BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 8

Typing????

 *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
       _(Miya kawo kishi?)_     *_Bilyn Abdull ce????????_*

08

……….Tunda ya amsa wayar ya turama wadda ta kira da sister ɗinta address ɗin inda suke yaketa lallashinta ko ruwa tasha amma taƙi sai faman sharɓan hawayema takeyi. Hakan yasa yay tagumi kawai yana kallonta. Komai tai birgesa takeyi, Duk da ƙaramin jiki da take da shi kai kasan ba yarinya bace, sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci lallai ƴar gatace a gidansu dan saurin karayanta yayi yawa. Hoto ya fara mata yana Babumurmushi batare data sani ba…..
         Tunda ya shigo idonsa ya sauka a kansu. Wani irin baƙin ciki da ɓacin ransa sai suka ƙara ninkuwa. Nufarsu yay rai a ɓace sai dai bazaka taɓa fahimtar hakan akan fuskarsa ba duk da ya ciskulleta sam babu fara’a. Kamar ance ta ɗago idonta ya sauka a kansa. Babu shiri ta miƙe zumbur dan yanayinsa ya tsorarata, bata manta dukan da yay musu ita da Aysha ba. Wani irin mugun kallo yay mata ya ɗauke kansa ya maida ga saurayin da shima ya miƙe dan ya gansa. Kallon banza da tsana yake masa yayinda shi saurayin yay ƙoƙarin mika masa hannu suyi musabaha yana murmushi duk da yaga kallon banzar amma ya shanye.
    Kallon hannun yay ya wani ɗauke ido da maidawa kan fuskarsa yana mici-mici da idanunsa dan sarai ya gane shine ranar yayta binsu daga wannan restaurant ɗin…..
       “Kana buƙatar ka zauna lafiya?!!”.
    Duk da a yanda yay maganar cike da isar gadara hakan bai hana saurayin sakin murmushi ba da jinjina kansa. Cikin sauƙaƙa tasa muryar yace, “Sosai kuwa babban Yaya. Ai magabatanmu kance zaman lafiya yafi zama ɗan sarki”.
     Kansa ya ɗauke duk da shine ya buƙaci amsar kuma aka bashi. Wani ɗan juya harshensa yay cikin bakinsa cike da basarwa yana sakin murmushi mai harshen damo. Sai kuma ya jinjina kansa da sake maido dubansa ga saurayin fuska a haɗe. “To daga yau, daga yanzu, karka bari na sake ganin wannan fuskar taka a inuwa ɗaya da ita. Inba hakaba……”
    Ya ƙarasa da wani shegen murmushi dimple ɗinsa na loɓawa, yaɗan bubbuga kafaɗar saurayin. Bai saurari amsar da saurayin zai bashiba ya fisgi hanun Anam dake maƙure waje guda zuciyarta kamar zata kifo ƙasa. Da tasan shine zaizo ɗaukar tata data aminta da shawarar saurayin daya buƙaci Aysha ta tura address ɗin gidan shi ya kaita amma taƙi. Jakkarta dake kan desk ɗin ya fusga itama tare da wayarta yay gaba da sake yima saurayin warning da idanunsa dake rine matuƙa fiye da yanda ya shigo wajen…..
      Turata yay a motar ya rufe har saida ta zabura dan kaɗan ya hana ya datse mata yatsun hannu. Ya zagayo mazauninsa tare da figar motar a guje yabar wajen. Yanda yay ɗin yay masifar sake firgitata har sai da ta faɗa gefen hanunsa ta ƙudundune fuskarta tana kiran sunan ALLAH, dan ta zata gabzama motocin gabansu karo zaiyi ma. Ƙuwwww!!! Ya taka birki da daka mata wata razananniyar tsawa. Saurin sakinsa tai tai baya a firgice, sai kuma ta fashe da kuka dan gaba ɗaya ya sake firgitata ta tsani tsawa…
         “Stupid! shut up!!. Idan baki rufemin shegen bakinki ɗin nan ba na fara kashe fuskarki da maruka sai kin suma. Wawuya kawai. K har idonki yay tsurin bin motar saurayi kuje restaurant?! Dama abinda kikazo yi kenan a Nigeriar?!!!”.
      Yanda ya ƙare maganar a matuƙar tsawace ya sake birkitata. Amma sai ta danne cikin ƙarfin hali tace, “ALLAH ya kiyaye danni ba mayyar maza bace”.
Ya sake watsa mata harara kai kace cinyeta zai da jajayen idanun nasa. Sai kuma yay ƙwafa da ɗauke kansa yana sake tada motar. Ko motsin kirki bata sakeyi tunda ta samu bai maketa ba. Kukan ma ta daina na zahiri na zucici takeyi. Gaba ɗaya jitake tama gama tsanar Nigeria, ita dai gaskiya bazata iya wannan masifar ba, tun farko abinda ta guda kenan amma su Mamie sukaƙi fahimtarta. Itakan duk ma yanda za’ai a satin nan sai tabar Nigeria hidimar ƙasar nan bazata yuwuba…..

       Ko gama dai-daita parking baiyiba ta fita dan mutanen gidan duk suna tsakargida tsaitsaye Gwaggo da Mommy ne kawai babu sai irin su Fawwaz da sunyi barci tuni basu san abinda akeyiba. Aysha ce ta taho da gudu suka rungume juna, sai kuma ta saketa taje ta rungume aunty amarya da Mom. Su Daddy da tuni Aysha ta kirasu suka dawo gida zaman jiran isowarsu suma ajiyar zuciya kawai suke saukewa..
      Mom dake shafa kanta da murmushi tace, “Kukan ya isa haka mana mamana. Tunda kuma an dawo gida sai muce Alhmdllhi. Jeki gaida iyayenki”.
    Babu musu ta saki Mom tana share hawaye ta nufi su Abba. Gaishesu tai hawaye na sake silalo mata, abinka ga ƴan boko kasa daurewa Daddy yay sai da ya ringumeta. “Haba Mamana ina kika shige haka duk kin tada mana hankali”. Ya faɗa yana mai ɗagota a jikinsa. Murmushi tai tana share hawayen da suka ƙi tsayawa. “Daddy na kasa ganewane, idan na tsaida masu keke ɗinnan sai suce basu gane yanda nake faɗa musu gidan ba”. Tausayinta sosai ya ƙara kamashi, kanta Abba ya shafa yana murmushi. “Dole ki dage ki koya hausa a zaman nan Mamana, dan rashin iyawan ya taka rawar gani cikin accident ɗin nan”.
      “A’a Abba dan ALLAH ni zan koma  Malaysia”.
    “Tsit gurin yay babu wanda ya iya cemata komai. Sai Shareff ne ya wani taɓe baki da barin wajen ko uffan baicema kowaba balle bayanin yanda ya samota dan a matuƙar gajiye yake ga ciwon kan nasama zazzaɓi yake neman komawa. Daddy ya kashe shirun wajen da faɗin, “Kuje ciki tai wanka taci abinci dan tana buƙatar kwanciya da wuri. Mamana mayi magana da safe”.
    Badan tasoba tabi Mom dan bata iya musu ba kuma. Duk da yanda Aysha ke tsoron faɗan Mom haka tabi Anam sashen Mom da ƙudirin su kwana tare, dan jitake kamar kafin safiya za’a ƙara cemusu ba’a gantaba ta sake ɓata.
  
   Washe gari tunkan ma Anam ta kira Abie ɗinta ta sanar masa Daddy ya kirasa sukai magana. Yayma Shareff kuma faɗa sosai kamar zai ari baki. Daga ƙarshe ya kafa masa dokar hukuncinsa shine kai Anam wajen aiki kullum ya kuma ɗakkota. Idan ko wata matsala ta sake shigowa akan Anam to lallai ya kuka da kansa dan sai ya matuƙar ɓata masa rai a gidan.
      Shi dai Shareff ɗin baice komai ba akan hukuncin. Sai Mommy ce tace sam bata yardaba ɗanta ba driver bane ba. Ko kallonta Daddy baiba, ya dai tabbatar mata idan Shareff ya isa yaƙi bin umarninsa.
       Ai wannan magana ta dagula ran Mommy a safiyarnan. Dan tata masifa ita da Gwaggo data fito tana goya mata baya. Daga Daddy har Abba babu wanda ya sake tofa tasa dan sukam dai yanzu sai dai su kalla Gwaggo kawai tunda sun fahimci bata ƙaunar zaman lafiyarsu da ɗan uwansu, Halima ce kawai ta kasa fahimta sun kuma barta wataran zata gane da kanta musamman da suka san idan akai auren nan na Fadwa da Shareff.

        ★★★★

  Duk yanda Mommy taso hana Shareff ɗaukar Anam hakan bai yuwuba. Dan shi dai haƙuri kawai ya bata da nuna mata illar fushin mahaifinsa a garesa. Ya roƙeta ta kwantar da hankalinta a hankali zai janye jikinsa ya samama Anam ɗin driver kowa ma ya huta. Wannan magana tashi ce taɗan kwantar mata da hankali ta maida kanta ga hidimar shirye-shiryen bikinsa.
      Daga ɓangaren Anam ma taci uban borinta akan malaysia zata koma ta fasa hidimar ƙasar su Mamie suka lallasheta da tabbatar mata cewar idan sukazo bikin Shareff zasu san abinyi. Hakanne yaɗan kwantar mata da hankali ta zauna zaman jiran lissafin kwanakin bikin. Yayinda ta cigaba dabin Shareff ɗin a takure. Shike kaita shike ɗakkota, daga gaisuwa babu abinda ke haɗasu sai harara. Ita kuma tata tura baki kenan da ɗaure fuska ita a dole haushinsa takeji duk da bata da riƙo sam wannan karon dai ta riƙe.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button