DANGI DAYA HAUSA NOVEL
❣️DANGI ‘DAYA❣️
{Romance & Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Marubuciyar:
DANA SANI
{Ahmad & Feenah}
BURINAH
{Amal & Daddy}
WAZAN ZABA?
{Iman & Aliyu}
SHALELAN BABA
{Haneef & Haneefa}
NI DA KE
{Mk & Baby}
And now!
????
DANGI ‘DAYA
Bissmillahir-rahmanirraheem
Ina qara godia ga Allah daya bani damar rubuta wannan littafi, ya Allah ka haneni rubuta abinda yake sharri ne da kuma abinda bai kamata ba, Allah kabamu ikon yin amfani da abinda yake Mai kyau ne, kasa muyi watsi da marar kyau.
Littafin DANGI DAYA qirqirarran labari ne, saide ina fatan idan yayi daidai da Rayuwar ki wadda kika tsinci kanki aciki yanzu kisamu solution acikin wannan littafin.
Idan labarin DANGI DAYA yayi miki dad’i inaso duk lokacin dakika tuna Dani kiyimin Addu’ah.
Daga qarshe, duk wani masoyin Amnah El Yaqoub, na sadaukar da wannan page din agareshi????.
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/
1&2
“NIHLA! lokacin tafiyar ki makaranta fa yayi, kitashi haka kada ki makara”
Cikin jin dadin baccin tayi juyi tabawa wadda take yimata magana baya,hakan yabawa dogon gashin kanta Wanda duk ya cukurkude damar rufe mata fuska, cikin magagin bacci tace “Diddi Allah ni baccin bai isheniba”
Dan qaramin tsaki taja, tasa hannu tadauketa cancak, bata ajiyeta ako’inaba sai afilin Dan qaramin tsakar gidansu na qasa Wanda yake ashare tas
Tsugunnawa tayi daidai Tsawon yarinyar tace “dan ubanki bude idonki, idan kika makara dukanki zasuyi “
Jin maganar duka yasa ta wartsake lokaci daya, ganin tatashi sarai yasa mahaifiyarta rabuwa da ita, takoma cikin dakin tad’auko mata d’an qaramin brush dinta, tabata, sannan tadauki baho tafara hada Ruwan Mai d’an d’umi.
Ruwan wankan data hada tad’auko takawoshi gaban yarinyar, sannan tadauko kwandon wanka Wanda yake d’aukeda soson wanka Mai laushi, da alama na yarinyar ne, ta tsugunna a gabanta “wai bazaki hanzarta kigama wanke bakin ba?”
Cikin sauri yarinyar ta wanke bakinta, ta ajiye brush din akan wata yaluwar jarka ta OKEY wadda take cikeda ruwa, bakin ma bai wani fita sosai ba, haka tahaqura tace “Diddi nagama, afara wankan”
Hannunta tasa ta tattare gashin kan yarinyar, Wanda yakeda tsawo sosai, cikar batada yawa, ta d’aureshi waje d’aya, sannan tafara yimata wankan
Idanunta a runtse tace” Diddi baza’a wanke kanba? “
“Nihla idan aka wanke wannan kan naki shi kad’ai ma zaisa ki makara kafin ya bushe, kibari idan za’a miki wanka da yamma saiki siyo omo awanke miki”
Tace “to Diddi”
Tsaf tagama yiwa yarinyar wankan anan filin tsakar gidan nasu sannan tasata tayi alwala , kasancewar akwai rairayi kad’an agidan hakan yasa qasar wajan ta shanye Ruwan, lokaci d’aya farar fatar yarinyar tasake futowa, wani zanin atamfa taja akan igiyar tsakar gidan nasu, tarufa a jikinta sannan tashige d’akinsu da gudu.
Itama bayan yarinyar tabi zuwa d’aki, ta goge mata jikinta, sannan tashafa mata Mai Vaseline na Habiba, tasa ta tafara sallah, dukda yarinya ce qarama, tayi kokari wajan yin sallar saide gyara ‘yan kad’an
Hijabin datayi sallar dashi tacire, tad’auki mataji tabawa mamanta tace”Diddi gashi “
Batare da tace komai ba ta karbi matajin, tafara tajewa yarinyar gashin kanta, me mugun tsawo sosai, tad’aure matashi da ribom sannan tatufke mata sauran, zanin atamfar data goge mata jikinta dashi tad’auka ta goge mata fuskarta, saboda maiqo, sannan tasaka mata d’an qaramin hijabinta fari me hula, kasancewar hijabin d’an qarami ne hakan yabawa jelar gashinta damar futowa ta qasan hijabin, takalmin ta tasaka silifas, sannan tace “Diddi natafi”
“to Muje wajan babanki kikarbi kud’in karyawa”
Wani d’aki suka shiga Wanda yake kusada Wanda suka shirya, tana tsaye abakin kofar d’akin ta doka sallama, radion dayakeji yarage sautinta, sannan ya amsa mata, ko ina kwana Babu tace masa “Baba kudin karyawa”
Murmushi yayi, yadauki nera goma acikin aljihun rigarsa yabata, takarba tafuto, ta kalli Diddi dake tsaye abarandar gidan nasu tace “Diddi natafi”
“to Nihla saikin dawo, banda wasa ahanya kinji ko”
“to Diddi, idan anyi tara nataho gida ko?”
“Haba Nihla, mezakiyi idan kinzo?ba ana baku abinci a makaranta ba? Kiyi zamanki sai antashi, nisan ai yayi yawa”
Cikin shagwaba tace “to Diddi idan basu bamu bafa?”
“tome amfanin nera goman da aka baki? Saiki siya wani abun kici”
Tace “to natafi”
Itama tace “to Allah yakiyaye, banda wasa de kinji ko”
Tace “to” tareda ficewa daga gidan
Ita kuma Diddi tad’auki albasa yan madaidaita guda uku tafara Yankawa, amma abin mamakin shine hancinta yana gab da albasar datake Yankawa tana shaqar yajin albasar Kamar batajin zafi
Kamar kullum tana futowa daga gida adede lokacin shima megadin gidansu ya wangale musu get, kallo d’aya tayiwa motar qirar Mercedes Benz tadauke kanta, ta gabanta motar tazo tawuce, tana d’ago kanta taganshi shi kad’ai a bayan motar ana jansa, shima uniform ne ajikinsa amma ba irin nataba, da alama na private school ne nasa, cikin sauri yajuyo ta glass din bayan motar yafara d’aga mata hannu yanayi mata bye-bye,sarai taganshi, amma taqi yimasa bye-bye din, sai murmushi datayi masa har dimple d’inta suka futo gaba d’aya biyun
Juyawa yayi yadena Kallanta, yabude school bag dinsa yayi rubutu ya cukwikwiye yasaukar da glass din gefensa, ya wulla mata takardar, sannan Yarufe glass din yana daria, baisake Kallanta ba
Itama tana kallan motarsu, har sukai mata nisa, takardar dataga ya wullo mata tad’auka, ahankali ta bude takardar “You’re my friend”
Shine abinda tagani ajiki, bata fahimci komai ba, Dan haka tayagata ta watsar awajan ????
Taci gaba da tafiya tana ball da duk abinda tagani agabanta
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
“Abubakar”
“na’am Hajiya”
Wata takarda tabashi doguwa alinke, sannan tasake kallansa tace “riqe wannan takardar”
Karba yayi yariqe fuskarsa cikeda mamaki, bai iya boye mamakinsa ba yadubeta yana qoqarin bude takardar “Hajiya wannan takardar mecece?”
Cikin sauri tace masa “karka kuskura kabud’e wannan takardar Abubakar, abinda yake cikin ta Sirri ne tsakanin nida mahaifinka da mahaifiyar ka wato abokiyar zamana”
Kallanta yasakeyi sosai”to Hajiya meza’ai da’ita? “
” yauwa Tun farko abinda yakamata ka tambayeni kenan, Abubakar wannan takardar wasiyya ce da mahaifinka yabari ahannun mahaifiyarka Tun kafin yabar duniya, ita kuma tad’auka tabani kafin itama Allah yayi mata rasuwa, ni kaina inaji ajikina ba lalle naqara shekara d’ayaba nan gaba, shiyasa nima na damqa maka wannan wasiyyar ahannunka amatsayin ka na babba acikin MAZAWAJE FAMILY,”
” haba hajiya, meyasa zaki dinga yimin irin wannan maganar? Ke kad’ai ce kika rage mana, sannan ke kad’ai muke gani muji dadi, kinasa jikina yanayin sanyi sosai “
” Kayya, Abubakar kenan, shekara tamanin da biyu ba nan bace Abubakar, gara inyi abinda yakamata Tun kafin lokaci ya quremin, mutuwa bata sallama “
Shiru yayi, kansa a sunkuye, maganar hajiya tasa jikinsa yayi mugun sanyi, bata taba nuna masa banbanci da ‘ya’yanta ba duk da ba’itace ta haifeshi ba, kishiyar mahaifiyarsa ce, idan itama tatafi tabarsu yaya zasuyi? ????
lokaci d’aya Idanunsa yakad’a yayi jajir, yadago yadubeta “Hajiya yanzu yaya zanyi da wannan takardar?”