BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 7

Typing????

 *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
       _(Miya kawo kishi?)_     *_Bilyn Abdull ce????????_*

07

………Tunda suka tafi tsakanin shi da ita babu wanda yayma ɗan uwansa magana. Yanata tuƙinsa da amsa wayoyi itako tana buga game a wayarta cike da nishaɗi har suka iso. Motar ta buɗe tai ficewarta tana taɓe baki, sai da ta rufe masa ƙofar batare data kallesaba tace, “Jazakallahu khairan” tai gaba abinta. Fusgar motar yay da ƙarfi yay gaba har yana tada ƙura. Hakan yasata faɗin, “Kaji dashi in kayane dai”.

        Koda ya tashi a aiki baibi takanta ba yay wucewarsa gida. Tun Anam na jira da marmari har ranta ya fara ƙuna gashi bata sayi layin Nigeria ba har yanzun. Sosai ranta yake a ɓace ga yunwa dake bala’in cin hanjinta dan bawani abun kirki taci da safeba ta fito, da rana ko inibi data taho dashi a bag kawai tasha da strawberry. Ganin yamma na ƙara mata, gashi bata san yanda zata kira wani a gidan ba tunda babu waya ta fito domin samun abun hawa ko zata iya ganewa. Ga wani irin zafi dake ratsata duk da rana ta risina kasancewar anyi la’asar, sai dai ita zafi takeji matuƙa kodan inda ta fito akwai ac ne.
        Ta tare abin hawa yafi sau huɗu amma ta rasa yanda zata musu misalin anguwar, wasuma basa gane jagulalliyar hausarta da yaren malay ya cinye, turancin ma idan tayi wasu suce basaji wasu suce basu fahimci kwatancenta ba. Kanta ta dafe ƙwalla na cika mata ido dajin wani irin tsanarsa a cikin ranta, tabbas bata ƙaunar wulaƙanci shiyyasa bata wulaƙanta kowa, kai bama ta tashi taga iyayenta na wulaƙanta wani ba kowa abin girmamawarsu ne koda bai kaisu wani matsayi na duniya ba. Hannu takai a hankali ta share ƙwallar idanunta tana maijin kewar iyayenta da ƙaunarsu, waɗannan matsalolin na ɗaya daga cikin abinda ta guda a zuwanta hidimar ƙasa Nigeria, amma su Mamie suka kasa fahimtarta…….
        Harya gota ta ya dawo baya da mamakin kodai gizo idonsa ke masa. Dai-dai saitin da take yay parking da sauke gilashin motar. Tabbas itace inhar bai ruɗeba, dan yanda yarinyar ta shiga ransa bayajin zai manta fuskarta koda a barci ya tashi.
     “Beauty!”.
  Ya faɗa cikin tsantseni da taraddadin wasiwasi.
           Duk da tajisa tunma tsayuwarsa hakan baisa ta ɗago ba. Sai ma sake haɗe fuska da tai ta ɗauke kai gefe fiye da yanda ya sameta. Murmushi ya saki dan yanda tai ɗin ya tabbatar masa ita ɗince. Buɗe motar yay cike da farin ciki ya fito. “A gafarce ni. Assalamu alaiki ƙyaƙyƙyawa”. Duk da bata saki fuska ba ta amsa masa. Ya koma ta gabanta cikin sake raunana murya. “Inaji a jikina ke rabonace Beauty. Ranar Yayanki ko saurayinki ne ban saniba ya gudumin dake gashi yau ALLAH ya haɗamu daga ni sai k”. Karon farko ta ɗan ɗago ta dubesa, ya sakar mata murmushi. “Dan ALLAH kar kice baki ganeni ba”.
     “Bamma taɓa ganinka ba”.
Ta faɗa da ƙoƙarin barin wajen. Sauri bin bayanta yay. “Please dan ALLAH karkimin haka. Ni ne wanda muka taɓa haɗuwa a GJ restaurant da daddare”. Sarai ta ganesa tun kiranta Beauty da yay dan muryarsa bata bace mata ba. Amma sai ta sake ɓata fuska aɗan fusace tace, “Bani bace Please kabar bina”.
       “Kiyi haƙuri bazan iya daina binki ba wlhy dan kullum cikin addu’a da sadaka nake akan ALLAH ya sake nunamin ke. Ya kuma amsamin sai nayi sakaci da damata”.
   Sosai ya bata dariya a wannan gaɓar, wai sadaka. Dan kawai ya ganta zaiyi sadaka. Hararsa tai zata sake wucesa ya babbake ko’ina. “Dan ALLAH ki saurareni”. Kanta ta dafe dan yanata faman haɗata da abinda bazata iya jayayya ba. Hakan yasa dole ta nutsu ta sauraresa. Bawata magana sukaiba damar kaita gida kawai ya nema. Bata da mafitar data wuce binsa, amma maimakon gida da yace zai kaita sai kawai ta buƙaci ya kaita inda zata sai layin waya. Bai musa mataba, dan a ganinsa hakanma wata damace.
        Kai tsaye office ɗin mtn dake cikin wata plaza yakaita duk da yasan sun tashi aiki yanzu. Sai dai yanada alfarmar da za’a iya biya mata buƙatarta a wajen. Ilai kuwa tarba ta mutuntawa taga ana masa a wajen, yanda kuma suke gaisuwa da ogan wajen taji a ranta ɗan uwansane ko aboki.
      “Mutumina wannan ƴar shilar fa haka?”.
    Abokin ya tambaya cike da shaƙiyanci cikin zaurancen hausa da Anam ta kasa gane komai dan shima ya fahimci bata iya hausan ba, saboda yanda yay mata tambaya da hausa ta gagara bashi amsa mai ƙyau. Dole suka koma magana da turanci. Murmushi kawai yay batare daya bashi amsaba, sai ma danna waya da yake faman yi abinsa.
     “Wai ka zama kurma ne?”.
Abokin ya sake tambaya yana harararsa.
       “Sarai ina jinka. Kai dai yi aikinka  kawai ba buƙatar tambayar ne”.
   Dariya kawai abokin yay ya cigaba da ƙoƙarin ɗaukar Anam hoto. Tun a gurin ta ɗora layin akan wayarta, ta kuma tambayesu ko zata iya amfani da shi. Kasancewar abokin nasa babban ma’aikaci sai ya amshi wayar yay ƴan danne-danne ya miƙa mata. “Indai kiran gaggawa kike sonyi da shi bashi nan da mintuna talatin sai kiyi”.
    Godiya ta masa tare da duban saurayin da har yanzu ko sunansa bata sani ba. “Zamu iya tafiya?”.
     “Why note Beauty”.
  Ɗan murmushi kawai tai da mikewa. Shima ya bama abokin nasa hannu suka cafke. “Friend ina zuwa ka jirani Please ”.
     “Ba damuwa”.
Cewar abokin nasa yana dariya.
        
    Ganin sun ɗan gota plaza ɗin tace su ɗan tsaya mintuna talatin ɗin su cika. Bai musaba sai dai ya kalla agogonsa duk gudun kar lokacin salla ya shiga. “Beauty inaga muɗan matsa gaba akwai massallaci sai na shiga nai magrib ko”.
     “Babu damuwa”.
Ta faɗa hankalinta akan wayarta. Tun fitarsa a motar babu abinda take sai irga mintuna har ALLAH yasa suka cika. Kai tsaye number ɗin Abie tahau gwadawa dan ta loda kati daga kuɗinta na bank a ciki. Taƙi samunsa saboda network. Komawa tai kan Mamie itama dai yaƙi tafiya kiran. A take idanunta suka sake cika da ƙwalla, ta kife kanta a gwiwarta tana karanto duk addu’ar da tazo mata a baki. A haka ya dawo ya sameta. Sai dai tanajinsa tai azamar goge hawayen nata ta haɗiye kukan.
     “Beauty ina muka dosa yanzu kenan?”.
           “Abinda nake tunani kenan, dan kona maka kwatance ba lallai ka gane ba. Amma in ban takurakaba ka kaini restaurant ɗin nan kawai ka ajiye zan samu mafita”.
        Kallonta kawai yake cike da nazari. “Na miki wani tambaya mana in bazaki damu ba?”.
    Shiru kamar bazata amsashi ba. Sai kuma taja numfashi da jinjina masa kanta. Gyara zamansa yay sosai yana fuskantarta. “Harshenki ya tabbatar min idan ma ke ƴar Nigeria ce ba’anan kike rayuwa ba? Hakan na nufin ke baƙuwace shiyyasa bazaki iya gane inda zakije ba?”.
       Nanma kamar bazata amsashi ba sai kuma ta ɗan kallesa ta duƙar dakai. “Karka damu ka kaini inda nace kawai Please”.
   “Baki son na sani ko?”.
“No, kawai”.
Ta faɗa a taƙaice. Bai sake magana ba ya ɗan rausayar da kansa da yima motar key yana murmushi.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button