NOVELSUncategorized

KWARATA 69

???? —— 68


          Wuri ya samu yayi parking ya fito a nutse yana murmushi , hannu ya fara bawa mutane suna gaisawa duk wani ma’aikaci dake wurin saida Sultan ya miƙa mishi hannu suka gaisa cikin sakin fuska , shima dai wankakken matashi ne wanda shekarun shi bazai wuce kamar na Dikko ba ,


       Wurina ya nufo yana murmushi , nima murmushin nayi masa cewa takwarana barka da zuwa , da yawwa ya ansa yayi gaba nabi bayanshi muka shiga ciki , a palo muka samu Kaka gaba ɗayanmu wuri muka samu muka zauna , bayan mun zaune Sultan ya gaishe ta , ta ansa cikin sakin fuska da ɗan barkwancin hakan nan dai.

      Fira sukaci gaba dayi da Kaka ni kuma na miƙe nayi ɗakina , ina zuwa alwallah nayi na gabatar da sallah azahar bayan na gama naci gaba sabgogin gabana a cikin ɗakina , kayan da Yazeed ya kawomin na buɗe ina gani , wanda sukafi burgeni suka tafi da tunani na fara zamewa gefe ɗaya zan kai ɗinki.

      Ina ta ciccire kayan ne Sultan ya shigo , kamar ya saba dani ya duƙa wurin kaya shima yana fiddowa yake tambayana me za’ayi dasu ne ? Ina murmushi nace ɗinki zankai na taɓa wanda zankai ɗinki da hannuna , ɗan murmushi yayi kaɗan ya fara ciro wasu daga cikin wanda na fitar zankai ɗinki yana cewa gaskiya wannan bama sanshi , tou wai har an kawo lefen ne ni ban sani ba …..?

Dariya nayi nace bafa lefe bane ba , dani dashi gaba ɗayanmu kallon juna mukayi lokaci ɗaya , kyakkyawan murmushi yayi min yana cewa waye ya baki ? Wani ne ya kawomin , wayyo mun kuwa gode ya faɗi maganar yana komawa gefen gado ya zauna.

    Sultana ya kira suna na , ba tare dana juyo ba nace na’am , Abba yace nazo na ganki na kuma gaisheki ni Abubakar Sadiq nake suna kirana Sultan ne sunan Baban Mami na ne , ina da mata ɗaya yarana biyu , auren zumunci shine al’adar wannan ahali , amma ni aurena na farko banyi auren zumunchie ba saboda babu wacce zan aura a lokacin yaran duk basu girma ba ni kuma na tashi aure Abba yace inyi kawai daga baya idan yaran sun girma sai in kulle ta biyu da auren zumunchie , kin ganni na ganki ni kinmin a haka Allah yasa nayi miki…..?

        Ba tare dana juyo ba nace Ey mana kamin ina sanka , amma fa ni karuwa ce shin zaka aura karuwa ? Yi yayi kamar baiji abinda nace ba yaci gaba da cewa Mami ta bada shawara a ɗaura aure sati mai zuwa sati na gaba kuma sai ayi shagalin biki , nace tou Allah yasa alkairi ya bamu zaman lafiya fita da sharrin dake ciki ubangiji ya kauda shi ya tsinkule idanuwan maƙiya , am3n Sultan ya ansa tare da miƙewa idan kin gama haɗa kayan ki sameni a waje sai in kaiki , na ansa da tou shi kuma ya fice…

      Yana fita naci gaba da fiddawa bayan na gama haɗawa na zuba a lader na ɗauka na fita , a mota na samu Sultan na buɗe na shiga saida na zauna na rufe yace ina zamuje ne ? Nace masa goruba road , murmushi yayi tare da kallona yace kice dai amaryar tawa mai kuɗi ce goruba kike kai ɗinki ? Murmushi nayi ba tare da nayi magana ba , jinjina kai yayi bai sake magana ba ya taka mota muka fita daga gidan , muna fita wayarshi ta fara ringing ɗauka yayi banji abinda abokin wayar yace ba shidai yace zanje goruba ne , a , a kayi haƙuri don Allah jirani yanzu zan ajiyeta nazo don Allah , babu damuwa bara na fara zuwa tou yana faɗin haka ya ajiye waya , yana cewa yi haƙuri da Allah na anshi saƙo , babu damuwa na bashi ansa.

      Hajiya wai bayan su Dad inmu shi Malam kafin ya mutu yana da wasu “ya “yane don Allah ? Hafsa ce zaune a gaban Kakarta take tambayarta shin ko Dad inta yana da wasu “yan uwane bayan wanda ita ta aifa da cikinta ? Hajiya dake kwance tana gab da ramin mutuwarta tace Hassatu me yasa kikai min wannan tambayar ne ?

     Gyara zama Hafsa tayi cewa ba komai kawai dai ina so na sani ne , cikin yanayin wahaltuwa ta majiyyacci Hajiya tace yana da yara biyu amma basa tare damu a halin yanzu ? Hajiya suna ina ne haka ? Fashewa da kuka Hajiya tayi cikin kuka take cewa haƙiƙa ita rayuwa taƙaitacciya ce kuma ƙarewa takeyi ba tare da tayi shawara dakai ba , duniya da komai zaka ajiye kaje ga Allah , babu wanda yazo da arziƙi kuma babu wanda zai koma dashi , ruɗin duniya da shaiɗan yasa na tabka kuren da bashi da gyara kuma rayuwa ta riga ta ƙuremin , cikin kuka sosai taci gaba da cewa yau da zanga Aliyu da ɗan uwanshi dana roƙi gafararsu su yafemin , ni nake kwance ina ciwo amma duk lokacin dana kwanta da sunan bacci sai nayi mafarkin ina faɗawa cikin wani irin tsukakken rami kuma wuta yake ci a cikin sa ,

      Hassatu duk arziƙin ka baka isa kayi ma wani arziƙi ba , haka kuma idan ubangiji ya arzurtaka kai bawa baka isa ka talauta wanda ubangiji ya azurta ba , kowa tsirara yazo babu wanda aka haifa da wando ko riga kowa haka ya faɗo kuma kowa haka zai koma daga shi sai likafanin shi , duk abinda kazo duniya ka tara kanaji kana kallo kana sanshi zaka tafi ka barshi magada suci gadonshi ,  ka bar musu dukiya sunajin daɗin duniya kwana kaɗan sun manta dakai sunci gaba da sharholiyar duniya sai ɗaiɗaiku a “ya “yan naka zasu riƙa tunawa dakai har ka samu suyi maka addu’a.

         Haka take ga mace , idan mijinta ya kwanta ya mutu kuka na wani lokaci zatayi daga inda aka raba gado aka bata shikenan ta mance da shafinka a rayuwarta , ga dukiya ka mutu ka bar mata gidanka taci gadonshi tanajin giyar kuɗi yana motsa ta taci abinda ranta yake so tasha wanda take so idan za’a nemi shawararta a misali za’a ce mata Hajiya ko a dawo da Alhaji daga duniyar mutuwa cewa zatayi a , a , a ƙara kwaɓa ƙasa a zuba a saitin kanshi , bayan wasu watanni tayi takaba ta gama tuni ta manta dakai namiji zata samu ta aura kana lahira wani yana kwana a gidanka…

       Idan kana da “ya “ya da ita kila idan tana da sauran imani ta kallesu ta tuna dakai , dan ba duka aka taru aka zama ɗaya ba , to ni ba auren nayi ba Hassatu dukiyar nake mawa wannan dalili yasa na fasa gidan na kora “ya “yan malam biyu suka shiga duniya yayin dana kashe uwarsu saboda san duniya kuma duk saboda “ya “yana nayi haka dan ina so suji daɗi kuma sufi na kowa , amma kaico duk wannan yaƙin da nayi Hassatu ubanki sai yayi ruf da ciki akan kaf wannan dukiya shi ya cinyeta duka ya hana “yan uwanshi komai nima mai yaƙin sisi bai bani ba duk abinda nace masa ina so , ko ya kawo abu ya ƙare sai yayi masifa sosai sannan ya ɗauko ya bani kamar zai dokeni. Ki gayamin ɗan da bai ma idonka ba bayan idonka zaiyi ne ? Hafsa tace a , a , murmushi mai ciwo Hajiya tayi sannan tace…

       Ina da abiyar zama kuma tana girmamani sosai a matsayina na Yayarta a wurin miji , tana bani girma na yadda ya kamata ko aiki taga zanyi bata barina nayi idan har kika ga ina aiki tou lallai Maryam bata lafiya ne , kuma ko tana ciwo saita daure cikin ƙarfin hali tazo ta kamanin dan dai ta bani girmana da mutuntuwa na ina gaba da ita a gidan aure.

Tunda nake ban taɓa ganin ɓacin rain Maryam ba domin mace ce mai haƙuri kunya kawaici da kara , duk “ya “yana dana haifa bana musu wanka ko tsarkin kashi ko goyo duk Maryam take musu idan har kika ga ɗana a hannuna to wallahi nono yake sha kuma yana gamawa Maryam zata ɗaukeshi ta goye , wankina dana yarana duk itace take haɗawa tayi ,

     Duk lokacin da Maryam ta samu ciki sai nayi yadda na lalata cikin nan ya zube nayi ta neman asiri karta aihu amma dake ubangiji yayi alƙawarin biyu sai sunzo duniya Allah ya bata Aliyu da Muhammadu , bana san yaran kwata² ina ta neman hanyar da zanyi na sabauta musu rayuwa dan bana san ace “ya “yana suna da “yan uba ba hangen wata irin ƙatuwar gona da Malam yake da ita tun a wancan lokacin an taya gonar naira dubu ɗari 3 da hamsin bana so ace an raba wannan kuɗi idan Malam ya mutu wasu su samu sai nawa kawai.

     Wannan gona duk duniya itace kaɗai Malam ya mallaka bayan ita bashi da komai a duniya kuma gonar itama ba gadonta yayi ba , domin talauci ne ya isheshi shine ta fara harkar tsibbunci kuma Allah ya dafa mishi kasuwa ya buɗe yayi ma wani attajiri aiki da buƙata ya biya shine ya baya da gonar yace ya riƙa noma dan ya cida iyalinshi.

     Haka Malam yaci gaba da aiki a ƙauye har manyan “yan siyasa suka ganoshi duk buƙatar da mutum yazo dashi insha Allah Malam yanayin aiki an dace , abinda ya maidomu garin Katsina wata yayi ma aiki tayi mishi kyautar gida muka tattaro muka dawo birni.

Muna dawowa liƙafa yaci gaba sosai a taƙaice dai Malam ya tara manyan kuɗi da ƙaddarori manyan gonaye a garin funtuwa gidaje a cikin gari , ganin kullum Malam yana ƙara ginuwa shine na nemi hanyar da zan kora Maryam , bayan nayi shawara da wata aminiyata itace ta bani shawara mutuwar Maryam shine kawai mafita , idan ba mutuwa tayi ba ko sun rabu da Malam itama zata saka ran zataci wani abu a dukiyar gadon fitina za’ayi sosai shafeta daga duniya shine kawai abinda ya kamata muyi , to itace ta rakani wurin wani boka yayi asiri ya haɗa Maryam da aljannu aka tura mata yace idan ta firgita tayi ƙara aljannin zaiyi tsalle yahau saman harshenta take a wurin zai zuƙe jininta shikenan an rufe littafinta , idan kuma ta kira sunan Allah aljanni bazai iya zuwa wurinta ba , haka kuwa akayi Maryam dai ta tafi.

    Bayan mutuwar Maryam kuma nayi makircin da nasa Malam ya korasu Aliyu daga gidan nan , nayi tunanin idan suka tafi za’a sacesu dan nayi zaton kawai zasu halaka a duniya ne , da naji labarin basu ɓace ba shine nayi asirin da zasu manta da gida kwata² , kwatsam sai naji labari wani gida sun ɗaukesu suna zama dasu shine na faɗawa mahaifinki nace yasan yadda zaiyi da yaran nan dan a lokacin Malam ya rasu nace idan har hankin yaran nan ya dawo gida zasu buƙaci a basu gadonsu ,
https://www.2gnovels.com     Wannan dalili yasa Dady ya tura Bello ya shiga rayuwar Binna , saboda Bello baijin magana ko kaɗan iyayenshi ma kansu ji sukeyi dama basu haifi banzan ba , kuɗi Dady yake biyanshi kuma shine yace yana so Bello ya gurɓatawa Binna rayuwa yadda ko ya girma ya zama mara gulihu dan karya nemi kuɗi kuma yanaso Binna yayi wulaƙantacciyar rayuwa karya zama na gari dan baya so kwata² ya tuno da labarin gida  , Bello da Dady sukayi ciniki Dady ya bashi rabin kuɗin aiki , shine Bello yayi asiri ya saka Binna ya fara caca shan giya neman mata da sauransu , wannan aikin duk na Dady ne Bello kuma ya biya mishi buƙatarshi , aikin Bello kuma shine ɗaukar fansa akan abinda Binna yayi mishi na ansar budurcin matarsa , Binna ya gudu shine Dady yace ba’a barin maƙiyi ya tafi ka dawo dashi wurinka yadda yayi maka kaima ka rama , shikenan Bello yaci gaba da jifar “ya “yan Binna da asiri…

      Duk nice na kawo wannan shawarar amma Ubanki ba “yan uwanshi ba ni kaina sisi ya hana a kuɗin gadon nan , girgiza kai Hafsa tayi tare da cewa har nawa ne kuɗin gadon ? Hajiya tace zunzurutun kuɗi Malam yabar naira miliyan 45 gonaye da kuma gidaje , miƙewa Hafsa tayi tana shafa wayarta tace tou ƙalu bale ga rayuwarku domin ɗiyar Binna ta tiso ƙeyarku gaba dake da Dady ƙaryarku ta ƙare ba abinda ya shafeni kinga tafiya…….tana kaiwa nan ta fice daga gidan.

       Da gudu Hafsa ta fita tana kuka innalillahi wa’inna ilaihir raji’un yanzu Baba Binna ƙanin Dady ne shine yayi iskanci dani……? Wani irin ihu tayi cewa na bani na lalace ni Hafsa ubana ya kwanta dani ya buɗemin jikinshi na gani , da sauri ta rufe idanuwanta ta dafe kanta , yauni na shiga 3 ni Hassatu na lalace Baba Binna Allah ya rufa maka asiri da baka raye yau da wane irin baƙin ciki zakaji idan har kasan ni ɗiyar ɗan uwanka ce ? Wayyo Allahna ƙanin ubana yayi iskanci dani kaico da wannan tsohuwa , tirr da halinki duk kece silar rushewar komai ni naga tsiraicin ƙanin ubana yaga na “yar sa Sultana kuma taga na Dady , itama ita da Dady kenan sunyi ? Tabbas sunyi shi yasa har ta ɗauko videon girmanshi ta turomin , kai mun shiga 3 mun lalace wani irin ihu ta kurmama tare da faɗuwa ƙasa somamiya…..

       Kai anshi ka irga kuɗin , Bello yakeyin magana bayan yasa wani matashi ya anso jaka daga hannun Dady , buɗe jakar sukayi amma da mamaki sai suka ga wayam , ce ma Bello sukayi ai babu komai a ciki , ɗago kai yayi da niyar yima Dady magana Dady ya gaggaɓe da dariya yace kana wasa dani kenan ko ? Ai kace idan na kawo kuɗi saika sokamin wuƙa na mutu Bello ka cika tsarabarka da yaji ƙaryarka tasha ƙarya yau nine ajalinka hukuma zata kashe ka da hannunta bayan ta kamaka da hannu dumu² a kisan Sultana ,

       Bello yace ai hukuma bazata kashe ni ba ta dalilin kisan Sultana saida ta kamani ta dalilin kisan ka , idan baka sani ba bara na faɗa ma tun daga ranar da kasa akayimin duka a ofishin “yan sanda duk wani abinda ya faru tsakanin ni dakai tun daga ranar dana fara zuwa wurin Binna ya ɗaga wasu takaddu yace to ka sani yana rubuce anan ciki…..

       Wannan gurzajjin ne amma na gaskiyar ya tafi zuwa hannunshi , duk halakkacin da nayi maka lokaci ɗaya kasa ƙafa ka shure saboda kai kanaji kana da hukuma a hannunka kai ɗan siyasa tou ka sani nawa siyasar yafi naka , dani dakai yarinyar da muka haifa tayi wasa da hankullanmu lokaci guda wurin ganin ta haɗa mana fitina ta yadda zamu fara muna farautar junanmu ,

       Na ganota ne domin kirana da tayi da layin da ita kaɗai na kirata dashi cewa saina kasheta , na yadda da hakan da tayimin maganar ka ta kuma yimin maganar Sultana , tana tsaye ne a saman ƙafafuwanta wurin ganin taga bayanmu dukanmu gaba ɗaya daga ni har kai ,

     Shi yasa tayi amfani da wasu sirrika data sani wanda kwalwarta da tunaninta ya bata , sai tayi amfani da wannan sirrinka wurin kirana tace kace kaza² kaima saita kiraka wanda haka yasa yanzu kazo min da jaka babu kuɗi.

      Saboda ka yadda da cewa zan kashe ka ne yayin daka bani kuɗi domin tafiya da gawar Sultana , banzo da ita ba kuma ban kamota ba amma ina tare da duk wani motsi nata , ta fita daga gida bayan sallah azahar misalin 2:31 , wani ne ya ɗauketa a mota bayan Dikko yaje gidansu ya fita kuma yasa an tare hanyar fita da shiga harsai ya gama magana da ita ya tafi ,

     Mota mai lambar kaduna ta daɗe a ƙofar gidan sakamon hanata shiga da akayi cikin gidan , bayan kimanin awowi biyu da wasu mintuna Dikko ya fita daga gidan mota mai lambar kaduna ta shiga , ta daɗe motar sosai sannan ta fito daga cikin gidan bayan mai tuƙa motar ya fito ɗauke da Sultana ,

      Yaje kasuwa central market ya anshi saƙo , daga nan ya wuce goruba road , yanzu haka tana goruba road j ta fita daga cikin mota ta shiga shagon ɗinki a halin yanzu tana cikin farin ciki shin zaka bayar da kuɗi na basu damar kasheta ko kuwa…..?

     Dady yace takaddun da kake magana ka tura zuwa gareshi waye shi ? Bello yace Dikko ne nayi haka ne domin kuɓutar da tawa rayuwar shin zaka bada kuɗi nace su dawo dasu karsu isa wurinshi ? Har yanzu kana da sauran dama mutuwar Sultana ko kuma taka wace ce ka zaɓa…..?

     Dady yace amma me yasa ka tura shedar takkadu wa Dikko ? Saboda shine mijinta kuma ya zama dole yasan duk wasu sirrika da yake ta faman bincike babu dare ba rana , na yanke kawai na rubuta komai na tura mishi ta hanyar ɓoye sunana amma na bayyana naka , abinda yasa kuwa nayi haka dan kayi min kuri da hukuma shi yasa na miƙa kaina ga hukumar gaba ɗaya ,

       Kai…. Dady ya faɗa tare da nufa wurin Bello ta haɗashi da bango yace kana da hankali ne ko kayi hauka ne ? Dariya Bello yayi tare da cewa lafiyata garass amma ka sani matar da Mami ta turo ta ɗauki kwalbarnan munyi dukawa matar sosai ta samu ta kubce bayan mun bita bamu samu ganinta ta ɓace mana a cikin asibiti , taje ta ɓoye tayi jinyar sirri a wani wuri daban bayan ta samu sauƙi ta dawo ta duƙufa neman Sultana bata samu ganinta ba amma a bincikenta ta gano Sultana tana tare da DK shi yasa ta tafi wurinshi domin buɗe mishi duk wani ɓoyayyen sirri kenan kaga faɗan yazo ƙarshe , na kashe ko a kashe ni wannan shine muradina domin ni nasan ƙaryana yazo karshe kuma banda sauran dubara ko mafita tunda case ya koma hannun Dikko………

Ka saki wuyana kawai kaje ka fara neman shedar da zaka kare kanka , 45miliyans sai aje ayi ÷ ÷ ɗinsu in to su Sultana…….. Kowawa sukaci gaba dayi tsakanin Bello da Dady , dariya Bello keyi domin shi ƙarya yake ma Dady babu wani abinda ya rubuta akaima Dikko amma karuwarshi yaji labarin tana ta zuwa neman Dikko ba’a barinta ta ganshi , kuma yana ta farautar ta har yanzu basu haɗu ba , dan ƙawarta wacce ta bawa Sultana numberta tace zata kirata itace ta bata labarin yaran Dikko sun kamata sunyi mata tambayoyi kuma ɗiyar Binna tana nemanta , tace ta anshi number Sultana amma ta manta bata ajiyeta a wayarta ba , data tambayeta inda Sultana ke zama shine tace tana zaune wurin DK a goruba road…

     Shi kuma Bello ya girgiza Dady ne dan ya anshi kuɗi a hannunshi amma kamar yadda yace duk wani motsin Sultana yana hannunshi tabbas yana tare dashi…

     Saida suka gama cakuwa kowa ya saki kowa cikin wahala , saida Bello yayi nishin wahala yace kuma nine na tura yarinyar ka ta zama karuwar Binna , wani irin gumji Dady yayi da niyar riƙo Bello amma ya ruga da gudu ya hau mota ya nufi goruba road domin ganin bayan Sultana dan lokacin da boka ya ibar masa wa’adinsa ya cika , danshi baya iya auren uwarshi gara kawai ya kashe Sultana magana ce ta shari’a kawai ai tayi ana Sign daga ƙarshe ƙotu tacezaiyi gidan yari , Dady cikin ɓaci rai yace ma “yan sanda da yazo dasu suje zai sake nemansu ,

     Hafsa kuwa mutane suka ɗauketa suka mayar da ita cikin gidan Hajiya , aka yayyafawa banza ruwa ta dawo , tana dawowa taci gaba da ihu tana na bani na lalace… Gaskiya Hajiya ke sheɗaniya ce ta bada labari a jarida ina ahalin mahaifiyar shi Ba Binna……? Wato mahafiyar ita Maryam kakar ba Binna kenan wacce ta haifi mahaifiyarshi ina suke……………? Ta tambayi Hajiya yayin data sake tafiya zuwa duniyar suma.

       Ina zaune a saman kujera shagon ɗinki ana nunamin style Sultan yacemin bari yaje ya dawo kafin in gama zaiga wani abokinshi a road na gaba , fatan dawowa lafiya nayi mishi ya tafi ni kuma naci gaba da dubawa saboda tun farko nace nidai suymin basai na duba ba amma suka tursasani wai indai duba…

      Bayan na gama zaɓa na miƙe ana auna ni juyowar da zanyi naji kaina ya sara sakamakon Bello dana gani tsaye ya raɓa ƙofa biyu yana kallona , wata irin mummunar faɗuwar gaba naji a dai² lokacin daya fara kwaikwayon muryata cewa kun haɗa kai akan zaku kashe wata yarinya amma shine naji yana cewa sai ya kashe ka , shigowa yayi cikin shagon yana cewa idan baki mata ba da kikayi wannan maganar ai dariya nayi miki , na baki ansa cewa ko wace daƙiƙa saƙo da lungu rana da dare neman sa’ar mutuwarsa nake saina kashe shi.

      Hihihihihihi yayi dariyarshi ta raini wayau yace zakiyi tunanin banda lissafi shi yasa nayi wannan maganar ? Tou saboda kece kaɗai na siya layin nan , nine nan na kiraki nace saina kashe ki , yasa anata gadinki ya hanaki fita saboda baya so ki mutu shin yanzu yana ina ? Ko ya isa ya tseratar dake daga mutuwa ? Kin taɓajin labarin zafi da radaɗin azabar fita rai ? Hihihihihi ya sake dariya yace ai na manta yarinyar malama ce ba mamaki an baki labari a islamiya yayi maganar dai cikin yanayi na jahilci.

      Saida ya sake dariya tare da tafa hannayenshi ya ɗora hannunshi a saman kunnenshi kamar yana waya da irin maganata zanzo fesra hotel sanye cikin hijabi da niƙaf napep zai saukeni idan ka isa ka kamani ka kasheni a wurin hihihihihihihihi ya ƙarasa maganar yanayin dariyarshi mai tada hankali sai kuma ya ɗaure lokaci guda yace a maimakon kizo sai kikayi wa Hafsa waya ke mai wayau kika rufzata a rami sai tazo saida ya sakeyin dariya ya fara matsowa inayin baya yaran shago kuwa rugawa sukayi suka fita daga cikin shagon lokacin da suka ga Bello ya fiddo wata irin shareriyar wuƙa daga cikin rigarshi yana cewa rana dubu na ɓarawo rana ɗaya cif shine na me kaya yau gani gaki bankwana da duniya , ya ɗaga wuƙarshi ya nufo dai² saitin zuciyata dashi………..

      Yana cewa ba kin kirani cikin dare ba ni kuma na faɗa miki cewa zan kashe shi misalin 10 dai² na safiyar yau , kina tunanin ina cikin maye ko ? Tou kwalba biyar na shanye a daren amma kaina baya manta komai , idan kin isa barzahu lafiya kicewa Binna zanzo na yayyafawa kabarinshi giya kwalba biyu ta tayashi murnar isowar uwar masu gida wurinshi….

PLS CLICK ON ADS

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());    

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button