BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 72

       Sai da suka kammala Gwaggo da Mommy suka dubi Shareff ɗin cikin komawa serious da ƙyau. Hakan daya ganine ya sashi nutsuwar shima ya maida hankalinsa garesu.
    Gwaggo ce ta fara magana. “Mustapha abubuwa da yawa sun faru waɗanda basai mun zauna lissafi akansu ba ko sake maimaita batunsu anan gurin. Sai dai waɗanda suke faruwa a yanzu sune abun dubawa. Kayi haƙuri munyi kuskuren tilasta maka auren Fadwa ba’a san ranka ba, sai dai mu munyune domin ƙarfafa zumincin ALLAH. Amma ashe zuciyar uwarta cike take da tsatsa. Tunda har a matsayinka na ɗan ɗan uwanta zata iya neman asiri taba ƴarta ta zuba amaka a abinci ko abinsha ya tabbata zata iya kasheka wataran domin farin cikin ƴar tata. Mudai bazamuce dole sai ka saki Fadwa ba. Amma ka zauna kayi tunani mizai iya zuwa ya dawo nan gaba. Dan hatta cikin datai ɓari kwanaki mun fara zargin yarinyar nan zubar da shi tai tana akan sani”.
A matuƙar razane Mommy da Shareff suka dubi Gwaggo. Har Mommy ta kasa haƙuri….
“Gwaggo miyasa zakice haka a ina kikaji wannan maganar kuma?”.
Baki Gwaggon ta taɓe, “Yo Nafi abin duniya na ɓuya ne, kawai nayi shiru ne ban faɗa mikiba. Amma a jiyyarta da nai asibiti na karanci abubuwa da yawa game da yarinyar wlhy. Sai dai ban tabbatar ita ɗin ta zubarba. Amma Mustapha kaje kayi bincike harka tabbatar da gaskiya. Sai dai kayi komai a sirrance basai ka faɗa mataba a yanzu dan karta toshe duk wat hanyar gaskiyarka. Abu na gaba akan aurenka na biyu ne, mudai ba son auren nan muke ba sam, amma munga kai kamar kana so. Dan haka mun yanke shawarar barinka da matarka ku zauna. Sai dai da sharaɗin zaka ƙara aure. Kuma munma zaɓa maka wadda zaka aura yarinyar kirki da tasan mutuncin kanta, idan ƙyau ne kuma duka matan naka ta fisu. Mun tabbatar zakaji daɗin zama da ita insha ALLAHU duk wani ƙuncinka zata ƙwaranye akan waɗan nan ƴan iskan yaran”.
Sosai ya tsurama Gwaggo ido ko ƙyaftawa bayayi, babu abinda zuciyarsa keyi sai luguden daka. Ya haɗiye yawu da ƙyar. Harshensa na rawa yace, “Aure kuma gwaggo?”.
Mommy ta amshe da “Eh aure Babana. Shine zai baka kwanciyar hankali muma kuma ya bamu, dan nidai kasan matarka ta biyu ba zan taɓa sonta ba, amma na haƙura in har kabi umarni na a yanzuma zan barka da ita. Idan kuma ka bijire su duka biyun zaka sakesu ka ƙara auren kuma koda bada zaɓina ba. Dan wlhy itama Fadwa ta fitamin arai. Ko kaunar jin sunan yarinyar nan banayi yanzu. Kuma ina nan saina tabbatar da nunama uwarta kai ɗin jinane ni na haifi abuna kuma. Dan haka kaje kayi shawara daga kwana daya har sati guda muna jiranka. Duk abinda ka yanke sai mu sani.”
“Amma First love……”
“Bana son jin komai Shareff. Kaje kawai kayi tunani kafin ka yanke hukunci, yarinyar da muke so ka aura itace Bibah ɗiyar Luba na san dai ka santa”…………✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button