AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 35-36

Ranar sunyi chatn sosae da Afham ana shirin yin sallar magrib yasauka yace itama taje tayi sallah, amma taji har akayi sallar magrib tana zaune, sai bayan angama sannan tatashi tayi sallar, bayan tagama tana tatashi tadauki wayarta tasaka chaji amma ta gagara ajiye wayar sai duban DP din frds dinta take har lokacin da hilal ya dawo babu Abnda Ameelah tayi, sai da taji tsayuwan motarshi ta ajiye wayan da sauri ta fara gyaran dakin…

Da leda ya shigo a hannushi ta amsa ta mishi sannu da zuwa ya qarema dakin kallo yanda ya barshi haka ya iskeshi, tana shafar kai tace “tunda ka tafi nake bacci ban samu nayi komai ba gidan!

Hilal yiyi murmushi
Yace “ay kara ki dinga hutawa, bari in fito in tayaki shara! Tayi murmushinta ya shge bedroom dinshi shima babu abnda ta gyara, haka ya shga toilet watsa ruwah shima ko wanki babu (sis rabi’at itama datake macce saida tace wannan wane irin jarabar chatn ne? Wasu matan zasuyi chatn bzasu gyara gdansu ba, babu ruwansu da tsaftar yaransu ko girkin mai gida! Sun gwammace su hau chatn suna cin Amanar aure, ko kuma chatn da qawayensu yaafi musu, nace “gsky ne ba duka matan ke da wannan tunanin ba)

Cikin sauri tashiga gyara gidan kafin ya fito, bayan yafito yazo yatayata suna aikin suna fira babu jimawa suka gama, ana kiran salar isha, hilal yafita yaje masallaci,

Yana fita, kamar tana jira, dasauri takoma gurin wayarta, daman datarta abude take, sakon ni taga sunshigo da yawa, harda wata bakuwar number, ta tsaya tana kallon number, number kamar bata Nigeria ba, saidai kuma hello kawai akace acikin number, saida ameelah takarewa number kallo sannan tafito, lambar hmm tagani ya auko mata sako, tayi sauri tashiga taduba, yace “beauty nayi miss din kalamanki dan Allah muhadu shabiyun dare akwai wani kyankyawan albishir dazan miki, plx kihau karki cemun kin manta saimun hadu” tayi ajiyar zuciya, kafin tafara zancen zuci “yanzu yazaayi muhadu, inason naji albishirin nan nasa” saikuma ta kada kai tace yes natuna,(na kalli rabi at nace “sis mekuma ameelah ta tuna “, tace “oho.. Musa ido mugani” nace “tomh)

Tana zaune tatuna da sallah dasauri tatashi tanufi bandaki bayan tafito tafara sallah, kamar wadda aka saka yin dole shaf shaf takarasa, tatashi ta nade sallayar sannan tafara shirin bacci kafin hilal yadawo,

Bayan ta kammala shirinta tafesa turare, sannan takoma kan gado ta kwanta, tanajiran dawowar hilal,

Kusan mintinta ashirin a kwance tana jiran dawowarsa, jitayi anturo kofar dakin, tunkafin yakarsa shigowa tayi saurin gyara kwancinta, sannan tarufe ido, tafara jan minshari…..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button