BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 71

A falo ya samesu su duka. Anaam na tsaye riƙe da cup na shayi idonta a tv tana murmushi. “Wato blood film ɗin nan fa zaiyi daɗi, sai dai guy ɗin film ɗin sam baimun ba shegen kunensa uwa na zomaye ALLAH”. Dariya Aysha ta sanya harda ƙyaƙyƙyawa tana leƙowa daga kitchen. “Amma wlhy kinci zarafin mutumin nan, ni banga wani kunen da kike masa sheri da su ba.”
“ALLAH da gaske yanada kunnuwa gasu nan, ga shegen rawan kai a wajensa uwa dangin makaɗan zamanin jahiliyya, ALLAH an cuceta da aka haɗata da shi”.
Alamar komawa yay ma Aysha data leƙo zatai magana, tai saurin komawa cikin bin umarninsa harda turo ƙofar kitchen ɗin dan ta tabbatar wata taɓarar za’ai. Rayuwar Yayansu na birgeta tun akan Fadwa, gashi dai mutum miskili da baya ɗaukar raini amma matansa nashan sharafin soyayyarsa. Cigaba yay da tsayawa a bakin ƙofar hannayensa harɗe da ƙirjinsa yana kallon Anaam ɗin kawai. Ita ko sam bata san da zamansa ba amma tanajin ƙamshin turarensa a hancinta wanda take ganin hakan normal ne tunda dama yana shigowa maybe tunna baya ne. Juyowa tai zata koma saman kujera suka kusa cin karo da shi dan ya baro ƙofar. Da sauri ta ɗanyi baya a zabure dan tsoroma ya bata. Cikin zafin nama ya riƙe cup ɗin shayin dake neman antayewa a jikinta.
Baki ta tura gaba da ƙwaɓe fuskarta da tasha kwalliya. “Kai Yaya ALLAH ka tsoratani”.
Idonsa akan lips ɗinta ya ɗage mata gira ɗaya, “Kin dai so ki tsorata madam”. Bakin ta ƙara tura masa tana ƙoƙarin janye jikinta. Hanata hakan yay ta hanyar riƙo ƙugunta, ya zuba mata mayun idanunsa cikin nata idon, tare da matso hanunta da nasa dake rike da kofin shayin yakai bakinsa. “Wayyo Yaya ni ALLAH zaka shanyemun tea ɗina”.
“K miyasa rowanki yayi yawa ne?”.

“To kai miyasa kwaɗayinka yay yawa ne”.
Murmushi yayi da kai yatsarsa ya ɗalle mata baki, “Magananniya da ba’a kadata. Sammin lipstick ɗin shima Please”.
“Tab ni ban saka da kai ba ni kaɗai zan shanye abuna”.
Dariyarsa ya danne da ƙyar, ya ɗan ƙwaɓe fuska da langaɓe kai gefe, “Babie Please mana”.
“Naƙi wayon”. Ta faɗa dayi masa gwalo tana tura lips ɗin cikin baki. “Ni kikama rashin m ko? Zan rama ALLAH”. Dariya ta ƙyalƙyale da shi da masa gwalo. “Kafin ka rama na ƙara wani rashin m ɗin ma”. Ta zille, riƙota yasoyi amma tai tsalle gefe tana masa gwalo. “Zan rama ne yarinya ai zaki zo hannu. Oya muje breakfast”..
Idanu ta ɗan waro, “Gashifa Aysha na mana anan”.
“Kin manta tsarina kenan”.
Shiru tai cikin ɗan tauke fuska. Dan ta ƙwallafa rai a abinda Ayshan keyi. Amma sai batai musu ba ta kaɗa masa kai. Tare suka fita, sun iske Fadwa na ƙara gyara dining ɗin. A yau ma babu wacce ta kalla ƴar uwarta a cikinsu. Dan haka ya duba kowacce fuskarsa a tsuke. “Kun gaisa da juna?”.
Shiru duk sukayi kowanne idonsa a ƙasa dan a serious yay maganar. Fadwa ce tai ƙoƙarin dannewa a shaƙe tace “Kin tashi lafiya?”. Baki Anaam ɗin ta taɓe da amsawa a shaƙen itama. “Alhmdllhi”. Komai bai sake ce musu ba, dan yasan a haka a haka watarana zai ci nasara. Wayarsa da yake latsawa ya ajiye, Fadwa ta fara haɗa masa abincin. A daidai nan Aysha ta shigo da ƙaramin tray. Wani irin ajiyar zuciya Anaam ta saki a hankali. Ya ɗan saci kalonta ta gefen ido sai yaji tausayinta. Ya fahimci tana son abinda Ayshan ke musu amma tabi umarninsa ta taho, shiyyasa yayma Aysha text yace ta kawo mata. Kasa ɓoye farin cikinta tayi har sai da ta kalla Aysha da murmushi. “Thanks you blood”. Murmushi Aysha ta mata. Itama sai ta sake murmusawa. Har Aysha ta juya zata fita Fadwa tace, “Ki dawo mu karya mana Aysha”.
“No Aunty gashi can na baro kar a barsa ya lalace shima”. Tai maganar tana nufar hanyar fita da ɗan hanzari dan karma Shareff ya tsaidata. Batama san shi baida niyyar tanka musu ba. Abincinsa yake ƙoƙarin fara ci kawai…………✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button