BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 70

kai inda kike buƙata nima ai”.
Baki ta taɓe da juya kai gefe. Nanma
Murmushin Abie ya saki kawai ya sake maida
hankali kan Share! da ransa ya ɓaci. “Babana
ina jinka miya haɗaku takai ga mari?”. “Ban taɓa fatan dan na samu matsala da
wata a cikinsu sai munzo gabanku ba. Amma
tunda ita tafi zaɓar hakan a koda yaushe fine.
Fita nai a gida tun safe ina wajen matsalar can
data taso a company, na dawo kawai na samu
ta cikamin sashe da ƙawayenta wai suna min
gyara. A yanda suke komai kai tsaye ya
tabbatar min ba yau ce rana ta farkon hakan
ba. Korarsu kawai nai na ƙyaleta domin ita
tasan bana son yanke hukunci cikin fushi,
amma saita biyoni bayan nace ta ƙyaleni a
yunƙurin farko da tai. Taya zata kawomin
wasu ƴan iska sashe, ta san adadin abubuwan
dana ajiye masu muhimmanci a ciki? Ko
bamma ajiye komaiba ita bazatai tunani da
hankalinta rashin dacewar kai wani can ɗin”. “Inafa zata san abinda ya dace tunda a nuna
mata barbaɗa magani shine kawai zaman aure”.
A harzuƙe Gwaggo Halima ta dubi Mommy
mai maganar. “Nafi wlhy ki iya bakinki domin
zai kaiki ya baroki allura ta tono galma”.
“Yo ta tono mana dan ubanta, abu mai sauƙi

bayan ta tono ita galmar ta turbuɗata cikin
ƙansa yanda ko mayen ƙarfe ƙaryarsa sake
ganinta”.
Aifa nan take falon ya harmutse da hayaniya
tsakanin Mommy da Gwaggo Halima. Mamaki al’ajab sukabi suka sanya Share! cikin madaukakin imani. Yau kuma aminai biyune kema juna tujara haka akan abinda suke ganin shine mafi ƙololuwar alkairi a garesu idan suka ƙulla. Kai duniya ina zaki kaimu ne haka?. Da ƙyar su Daddy suka samu sukai shiru. Gwaggo kam tayi kamar bata a falon tai muƙutt da cuno baki gaba ita a dole takai maƙurar ɓacin ran abinda su Mommyn ke aikatawa. Acan ƙasan ranta kuwa dariya taketa kwasa. Yanzu kam Abba ne ya amshe da zancen yana mai fuskantar Fadwa.
“K shashashar inace da zaki bama ƙawaye damar shiga ɗakin mijinki? Haka kikaga iyayenki na mana? Wace irin mace ce ke da baki kishin mijinki? Ai wannan jama kanki rainine ma wajen su ƙawayen naki da shi kansa mijinkin. To saurara ki jini, daga rana mai kama irin tayau, hakan ta sake faruwa ni da kaina zan hukuntaki sannan shima nasa ya hukuntaki tunda koba aure tsakaninku
Yayanki ne.. Kinaji na da ƙyau?”.
Hawaye ta ta share tana jinjina kanta. “Zan

kiyaye Abba insha ALLAHU. Amma Abba dama fa haushina yakeji, dan dama a kwanakin nan banda wulakantani babu abinda yakeyi saboda ya ƙara aure. Baya ganin kowa a gidan sai ita ƴar gwal…..”
“Shiyyasa kuka dage boka da matsubbata ke
da uwarki domin sabautamin ɗa. Su Malika na
kawo miki barbaɗe-barbaɗe kina faman zuba
masa dare da rana. To wlhy babu lallai babu
dole tun kan ai nisa sai ya datse igiyar auren
tunda bake kaɗaice mace ba a duniya……” “Dan ALLAH Nafisa idan baki sakashi ya
datse igiyar aurensu ba baki cika uwarsa ba,
kuma shi din bai haifuba a cikinki…” “Haka kikace?”.
“Eh na faɗa. bandama ƙaddara mi Fadwa
zatai da wani Share! can. Ko dama kun ƙulla
a haɗasu aure dan ku dinga maidamin yarinya
baiwarku”.
“Hahaha yo baiwa kuma ta nawa Halima.
Sai dai wata kuma dan ita kam ta riga ta gama zama labari”.
Ƙara hargitsewa falon yay, da ƙyar yanzu kam Abie da Abba suka sakasu yin shiru, dan Daddy dai ya mugun shaƙa zuciyarsa har wani zallo takeyi, gata tokare a maƙoshinsa kamar yay amanta ya huta………….
End of book

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button