BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 72

72

………Abincin yakeci cike da nazarin kowaccensu. Fadwa nayin komaine a taka tsantsan na gudun yin kuskure fatanta komai ya wuce. Yayinda Anaam ke komanta kai tsaye hankalinta kacokan naga abincin da takeci tamkar ta manta da zaman kowannensu a wajen ma. A haka dai suka kammala Fadwa ta fara gyara wajen, dakatar da ita yay dan haka ta koma ta zauna. Anaam data ɗauka waya yayma magana, itama ta ajiye suka bashi hankalinsu. Nasiha ya fara musu a nutse tare da jan gargaɗi. Daga ƙarshe cikin kaushin murya da tabbatarwa ya ɗan bubbuga table ɗin da yatsansa.
       “Bazan lalace wajen zargi akan ku balle ƙin cin duk abinda kuka bani ba, sai dai zan tabbatar muku, duk wadda ta zuba wani abu koda a ruwan sha ɗinane domin samun wani cikar burinta ban yafe mata ba. Kuma idan na kamata bazan yafe mataba ko iya cigaba da zama da ita duk da babu tsarin rabuwa da ɗayanku a zuciyata. Shawara ya rage naku, kumu haɗu mu zauna don ALLAH cikin soyayya da mutunta juna, ko kuma kowa ya ɗauka layin da yaga zai dace da shi a shirye nake wajen maganin duk wadda take tunanin zata iya fin ƙarfi na. Na ƙarshe respecting juna da kuma iyayenmu. Wlhy idan wata a cikinku ta sake kuskuren yin abinda bai dace ba akan wani ko wata a cikin iyayrenmu sai na sakata nadama ta har abada, ya rage naku ku dawo hankalinku kokuma ku ɗaura daga inda kuka tsaya”.
       Har ƙasan zuciya kausasan gargaɗinsa sun shigesu, sai dai sunfi ratsa Fadwa musamman akan zuba masa magani a abinci fiye da Anaam da wannan gaɓar bama komai ta fahinta ba. Amma dangane da girmama iyayensu da juna ya shigeta matuƙa, dan yanayinsa ya tabbatar musu zai iya komai. Bayan ya sallamesu kowacce ta nufi ɓangarenta tana ƙullawa da kwancewa. Shima fita yay a gidan zuwa can gidansu gaida su Mommy tunda yanzu Daddy ya janye masa sharaɗin hana zuwa gidan. Sai dai koda yaje ya samu Mommy da Gwaggo basa nan. Bai so haka ba, dan yazone takanas ya lallashi mommy ɗin da bata haƙuri akan komai ma daya faru, sannan ya yini da ita yau. Gidan su Anaam ma ya iske Mamie da aunty Mimi sun fita, dole dai ya koma gida dan gwara yaje ya huta kawai shima.

      A ɓangaren Mommy da Gwaggo gidajen su aunty Malika sukaje sukai musu tatas, inda akai hargitsi bana wasa ba har saida takai an gurfana a kotun baba Ibrahim. Shima al’amarin ya ɓata masa rai, dan yajima dajin tsiyatakun da su Malikar keyi a gidajen aurensu. Sai gashi yau suna neman saka Fadwa itama kuma abin takaicin harda haɗin kan mahaifiyarta. Sosai yayima Gwaggo Halima dake matsayin matar ɗan uwansa faɗa, ya nuna mata kuskurenta na son ɗaura ɗiyarta akan bigiren da zai rusa rayuwarta a dunuya da lahira. Suma kuma su Mommy yay musu nasu faɗan, dan tun farko da basu nunama Fadwa komai tayi a gidan aurenta dai-dai bane daba haka ba. Yanzu gashi sun ɗanɗana mata tana niyyar zartasu kuma sun shiga damuwa, ta riga kuma ta ɗanɗana ba lallai abin ya iya barinta ta sauƙi ba.
       Nasihar Baba Ibrahim bata canja komai a jin haushin juna da Mommy da Gwaggo Halima keyi ba. Sai ma ƙara jin zafin juna dan kowacce nada sirrin ƴar uwarta a tafin hannu. Kuma kowacce taci alwashin nunama ƴar uwarta fawa ɗinta akan ƴaƴan nasu da kuma mazajensu da suke amsa yayanninsu. Da haka aka sake rabuwa baran-baran…..


          Ga Shareff kam tun yana shashshare Fadwa harya dai ya sakko, mata da miji sai ALLAH. Sai gasu kamar komai bai faruba aka koma faranta ran juna, dan aranar ba ƙaramin rikita Soulmate ɗin nata tai ba, har yaji a karan kasa ta cancanci yafiya. Sai dai tsananin kishin mijinta na nan a zuciyarta. A duk sanda ta tuna akwai wata a yanzu bayan ita tare da shi takanji raɗaɗi mai zafi a zuciyarta. Sai dai ta ɗauka alƙawarin daina biyema su Aunty Safarah, bazata ƙara amfani da wani magani ba insha ALLAHU. Zata tsaya da ƙafafunta wajen kishin mijinta da ƙyautata masa kowacce ta ƙwaci kanta kawai. Dan tayi imani bazata taɓa son Anaam ba a zuciyarta, saboda tunda ta tashi a rayuwa da tsanar iyayenta da ita kanta ta rayu.
      A ɓangaren Anaam ɗin itama sosai take jin kishin mijin nata, dan akwana biyun nan da yake tare da watanta ba itaba tana matuƙar jin raɗaɗi da zafi. Abinda ya sauƙaƙa mata kawai zaman Aysha tare da ita. Amma ko shigowa yay wajensu sai tayi matuƙar dauriya take iya kallonsa har ta sakar masa murmushi. Banbancinsu da Fadwa kawai ita bata zafafa ba. Bata son Fadwa tun fil’azal saboda tunda ta mallaki hankalinta tasan Gwaggo Halima da su Fadwa basa son  iyayenta basa respecting nasu kamar su Daddy. Amma batajin tsananin tsanarta dan ita bata zafafama kanta abu, kawai idan ya ɓata mata rai ta nuna fushintane take anan da kwakwazo a wuce wajen. Daga haka kuma ta watsar zata fuskanci nagaba mai wucewane. Tadai ɗauka alwashin ƙyautatama mijinta da basa tarin tukuycin soyayyar daya jima yana mata tun bata san kanta ba. Duk wuya bazata yarda ta bijirema umarninsa ba ko cutar da Fadwa. Amma zata ƙwaci kanta akowane hali idan akai yunƙurin cutar da ita.

      Lahadi da yamma mijinta ya dawo hanunta, ya gama kwanakinsa a wajen Fadwa. Da taimakon Aysha suka haɗa abincin dare na gaba daya kamar yanda ya sharɗanta. Ta nufi sashensa domin gyarawa Aysha kuma ta gyara mata nata duk da ma babu wani datti mai yawa kasancewar babu yara ba kuma wasu jama’a ne da yawa ke shiga da fita ba. Duk kaiwa da kawowar da Anaam keyi a sashen Shareff a idon Fadwa ne dake leƙe ta window ɗin falonta. Kai tsaye tasan wannan rawar jikin na Anaam wai za’a tarba miji ba basirarta bace Aysha ce. Tai ƙwafa da cije lips, a ranta tana ayyana yarinya ni dake mu zuba a nan gidan. Oho bama tasan tanaiba, dan koda ta kammala rufo sashen tai harda saka key saboda ya bama kowacce key. Batare data ko lura da Fadwa ba ta nufi sashenta dan ta samu tai wanka tunda tasan a koda yaushe zai iya dawowa gidan tunda ba aiki ya fitaba. Yaje can gidane Mommy ta kirashi duk da a cikinsu babu wadda tasan da hakan. Yadai ce musu zai fita kawai. 

        ★Ransa fes ya iso gidan domin jiya ma yazo ya gaishesu kuma shida Mommy babu wata damuwa. dan koda ya bata haƙuri akan duk abinda ya faru tace masa komai ya wuce a gareta kawai. Yaso yaji kamar ba haka bane a ransa, amma saita kore masa dukkan tantama ta hanyar sakin jiki da shi sukai hira da suka jima basuyi irinta ba. Kuma abin mamaki ko sau ɗaya bata kawo maganar Anaam ba ko abinda ya shafi aurenta. Hakama Fadwa. Sun tattaunane kawai akan auren Aysha da kuma komawar Maheer wajen aiki a yau.
     Sai da ya shiga dukkan sashen mutanen gidan ya gaida kowa sannan ya nufi sashen Mommy a ƙarshe. Tana falonta zaune Hussaina na haɗa mata ƙwaɗon zogale ya shigo. Fuskarta da murmushi ta amsa masa sallamarsa. Ya kai zaune shima fuskar tasa da murmushi.
      “First love daɗi zakici haka?”.
Murmushi tayi mai nuna haƙora. “Ai gaka kaima kazo sai muci tare ko?”.
    “Harma na fiki lauma”.
Dariya tayi daga ita har Hussaina dake yin tata a ƙumshe. Ya gaida Mommyn, Hussaina ma ta gaishesa sannan tabar falon bayan ta kawo masa ruwa. A kwano ɗaya sukaci zogalan da Mommy cike da nishaɗi. Suna tsaka da cinne Gwaggo ta shigo.
          “Ja’iri kazo zaka cinye mata ɗan zogalan bayan acan na baka kaƙi ci”.
  Murmushi yay da taɓe baki, “Naki kin saka ƙuli ne itako gyaɗa ta saka shiyyasa”.
    “Oh, da gyaɗar da ƙulin duk ba abu ɗaya bane?”.
    “A wajena ni dai da banbanci”.
Mommy dai dariya take musu kawai.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button