BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 7

         Koda suka iso kamar yanda ta buƙaci ya tafi ya barta a wajen bai yarda yayi haka ba. Cikin lallashi ya sata suka shiga wajen. Yabi ya takura mata akan ta faɗi mi take son ci amma taƙi, dan Anam nada wani hali inhar bata saba da kai ba bata taɓa yarda ta sake da kai. Shi kansa badan tana neman mafitaba bazata bisaba tun farko ko wane irin naci zai mata kuwa. Haƙura yay ya amsar musu drinks kawai da snacks amma ko kallon natan bataiba balle yasan zataci.
    Tunanin kiran Aysha ne yazo mata a rai. Ta sake zaro wayarta dake cikin bag ta hau lalubenta. Cikin sa’a kuwa kiran ya shiga, sai dai harya katse ba’a ɗaga ba. Bata gajiba ta cigaba da kira har wajen 8missed call amma babu amsa. Da ƙyar ta iya ƙoƙarin danne kukan dake son taho mata……


      Ko kaɗan baiyi tunanin bazata iya maido kanta gida ba. Hasalima zuciyarsa raya masa take tuni ta dawo ɗin saboda yayi over time a office yau yana aiki, ga kansa na masa ciwo. Daya shigo gidan ma a ɗan gurguje ya shiga suka gaisa da Mommy ya fito. Wanka yayi a gaggauce shima saboda magrib dake kusantowa. Koda ya kammala shiri ya fito a compound ya haɗu da Abbah da Khaleel suma zasu massallaci. Tare suka fice, bayan an idar da magrib basu dawo gidaba sukai zaman jiran isha’i….

       Tun kafin su ƙaraso suka hango Mom da Aunty Amarya tsaye cirko-cirko a ƙofar sashen aunty Amaryar. Dukansu sai suka nufi can dan da alama babu lafiya. Shidai kusan shine ƙarshe dama. Daddy da suka haɗu a massallacin ne ya fara jefama su aunty amarya tambayar “Lafiya kuke tsaye anan haka?”. Aunty amarya ta bashi amsa cikin damuwa da ruɗani. “Daddyn Shareff lafiya ba lafiya ba. Anam ce bata dawo gidaba har yanzun. Mubarak yaje har wajen aikin nata kuma maigadi ya tabbatar masa babu kowa a ciki ita ɗincema kusan ƙarshen fita, ta kuma jima a titi kafin yaga wani ya ɗauketa a mota”.
      “Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un”. Daddy da Abba suka faɗa kusan a tare. Shareff ma dake daga bayansu gabansa ne ya faɗi, suka haɗa ido da Daddy daya juyo yana masa kallon tuhuma. cikin son danne abinda keson taso masa yace, “Shareff nasan dai kaji mi mamarku ta faɗa ina ka baromin yarinya?”.
      Sosai ƙirjinsa ke luguden duka. Ya girgiza kansa da risinar da idanunsa da sukai sirkin ja kaɗan saboda gajiya da ciwon kai.
      “Ba girgizamin kai zakaiba ka buɗe baki kai magana!!”. Daddy ya sake faɗa a tsawace.
            Kansa a ƙasa yace, “Ban baro office ba sai kusan 6, shiyyasa nai tunanin ta dawo gida”.
    “Shareff are you out of your senses?!! Har kake gayamin kazata tama dawo gida. Kana da hankali kuwa? Innalillahi wa-inna’ilaihirraji’un”.
         “Wai lafiya mike faruwa ne?”.
Mommy da Hassan yaje ya sanarma gidan babu lafiya ta faɗa tana ƙarasowa wajen. Babu wanda ya iya bata amsa saboda maganar da Daddy ya cigaba dayi a kausashe cikin kuma tsananin ɓacin rai….
       “Wlhy na baka nan da zuwa ƙarfe sha biyun dare ka kawomin yarinyata gida, inba hakaba sai ranka yayi mummunan ɓaci Al-Mustapha!!”.
           Cikin sauri Mommy ta dakatar da shi itama a fusace. “A’a Alhaji kamarya da wannan hukunci haka. Shine ya ɓatar da koma wacece ake neman da za’ace ya fita a wannan daren nemanta bay……”
        “Babu ruwanki a wannan maganar, idan kuma kikace zaki shiga wlhy zan sakaki nadama ne!!”.
      Gaba ɗayansu binsa sukai da kallo ganin yanda yabar wajen a matuƙar fusace. Banda Shareff da kansa ke ƙasa. Abba ne ya dubesa da damuwa shima, sai dai cikin sauƙaƙa murya dan bai kai Daddy zafi ba yace, “Son kayi kuskure. Ka manta Anam babu inda ta sani, ko anguwarnan bana zaton ta san sunanta ma, kag……..”
     A harzuƙe Mommy ta katse Abba “Anam!!. dama akan wannan tsifatar yarinyar ake wannan tada jijiyar wuyar? Shareff bance ka fita harkar yarinyarnan ba a gidan nan?”.
      Bai iya ya ɗago ya kalleta ba, dan baisan wace amsa zai bataba. Tana ƙoƙarin nufosa isowar Gwaggo ya dakatar da ita. “Wai hayaniyar mi nakeji a gidanne haka kai?”. Duk juyawa sukai gareta. Ganin kowa ya kasa cewa komai Khaleel yace, “Anam ce bata dawo gida ba”.
       “Shine miya faru kuma? Ita ɗin yarinyace?”.
      “Haba Gwaggo ya zakice haka? Nawa Anam ɗin take? Sannan ina ta sani bayan kinsan kamar baƙuwa take a ƙasarnan bama garin kano ba”.
          Harara Gwaggo ta zubawa Abba mai maganar. “Oh to kana faɗaminne ko kana tunamin Abubakar? Gallaƙeƙiyar budurwa da yanzu idan aka sakata ɗaki da namiji zata samo ciki kake sanarmin nawa take? Toni abindama ban ganeba mi’akema hayaniyar anan?”….
      “Titsiye Shareff sukai yaje nemanta kamar shine yace ta tafi yawon tazubar ɗin, dan nasan bai wuci can ɗin ta tafi ba tunda an saba a inda aka fito..”
       “A lallai kuna bukatar Addu’a Abubakar. Shi Mustapha ɗinne ya kaita ya ɓatar da zakuce yatafi nemanta a wannan daren bayan wahalar da yaje ya gama shawowa a wajen aiki ya dawo. Kai Mustapha muje naga ubanda zai saka fita ko nan da gate a daren nan dan…….”
     Sauran maganar ta maƙale ganin kaf wajen babu alamar Shareff ɗin. Su dukansu babu wanda yasan yama sulale yabar wajen. Horn da ƙarar buɗe gate ya sakasu juyawa can gaba ɗayansu. Sai dai kafinma wani yay wani yunƙuri har motarsa ta fice…..

         Wajen aikin nata ya fara zuwa, sai dai kamar yanda maigadin wajen ya faɗama Mubarak shima haka ya sanar masa. Lokacin da yake tafiya a hankali ya dinga tafiya kozai ganta a hanya. Amma ko alamarta babu duk da titin wajen tako’ina akwai hasken fitulun solar. Duk da hakan bai fasa sake bi a hankali yanzun ma yana dubawaba har ƙarshen titin. Ganin har tara ta gota na dare yay fakin gefen titi ya kifa kansa kan sitiyari dan ciwo yake masa matuƙa kamar zai faɗo ƙasa. Dama tuƙin yinsa kawai yake cikin dauriya.

           A gida kowa ka kalla a cikin damuwa yake, idan ka cire Gwaggo da Mommy da suketa bala’i da kowa ya kasa fahimtar dalilin yinsa. Aysha harda kukanta. Dan ansan ko wayarta aka nema baza’a samuba tunda bata da layin Nigeria. Abba da Daddy da Khaleel ma sun fice police station.
      “Aunty wayarki sai haske yake tun ɗazun”. Hassan ya faɗa yana duban Aysha data zuba uban tagumi tana sauraren masifar Mommy kawai daketa faman kai kawo tsakanin bedroom ɗinta zuwa falo. Kamar Aysha bazatabi takan wayarba sai kuma tacema Hassan “Ciromin daga cajin”. Ciro mata yay, ganin bata san no ɗinba tai tsaki ta ajiye. Duk kiran da aka cigaba dayi har kusan sau biyar bata kulaba. Sai ma ɗaukar wayar datai rai a ɓace zata kashe sai saƙo ya shigo da no din da aketa kiran nata. Guntun tsaki tai ta buɗe dan taga wai waye ma ya addabeta ya barta taji da damuwarta ma itakam. Zumbur ta miƙe da waro idanu, har zata fasa ihu sai kuma tai saurin gumtse bakinta da satar kallon inda Mommy take. Tai saurin haɗiye farin cikinta ta nufi bedroom ɗinsu da sassarfa. Jikinta har rawa yake ta maida ƙofar ta rufe harda saka key tana dailing number ɗin…
      “Blood da gaske kece?”.
Kamar jira Anam keyi ta fashe mata Aysha da kuka. “Ya ALLAH Blood Please kibar kuka, kina ina ne yanzu? Ga gida duk hankalin kowa a tashe da rashin dawowarki su Yaya dasu Abba duk sun fito”. Ta ɗanji sanyi, amma hakan bai hanata jin zafin Shareff ba. Da ƙyar tace, “Zan tura miki address ɗin yanzu bansan inaneba”….. Aysha na katse kiran tai kiransa.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button