BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 75

75

……..Rungume yake da ita yana sanya mata albarka bayan samun nutsuwarsu. “Noorie na wai miye sirrinne?. Kwana biyun nan fa kin ƙara zama mai tsadar tsada ta gasken gaske. ALLAH gigitani kike na manta da kaina gaba ɗaya. Ni’imomi sun ƙara cika garden ɗina”.
Kunya ta sakata tura kanta a ƙirjinsa tana murmushi. “Kai Yaya ko kunya bakaji?”.
“Kunyar mi zanji ina a gaban autar mata. Idan ban faɗa miki abinda ke raina game da ƙyautarki da ALLAH ya bani ba mi zanyi tauraruwa a cikin taurari?”. Ya ƙare maganar da manna mata kiss a gefen kunne. Tsam ta ƙara matsesa a cikin jikinta. Ƙaunarsa ta musamman na sake ratsa zuciya da ɓargonta. A duk sanda take tare da shi mantawa take da kowa da komai, bata tuna bayan ita akwai watanta. Farin ciki take bashi fiye da hasashen zuciya. Kamar yanda shima yake riritata tamkar ƙwai a cokali. Ya gama ɗorata da koya mata salo-salo na rayuwa dakan ƙara raunana rauninta taji koda agaban wanene batajin shakkar nunasa matsayin Jan-gwarzonta….
Sumbatar goshinta yay cikin katse mata tunani, ya ɗagota suna mai kallon juna a tsakiyar ido. “Anya bani da ajiyar baby a wajen nan Noorie?”.
Idanu ta waro sosai a kansa. Ya dage mata gira daya da ƙyafta idanun yana murmushi. “Am serious kin canja Juwairiyya. Jiba nan ya ƙara girma. Baƙya raki kamar da, saima so cikin zalama. Garden ya ƙara zama zakwai-zaƙwai”.
Doke masa hannu tai da ƙoƙarin juya baya ya riƙota. “Shike nan, shike nan na daina magana. Yanzu dai na haƙura Ki shirya kije kawai, bazan hanaki zuwa bikin ƙawarki ba”.
“Woow dan ALLAH da gaske My hero?”.
“Yes my Heartbeat”.
Wani irin ɗan ihun farin ciki tayi, tare manne lips ɗinsu waje guda. Cikin ƙanƙanin lokaci ta susuta masa lisaafi…..

(????????????jaraba).

  ★Shi da kansa ya kaita, bayan yayima Fadwa magana ta shirya itama taje ɗin har sai biki ya tashi tace a'a. Bai matsanta mataba ya ƙyaleta, dan shima dai yana buƙatar ɗaya ta zauna tare da shi kar a maidashi gwauro.
 Sosai Anaam ta tsinta kanta cikin farin cikin ganinta tare dasu Abie ɗinta. Nan fa sabuwar shagwaɓa ta tashi. Suko suna biye mata dan farin cikine baibaye da zukatansu. A ranar akai ƙunshi, sai dai tana nane da su Mamie bata shiga cikin gida ba. Washe gari kamu ta tashi duk batajin daɗin jikinta tun safe. Amma sai ta danganta hakan da kewar Shareff dake damunta. Tun wajen sha biyu ta shige cikin gida, kasancewar sashen Mom dana Mommy duk cike yake da baƙi saita nufi sashen aunty Amarya dan su Aysha nacan da gayyar ƙawayenta. Tuni ta shige cikinsu anata shan shafta har akai mata ƙunshi da Aysha ta matsa. Tun ana lallin take complain ayi maza a gama kanta ciwo yake, Aysha na hararar ta wai ƙunshinne bataso, in ma an gama anjima kaɗan tare zasuje Saloon ko taƙi ko taso. 
 Kamar wasa tace musu jiri takeji, kuma tana ganin hayaniyar gidance, Aysha dai taita lallaɓata ta shige bedroom ɗin aunty Amarya ta kwanta. Sai da ƙawayen amarya suka gama shiri suka fita tsakar gida Aunty Rahma ta shigo ta gata ita da Aunty Bintu. Sune suka sakata tashi dole tai wanka. Amrah ta kawo mata kayanta ta shirya anan. Jin yanzu babu jirin saita fito tsakar gida inda kamu ke gudana. Dan ƙarfin hali harda shiga fili taima amarya liki. Masu kiɗan kwarya suka shiga koɗata da kirarin Amaryar babban yaya Shareff. Ana haka Khaleel ya shigo shi da Shareff da Maheer. Anaam ta nufesu tana murmushi ta farama Khaleel ɗin liƙi. Hakan yasa aka dawo aka baibayesu masu kiɗan ƙwarya na cigaba da kwarzantata. Shareff dake kallonta yana murmushi baima san ya zaro nasa ƴan kudaɗen ba ya fara liƙeta, hakan yasa shima Maheer zarowa yana musu liƙin su duka uku. Aifa sai waje ya ɗauka ihu, dangi aka zagayesu su duka huɗun ana musu liƙi. Tun Anaam najin hayaniyar sama-sama harta fara jinta nesa-nesa. Idanunta suka fara limshewa tai baya zata sulale Shareff daya farga yay saurin tarota jikinsa. A take waje ya ɗau shiru. Da sauri Aunty Bintu ta kawo ruwa aka shafama Anaam ɗin saita kawo nannauyan numfashi. Kanta ta riƙe hawaye na ziraro mata. “Yaya kaina, kaina zai fashe Yaya”.
 Hankali tashe ya sungumeta akai sashen aunty Amarya da ita, dan nan ɗinne kawai keda karacin mutane, dama ƙawayen amaryane sai danginta tsiraru kasancewar ba ƴar kano bace, kuma duk sun fito. Maheer ne yay kiran Dr Jamal. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya iso, har yanzu Anaam na'a jikin Shareff tana masa kukan kanta. Yana riƙe da kan yana mata addu'a, su aunty Amarya zagaye da su. Dan hatta Mom da Aunty Mimi duk suna a wajen. Tuni kuma an kaima Mommy da Gwaggo rahoto sai dai basu fitoba. Mamie ma nacan cikin damuwa a tsakar gida amma dattakonta ya hanata shigowa taga halin da Anaam ɗin ke'a ciki. Su Daddy dai suna can gidan su Anaam din tare da Abie dan can ɗin babu mutane sosai duk anyo nan cikin gida.
   A kallo ɗaya Dr Jamal ya fahimci matsalar Anaam ɗin, dan haka ya kalli Shareff cikin ido. Hararsa yayi yana motsa laɓɓansa ahankali alamar magana yayi sai dai bata fitoba kasancewar falon cike yake da su Mom. Jininta ya ɗiba ya kuma bata maganin ciwon kan kawai. “Inaga zanje ai text first, amma dai tasha maganin sai taje inda babu wannan hayaniyar ta kwanta ta huta. Inba hakaba ciwon kan zai cigaba da damunta. Zuwa da safe insha ALLAHU zan kawo sakamakon ”.
   “Kana nufin wannan maganin kawai zaka bata ka barmin mata cikin ciwo kenan?”.

Shareff ya faɗa cikin suɓutar baki dan ya ma manta da su aunty Mimi dake wajen. Babu wanda baiyi murmushi ba, ƙanensa na gulmarsa a zuciya ina miskilancin nasa yaje. Sai dai babu mai damar cewa komai. Maheer kam jikinsa ne yay sanyi, ya dubi matarsa da sam tama ƙi sakewa a gidan saboda a wajensa ma bata samu farin ciki ba. Auren watanni huɗu ya kasa sakin ransa ko kusantarta yaƙi yi, ita kuma ta tura masa aniyarsa duk abinda ya dace mace ta gari taiwa miji bata gazaba tana masa gwargwadon iyawarta.
Yanzun ma ko kunya babu shine ya kaita can gidansu dan acanne kawai akeda ƙarancin hayaniya. Kai tsaye sama ya kaita ɗakin Mamie ya kwantar a kan gado, yana daga zaune kanta bisa cinyarsa yana tofa mata addu’a a kanta aunty Mimi ta shigo ɗauke da ƙaramar roba da towel ƙarami a ciki. Shine ya amsa, tai murmushi a ranta tana faɗin, (Ƴan banzan yara dakun cigaba da pretending da rabo ya kashe har mu bama ku kaɗai ba. Dan wannan daga gani ciki ne). A zahiri kam juyawa tai tayi ficewrta ta bar musu ɗakin. Towel ɗin ya dinga matsewa a cikin ruwan yana goga mata a goshi zuwa fuska har wuyanta da hannayenta. Sai da kanta dake zafi ɗau ya huce sosai sannan ya koma kafafunta. cikin ƙanƙanin lokaci sai ga barci ya ɗauketa. Ya sauke ajiyar zuciya da komawa gefen gadon ya tsugunna saitin fuskarta. Kallonta yake da murmushi, ƙaunarta na ƙara ratsashi. Ya kai lips ɗinsa kan nata ya sumbata, hakama idanunta dake lumshe. Har cikin ransa yana fatan hasashensa ya zama gaskiya. Addu’a daya jima yanayi ta samun rabo daga kowaccensu ta tabbata a wannan karon. Dan ko kwana biyu ba’ai ba da gama yima Fadwa ƙorafi akan hakan.
Shigowar Mamie data kasa haƙuri ce ta sashi mikewa yana shafar ƙeya. Haka kawai yanzu yake jin tsananin kunyarsu ita da Abie babu gaira babu sabar. Cikin sanɗa da dabara ya zare jikinsa ya gudu a ɗakin…..

   Su Daddy ma sun shigo dubata bayan sallar isha'i, har sannan kuma bata tashi ba tanata barci. Sun mata addu'ar samun lafiya suka fice. Sai da Abie ya rakatane ya dawo domin sake duba tilon ƴar tasa. Yana a ɗakin Shareff ya dawo, ji yay duk ya daburce, dan haka yaki sakewa ya gudu, duk da Abie nace masa ya dawo shi fitama zaiyi amma yaƙi tsayawa wai dama yazo ya sake dubatane zai wuce gida goma tayi.....

WASHE GARI al’ummar wannan family suka tashi da farin cikin bayyanar cikin Anaam ɗan watanni biyu da wasu kwanaki da adadinsu baida yawa na cika watanni uku. Zokaga murna wajen su Mamie da su Daddy. ALLAH mai alheri, su sunsha kuka da damuwar rashin samun haihuwa da wuri ga Anaam da bata rufa watanni huɗu ciff ba da ciki. Wannan rahama ce ta UBANGIJI mai yin yanda yaso a lokacin da yaso. Isar wannan al’amari kunen Gwaggo da Mommy tamkar saukar aradune a tsakiyar dare mai duhuwa. Dama dama ma Mommy bataji zuciyarta ta zafafa ba a wannan karon har hakan ya bata mamaki. Amma Gwaggo gaba ɗaya birkicewa tayi har bakinta ya dinga subucewa wajen sakin wasu maganganu. Koda ta kira Mommy gefe kan hakan sai Mommyn ta nuna mata ita duk da bata son Anaam da su Abie taji son cikin dan koba komai gudan jinin Shareff ne ai. Wannan furuci ya matuƙar ƙona zuciyar Gwaggo. Dan haka ta ɗau alwashin sai ta ɓata taron bikin nan. Cikin halin ko’in kula Mommy tai komawarta cikin danginta ta cigaba da hidimarta. Gwaggo ta bita da kallo zuciyarta na suya matuƙa, ita Nafisa zataima wannan ɗibar albarkar, to ai idan tasan wata bata san wataba wlhy. Barin wajen tai fuuu kamar zataci tun tuɓe zuwa sashenta tana ƙulla wutar da zata kunno a gobe idan ALLAH ya kaimu.
Bayyanar cikin Anaam ta matuƙar tada hankalin Fadwa, musamman dataga kamar dai nata Shareff bai wani zumuɗi ba ko rawan kai a zahiri. Amma kuma yanayinsa na son nuna kulawa ga Anaam ya tabbatar mata nunawarsa a fili bashi ke nufin baya son haihuwaba. Kawai dai hakan naturally ɗin halayyarsace ɓoye sirrin zuciya. Ba ita kaɗaiba hatta Gwaggo Halima maganar cikin nan ya tada mata hankali. A karon farko sai gata gidan Shareff ɗin dan bata taɓa zuwa ba. Cikin shirin tafiya gidan biki take, dan acewarta zataje bikin Khaleel ne bana Aysha ba, dan ita da Mommy a yanzu babu shiri kwata-kwata, saima yaƙar juna da akeyi.
Kuka sosai Fadwa ta dinga yimata akan ta shiga uku itakam, ga Anaam tazo a bayanta ta samu ciki amma ita tun miscarriage data samu babu wani bayani (Karfa ku manta ko Gwaggo Halima bata san Fadwa zubda ciki taiba. Ƙawayenta ne da Gwaggo kawai suka san wannan sirrin, sai ko Anaam. Gwaggo ma ita da Bibah da hajiya Luba maman Bibah kawai suka sani).
“Kinga kwantar da hankalinki a gama hayaniyar bikin nan sai mu tafi Germany kiga likita, karma ki bari wani abu ya tada miki hankali kinji shalele”.
Lallashin Mamanta ya saka mata samun ƴar nutsuwa harta shirya ta bita sukaje gidan bikin, inda da ace sun san mi Gwaggo ke ƙullawa da basuje ba, sai dai bawa bai isa sanin gaibuba daga kadarar abinda zai faru a minti guda na gaibunsa sam………✍

 Humm, yau fa akeyinta????????????????????????.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button