BABU SO 70
Chapter: 70 Share:
Report
BABU SO View: 283 Words: 2K
Chapter 70 70
……..Wasa farin girki wai amarya da tuƙa
tuwon tiya goma. Ashe rikici a waya tsakanin Mommy da Gwaggo Halima somin taɓi ne. Dan kuwa ba’a rufa awa guda cikakkiya ba sai ga Gwaggo Halima tazo gidan. Hakan yayi dai- dai da dawowar Daddy daga wajen aiki gidan shima. Yay sagade yana kallon Gwaggo
Halima data ƙaraso garesa tana huci. “Halima lafiya kuwa da magribar nan?”. “Inafa lafiya Yaya, Share! ya buɗe ƙwanji ya
shashsheka ma Fadwa mari amma saboda
son zuciya irin na matarka ta goya bayansa
saboda itace ta haifesa”.
Da mamaki sosai yace, “Mari fa dai? Ya
ALLAH mike damun Share! haka? Wannan ba
maganar nan bace shiga ciki nafara zuwa salla
kafin su Abubakar su dawo”.
A maimakon sashen Mommy ko Gwaggo da
da idan tazo gidan take shiga yau sai ta nufi sashen Mom…..
____★
Rashin fitowarsa har aka kira sallar magrib yasaka Anaam kasa zaune ta kasa tsaye. Tana son zuwa dubashi tanajin tsoro. Gani take kamar itama ɗin marin nata zaiyi. Harga ALLAH tana matuƙar tsoron duka a rayuwarta. Koda wani taga ana duka firgicewa take. Ballema har abada bazata taɓa iya
manta dukan dayay musu ba ita da Aysha. Da sauri ta juyo jin motsin buɗe ƙofa. Sukaima juna kallon cikin ido ita da shi, ita ta fara janye nata tana sauke ajiyar zuciya dajin shakkar
kallon fuskarsa dake a matuƙar tsuke. “Ki tashi kiyi salla”.
Ya faɗa a taƙaice da juyawa zai fita. Harya kama handle ɗin ƙofar zai fita ya tsaya cak, juyowa yay a hankali yana kallonta saboda ganin yanayinta. Sai dai baice komaiba ya juya ya fita. Numfashi ta saki a hankali da miƙewa ta shiga toilet domin ɗauro alwala.
Bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha’i, kai tsaye kuma sashenta ya zarto. Tunda ta idar da salla ta kasa tashi a wajen, babu abinda ke mata kaikawo, haka kawai marin nan na ɗazun da yay ma Fadwa ya matuƙar tsaya mata a rai, duk da kuwa ƙararsa kawai taji bawai yinsa akan idonta ba. Harya ƙaraso gabanta bata san da shigowarsa ba, ya kai tsugunne gabanta, tare da ɗago haɓarta. Cikin idanunsa ta zuba raunannun nata da babu gilashi, bata ganinsa fes yanda ya kamata, amma hakan bai hanata tsaidasu a
tsakkiyar nasan ba… “Mike damunki?”.
Ƙoƙarin janye idanunta tai a cikin nasa ya hana hakan, taso kauda kanta gefe nanma ya
hana, saita ƙara tsuƙe fuska da tura baki. A karon farko ya saki murmushi, tare da kai yatsansa ya ɗalli lips ɗin nata. “K wai baki san shekarunki sun girmi wannan taɓaran ba Autar mata?”.
Hanunsa ta ture zata tashi, yay saurin
damƙota yana dariya, jikinsa ta faɗa, dan
haka suka zube ƙasa gaba ɗayansu. Ƙafarsa
ɗaya ya kwanta, tare da jawota ya kwantar a
cinyarsa ita kuma. Ya tokarar da ɗayar ta
jingina kanta. “Nayi laifi ne wai?”.
Hanunsa dake kan cikinta ta kamo, ta saka
babban ɗan yatsan a bakinta ta ciza. “Wai wai
shiii! Wace mugunta ce muka wannan?”.
Dariya ta ƙyalƙyale da shi. “Noorie muguntafa
babu ƙyau sam sam”. Ka ɗan ta murguɗa
masa baki “Punishment ɗin mai yawo ne ai”. “Shi kuma punishment ɗin mai rashin kunya
fa? yaya ya kamata ya kasance?”. “Sai an binciko a littafin shara’a”.
Ta faɗa tana ƙoƙarin mikewa ta gudu. Riƙota yay yana ƙaramar dariya. “Sarkin wayo ai ni tuni na binciko. Yanzu kuma zan ƙaddamar da shi”.
“Wayyo yaya! Wayyo ni yunwafa nakeji, tun safe banci komai ba.”
“Nima ita nakeji ai”. Ya ƙare maganar da manne lips ɗinsu waje guda. Ko sau ɗaya batai ƙoƙarin hanashi ba, saima gudunmawa
data fara bashi, burinta kawai taga ya huce
daga fushinsa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gama
hautsina masa kwanyar kansa, tun yana binta
a salon jarumta harya fita a hayyacinsa ya
ɗauka wata hanya da ban da karatun da ya
kasance mai girma ga Anaam. A yanzu kam ita
ya nema gigitawa, yayinda shi tuni ya fita
hayyacinsa har baya gane ita ɗinfa ƙanwarsa
ce. Sunyi matuƙar shagala a farantama
junansu ring ɗin wayarsa ya shammacesu. Da
ƙyar Anaam ta iya janye jikinta dake rawa
gefe. Shima nashin rawar yake fiyema da tata,
sai dai jarumtar ƴan mazan ta ɓoye haka, ya
rimtse ido da ƙarfi ya sake buɗewa saboda
ganin mai kiran. Ko’a turu a kwantosa bai isa
ɗaga wayar nan ba, dan babu makawa sai
Daddy ya gane halin da yake a ciki. Haka ya
barta harta tsinke wani kiran ya ƙara shigowa.
Yanzun ma kasa ɗagawar yay har saida ta
yanke, da ƙyar ya samu iya ɗan dai-daita
kansa bayan wasu mintuna sannan yay kiran
Daddyn Back.
Koda Daddy yaji muryarsa a shaƙe a zatonsa
duk ɓacin rai ne, dan kuwa yasan wanene Share! idan yay fushi. “Ka sameni a gida yanzun nan kai da Fadwa”. Bai jira cewarsaba ya yanke kiran. Shima ɗin baice komaiba ya koma kwance tare da mirginawa jikin Anaam
data juya masa baya ya rungumota da ɗaura
kansa a gefen wuyanta yana shinshina, ga
sanyin tiles na ratsasu dan harya huda
sallayar tana iya jinsa a jikinta shima haka.. Jin saukar hanunsa a ƙirjinta tai saurin
riƙewa. “Yaya kirankafa Daddy yakeyi”. Iska ya ɗan hura mata cikin kunne da ture hanunta ya ɗaura a inda yay niyya tun farko. “Koratama kikeyi kenan?”.
“Eh mana, Daddy ba abin wasa bane ai,
umarninsa yana sama da muradanmu”. Sassanyan murmushi ya saki da sake
ƙanƙameta a jikinsa, a hankali ya furta Ina ƙaunarki da yawa”. Sosai tsigar jikinta ta yamutsa saboda yanda yay furucin a cikin wani irin wahalallen sauti. Taja numfashi mai kauri da cije gefen lips ɗinta sakamakon saukar kiss ɗinsa saman wuyanta. Bata iya ta ɗago ta kallesa ba harya fice daga ɗakin. Ta sauke sassanyar ajiyar zuciya da sake kananneɗe jikinta waje guda wani abu mai girma na tsikarar ƙasan zuciyarta….
A sashen Fadwa kan duk da yaji a ransa itace takai ƙararsa wajen su Daddy bai mata magana ba, umarnin kawai ta samesa a mota ya bata ya juya ya fita abinsa. Taja wasu mintuna kafin ta fito dan har ya kunna mota
ma.
Tafiya suke amma kowanne fuskarsa na gefe,
ita tana kallon mutane shi kuma titi har suka iso. baiyi mamakin samun Gwaggo Halima ba, Fadwa ta nufeta ta rungumeta tana sakin kuka. Lallashinta ta shigayi tana shafa bayanta da fuskarta wai tana neman tabon marin. Abin sai ya girmi kan kowa amma babu wanda yay magana sai Mommy ce taja tsaki da taɓe baki. Share! kam zama yay ƙasa a tsakkiyar ƙafafun Abie da Abba. Kansa a ƙasa batare daya kalla kowa ba ya gaishesu. Haka kawai yakejin tsananin kunyar Abie da Mommynsa fiye da kowa a wajen.
Abba da yaga mulmular da Gwaggo Halima kema Fadwa na neman yin yawa ya magana a kausashe. “K Fadwa tashi ki zauna da ƙyau bama son shashanci”.
Tashin tai zaune, sai a sannan kuma take
gaidasu. Iya su mazan kawai suka amsa.
mommy da Gwaggo babu wanda ya tanka.
Gwaggo Halima tai ƙaramar ƙwafa da ayyana
(Zanyi maganinku) a zuciyarta.. Abie ne ya
buɗe taron da addu’a, kafin ya maida
hankalinsa ga Share! cikin serious matuƙa. “Al-Mustapha miya haɗaka da matarka
harda mari? Bayan wannan ba ɗabi’ar dakaga wani a cikinmu nayi a gidan nan bane?”.
Ƙasa Share! ya ƙarayi da kansa, cikin
matuƙar girmamawa. “Kuyi haƙuri Abie nayi
kuskuren aikata hakan, sai dai saida na
umarceta ta tashi tabar inda nake dan bana
son yanke hukunci cikin fushi, amma taƙi yin
hakan har takai nayi marin”.
“Amma banda abinka Babana ai kai
babbane, da taƙi tashi sai kai ka tashi ka bata
waje tunda kasan baka iya controling kanka a
yanayin fushin. Su mata haƙuri ake dasu a
kowane hali, domin hangenka da nasu sam ba
ɗaya bane ba, sai dai sunada sauƙin sha’ani
kuma ba koda yaushe ake cizawa a kansu ba”. “Hakane Abie, insha ALLAHU hakan bazata
sake faruwa ba……”
“Tama sake faruwar mana. Wlhy da kaina zan
rama mata mara mutunci kawai. Kai yanzu
dan baka da kunya Share! har kanada hanun
ɗagawa ka daki Fadwa a gidanka?”. “Yaya Halima! Ya kamata kiyi shiru abi
komai a sannu”.
“Wane kuma sannu Abubakar, bayan kanaji
yana lallaɓashi saboda ba ƴarsa aka mara ba”. Murmushi Abie yay da girgiza kansa. Cikin
dattako da nutsuwar da kowa ya sansa da ita ya fuskanci Gwaggo Halima. “Ba haka bane Yaya Halima. Da Share! da Fadwa da Anaam duka su ɗin ƴaƴanmu ne, bazamu taɓa sakaci da cutuwar ɗayansu ba ai. Da kinyi haƙuri zan