da datake a d’inke ya had’e gabas da yamma, wajenta ya k’arasa ya tsuguna har k’asa yafara gaisheta cikin sakin fuska ta amsa masa tana shafa kanshi sai yaji duk tarin damuwar dayake ciki game da irin mafarkan dayake ta fara raguwa a hankali yace
“Ummi zan fita ayi mana addu’a”.
“Breakfast d’in fa?”. tace tana kallonshi tana k’ara nazarin yaron nata kamar yanada damuwa.
Fuska kawai ya d’an yatsina yana girgiza kai yace
“Banajin zan iya cin komai yanzu Ummi kawai zan fita zansamu abinda zanci acan”.
Sosai ta b’ata rai tace
“Ban yardaba sam, halinka ne ban saniba? kokuwa yau ka fara fad’ar haka kuma har kaje ka dawo baka sawa cikinka komai ba? meyasa kake son yin wasa da cikinka ne mai babban suna?”. Shagwab’e mata fuska yayi yana shirin yin magana ta dakatar dashi ta tashi tsaye tareda rik’o hannunshi batare datayi magana ba ta bayan kujerar datake sukabi suka nufi dinning area shidai yana biye da ita har suka k’arasa k’aton dinning table d’in daya gaji da had’uwa wanda aka cikashi da warmer’s kala kala masu muguwar tsada da plates da cups duk masu kyau da sauran kayayyakin da ake ajiyewa a dinning d’aya daga cikin kujerun dinning d’in taja masa ya zauna da kanta tayi saving d’inshi ta tura masa plate d’in gabanshi da mug da aka had’a tea mai kauri wanda yaji kayan k’amshi da na’a na’a da sauran had’in da larabawa sukeyiwa shayi sai tashin k’amshi yake, fuska ya shasshake yana kallon Ummi ganin babu alamun wasa saman fuskarta sam yasa baima fara yin magana ba ya maida kallonshi kan abinda ke gabanshi dan dole zaici abincin nan jin cikinshi yake duk a wani cunkushe ba dad’i bai sha’awar sa masa komai sosai mafarkin nan yafara tsaya masa cikin ranshi yarasa kuma ta yadda zai b’ullowa al’amarin gashi bayaso kowa yasani. Kujera Ummi taja itama ta zauna kusa dashi tana fad’in
“Saikace wani k’aramin yaro kullum sai anyi fama dakai wajen cin abinci kafi kowa sanin yadda kake matuk’ar shan wahala idan ulcer d’inka ta tashi amma bazaka dinga kiyayewa ba”.
“I’m sorry Ummi zanci fa”. yayi maganar yana b’ata rai kamar mai shirin sakin kuka shifa hidimarshi ma tafi k’arfin shi dan haka yake ganin tsayawa ma cin abincin kamar b’ata lokaci ne shiyasa saiya kusan yini da yunwa a cikinshi sai coffee da ako yaushe yake d’irkawa cikinshi.
Kan dole yafara tura abincin ganin yadda Ummi ta kasa ta tsare ba alamar ma zata bar wajen bare yayi sharp sharp ya tashi, bai wani ci dayawa ba ya ture mug da plate d’in daga gabanshi ya yagi tissue ya mik’e tsaye yana goge bakinshi da hannu d’aya d’ayan kuma yana k’ok’arin d’aukar wayoyinshi dake zube kan table d’in.
“Oyaa koma ka zauna”. cewar Ummi tana kallonshi.
Sosai ya marairaice mata ya wani langab’e kai yace
“Please Umminah I’m full wllhy ALLAH bansan ina zansa sauran ba kinji”. ya k’are maganar yana d’an tura baki gaba.
Kamar zatayi magana kuma saita fasa ta girgiza kai kawai tare da fad’in
“To ai shikenan ALLAH ya kiyaye yabada sa’a”. Murmushi yayi kad’an wanda ba lallai ma mutum ya fahimci murmushin yayi ba saboda yadda suka tsaya iya labb’anshi kawai cikeda jin dad’in addu’ar yace
“Amin Amin Ummi thank you so much”. ya k’arasa maganar yana sakar mata kiss a gefen kuncinta ya nufi k’ofar fita daga falon da kallo ta bishi har ya fice daga falon cikin zuciyarta tana k’ara bin yaron nata da kyawawan addu’oe.

Tun fitowarshi harabar gidan bodyguard d’inshi suka fara d’iban gaisuwa hannu kawai ya d’aga musu ya shige dank’areriyar motarshi wadda dama already an riga an bud’e masa tun kafin ya k’araso.
D’aya daga cikin motocin ne tafara fita bayan an bud’e k’aton gate d’in gidan sai wadda yake ciki ta take mata baya saikuma wata guda d’aya data biyo bayan wadda yake ciki suka shilla kan titin unguwar wanda yake kamar an shareshi saboda rashin mutane da motoci. Shi kad’aine a bayan motar ya lafe a bayan sit d’in idanunshi a lumshe ya lula can duniyar tunani kan irin mafarkin dayake tunani yake ya fad’awa Ummi ko Mujaheed babban amininshi kokuwa dai yayi shiru da bakinshi abin yana matuk’ar cimasa tuwo a k’warya yanaso ya samu mafita to ta ina mafitar zatazo masa ma? bai saniba yana rok’on ALLAH dai ya yaye masa dukkan wani duhu daya baibayeshi.
H. I .A GASHUA ENTERPRISES LIMITED Sunan dana gani kenan manne daga gaban companyn bayan shigarsu wanda yadda aka rubuta sunan ma kad’ai abin kallo ne da yadda aka tsarashi.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38Next page

Leave a Reply

Back to top button