BABU SO 69

Halima dake a wuya muryarta a shaƙe ta fara
magana batare da ko gaisuwa ba. “Yanzu
Fadwa ke kirana Share! ya mareta, tace kuma
ta kiraki ta sanar miki amma bakice komaiba
kin yanke waya. Kome hakan ke nufi kenan?”. A harzuke Mommy ta maida mata murtani.
“Abinda duk zuciyarki ta baki Halima. Nifa
bazan ɓoye miki ba na gaji da yawan kai ƙarar
Fadwa. Ita kullum bazata iya haƙuri da miji ba
saita kawo kararsa. Ko haka taga wani a
cikinmu nayi? Sannan kin tambayetama mita
masan ya mareta? Taya zata kai masa ƙawaye
ɗakinsa na sirri su gyara saboda rashin sanin
ciwon kai. Ni yamun dai-dai, kinga gobe idan
ta sake saiya mata dukan tsiyama ba mari ba.
Sannan Halima ki sani, dukkan ƙulle-ƙullen
da kukeyi ke da su Malika naji kuma na
sani……”
“To idan kinji kin sani ɗin sai yaya Nafi? Kin
goya bayan ɗanki akan marin da yay yarinyata ma, to wlhy ki sani da hannuna zan rama mata marin da yay mata, idan shi ɗin mahaukacine zan maidosa hankalinsa kuwa. Kuma karki manta duk wani ƙulli da tuggunki a tafin hanunna suke, ko dama wanzami baya son jarfa ne, yanda kika mallakemin ɗan uwa kike tunanin ke naki ɗan bazai mallaku ba. Hhhhh Nafi idan kikace wannan layin zamubi
ni da ke akan Share! da Fadwa wlhy muje
zuwa ɗan halak ka fasa….”
“Halima idan kin isa ke tujararriyace mu
zuba ɗin dan ALLAH, ni dake za’aga mai iko akan wannan auren. Shiyyasa dama ni tun farko ban so wannan haɗin ba kika katsatstsare ke da Gwaggo sai anyisa. Bayan nasa ƴarki bata da tarbiyya ko misƙala zarratin..”
“Matsalarkuce kuma wannan, ni nagama dake kuma muje zuwa ɗan halak ka fasa”. Gwaggo Halima ta faɗa da yanke wayar. Wani jijjiga Mommy tai zata maka wayar da ƙasa Gwaggo ta riƙeta.
“Kefa daɗina dake baki da hankali idan ranki ya ɓaci, ki nutsu, har mi akai kai Halima ne ma. Ai wannan yaƙin namune gaba ɗaya, shiyyasa naita nuna miki ki kwantar da hankalinki akan haukan da kike na tsinema Mustapha a banza saboda farin cikin Halima da ƴarta. To gashi nan tun ba’aje ko’inaba sun fara nuna miki halinsu”.
Kukan takaici da baƙin ciki Mommy ta fashe da shi………..
Ashe haka duniya take ƙafar kazace. Aminai biyu ya hakane ? Yanzune fa wasan na ainahi zai fara, dan za’ai yunwa muga cikin
kowa .