Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 31

Episode 31_*

……….WASHE GARI koda Raudha ta farka a barcin safe data koma ta samu Ramadhan ya wuce. Cikin mamaki takebin kulolin jiya da Anne ta zubo musu nama a ciki da kallo. Ta miƙe da ƙyar tana cire hijjabin sallarta dan akan sallaya barcin ya kwasheta tana azkar. Kulolin ta nufa. Ya cinye farfesun naman kan tas sai ƙasusuwa. Kazar kuma kusan ɗaya da kwata. Sosai mamakin hakan ya rufe Raudha, shiko wane irin kuren nama ne haka? Sai kace ya haɗa iri da mayu (😱😝 Raudha ta rama bani ba). Ta ɗan girgiza kanta zuciyarta na raya mata da alama dai ba shikaɗai bane akwai aljanun cin nama tare da shi. Da wannan tunanin ta nufi toilet. Wanka tayo da brush, bayan ta fito ta kimtsa jikinta da ɗakin. Itama kular sauran naman ta ɗauka da nufin ci duk da yayi sanyi kaɗan sai taci karo da takarda guntuwa da ATM card. Ɗauka tai ta ƙarasa kan sofa sannan ta buɗe takardan. Pin ɗin atm ɗinne a farko. Sai gajeren rubutu da bai wuce words goma sha biyu ba. (Anne zata aiko da sabuwar mai aiki, tare da masu zuwa miki yawo). Shike nan abinda ke jiki, sai wani ɗan zane kamar emoji data gagara gane ma’anarsa.
Saƙon ta dinga maimaitawa a zuciyarta, haka kawai take jinsa da girma. Tasan dai Anne bazata kawo wadda zata cuta mata ba, sai waɗanda zasu zo mata yawon ne take ɗar-ɗar, dan inhar yaran gidan ne akwai matsala kenan.

  Duk yanda taso samun nutsuwa ta gagareta, dan hankalinta bai tashi ƙololuwa ba sai dai baƙin nata suka iso har su biyar. Aina'u, Lubnah, Basma, Bilkisu, Muneera. Ta gane Lubnah ta kuma gane Aina'u. hakama Basma da Bilkisu da sukazo cike da murna suka rungumeta.. Su Aina kam suna mata wani kallone kamar trash. Dan Lubnah harda faɗin, “Kurwarmu dai ɗacine da ita, kar aga mun dawo kusa ai tunanin nama yazo. Wlhy mutum yace zaici ya taɓoma kansa mutuwa ne kawai”.
   “Tuna mata dai”. Cewar Muneera.

Komai Raudha batace musu ba. Sai gaishesu da tayi. Duk da basu amsa mata ba sai ta danne. Falon tsakkiya ta nufa inda tacema mama tambaya a gyara musu ɗakunan ciki. Mama Tambaya tai ɗan jimm kafin tace, “Amma ranki ya daɗe kodai ɗakunan falon farko zaifi, dan falon tsakkiya dana karshe da upstairs ke ce kawai keda hurumin yin huɗɗa da shi. Sai ko idan kunso kai baƙi masu muhimmanci ”.
Murmushi Raudha tayi, “Mama waɗan nan ma ai sunada muhimmanci, dukansu ƙannen mai gidan ne”. Daga haka ta juya ta koma ciki.
Sai dai kuma mi, koda aka gyara ɗakunan tsakkiyar sai su Lubnah sukace bazasu zauna anan ba sama suke so. Kobi takan Raudha da roƙon da Basma da bily ke musu basuyi ba suka nufi saman. Corridor ɗin ɗakinta suka nufa, duk bedrooms ɗin sai da suka buɗesu kowa ya zaɓi ɗai-ɗai. Da Aina ma na Raudha ɗin tace tana so, sai da Lubnah ta jata gefe ta raɗa mata wani abu a kunne sannan ta canja dana kusa da ita. Dama 4bedrooms ne, dan haka su uku kowa ta ɗauka guda.
Mama Tambaya zatai magana Raudha ta hanata, dole tai shiru. Koda Basma ta kira gimbiya Su’adah ta sanar mata sai ta hau banka mata zagi akan ina ruwanta, tunda can ɗin sukeso basai a barsu ba, daga ƙarshe taja mata gargaɗinta bayan ita takira wani ta sanar masa sai taci ubanta. Kuka sosai Raudha ta shiga ɗaki tayi, sai dai a gabansu bata yarda murmushi ya bar fuskarta ba.
Abinci da kansu suka bama kuku umarnin abinda za’a dafama kowannensu, Raudha dai batai ko tari ba, hasalima tunda ta shige bata fitoba sai da Mama Ladi ta iso. itace Anne ta aiko ta zauna da ita. Tayi hakane kuma domin ta dinga koyama Raudha abubuwa masu muhimmanci dan ta kula ba komai Raudha ta iyaba kasancewar mu ƴaƴan talakawa munada ƙarancin wayewar wasu abubuwan irin na masu hannu da shuni. A wahalar rayuwa da ilimin zaman cikinta kuwa duk da Raudha nada ƙarancin shekaru tanada wayo saboda irin rayuwar data tashi a ciki.
Mama Ladi mace ce wayayya dan tayi iliminta na addini dana zamani gwargwadon iko. Ƙaddarar rayuwa da jarabawar iska yasa bata zaman aure. Tayi aure yafi sau uku mazan na rasuwa. Wannan yasa ake gudunta a garin Taura. Harta kai ko gittawa tai ta waje sai a dinga gudu. Abin ya isheta ta tattara kayanta zata gudu a garin tsautsayi yasa Alhaji Basheer Taura (Pa) ya bugeta da mota lokacin yazo Taura ɗin. Taji ciwo sosai, dan haka ya kaita asibiti, bayan tayi jiyya ta warke sarai yaji matsalarta. Daga nan ya kaita family house ɗinsu na Taura ta zama shugabar ma’aikatan gidan tana kula da komai da kowa. Amanarta da iya mu’amula yasa suke ƙyautata mata sosai. Wanda ma bai sani ba yakan ɗauka ƴar uwarsuce a yanzun.
Maimakon sashen ma’aikatan gidan a falon farko Raudha tasa aka bata ɗaki. Hakan yasa su Lubnah basu san da zuwan mama Ladi gidan ba. Duk da ba wani damuwa sukai da ita ko a Taura ɗin ba. Hasalima yanda suke ƙyarar masu aiki da hantararsu haka sukema mama ladi itama

        ★Ranar da su Basma sukazo government house gimbiya Su'adah ta nufi masarautasu dake a jihar Bina. A can ta samu Adda Asmah na jiranta, dan dama haɗuwar tasu akan Raudha ce dai da suke kira karamar alhaki ta kuma zame musu damuwar zukata. Bayan sun samu shiga sashen mai-martaba suka gaisheshi sai suka ɗan shiga sashen tsohuwar kakarsu dake fama da jiyya kusan shekara bakwai kenan. Sun duba jikinta itama kafin su koma sashen fulani. Dan a tsarinsu sauran matan sarki basu ishesu kallo ba balle gaisuwa. Shiyyasa sam babu haɗin kai tsakanin yaran gidan tunda suna kallon su gimbiya Su'adah dake amsa sunan manya basu mutunta iyayensu da jansu a jiki balle su ƙanana.
    A babban falon kusa da fadar fulani suka yada zango, bayan sunci sun sha gimbiya Su'adah ta labarta musu yanda sukai da Raudha akan turaren tsakin kuka.
   Adda Asmah taja tsaki cikin ƙyaɓe fusaka da takaici take faɗin, “Kuji makirar yarinya, to ai tasha a no-no ke kuwa ai dole. Jinin karuwar gogaggun duniya ai dole tayi makirci irin haka wai Asthma ta tashi..”
  “Humm ki bari kawai Adda. Babban abinda ya ban takaici da ƙonan zuciya yakema bisa kan sake ƙonamin har yanzu wai ko kunyar idona Ramadhan bai gani ba ya ɗauka yarinyarnan cikin rawar jiki ya fita da ita saboda shi fitsararrene...”
  “Karkiga laifinsa Su'adah. Ke kina ganin zasu barsa hakane babu wani ƙulli? Kinsan kuwa wacece hajiyar birni? Gogaggar karuwa uwar karuwan manyan ƙasar nan. Yo uwar karuwan manyan ƙasa mana, tunda kuwa ƴaƴanta harda uwar yarinyar sune hajarta a wajen manyan ƙasar. Dan an tabbatarmin harda aurensu bin maza sukeyi”.
    “Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un. Wlhy Adda sake firgitani kikeyi”. Gimbiya Su'adah ta faɗa cikin nuna razana da tashin hankali.
 Kafin Adda Asmah ta sake cewa wani abu Fulani dake waya tun dazun ta ajiye wayar tana maida hankalinta garesu. “Ita hajiyar birnin har wacece ita, har mi akai akayita. Ai wlhy lokacin da kuka kawomin labarin tushen yarinyar ma sam ban kawo Hajiya Ɗahare bace hajiyar birnin, da ko aurenki zai mutu Su'adah bazan yarda da wannan kwamcalar haɗin ba. Dan nasan baku manta wata shegiyar karuwa da mukaita kicimillin raba mai-martaba da ita ba shekara ashirin da ɗaya kenan”.
   Cikin zaro idanu waje su duka har haɗa baki suke wajen faɗin, “Ammy wai kina nufin matsiyaciyarnan data like masa a loss lokacin ana shirye-shiryen basa mulki”.
 “Ƙwarai kuwa ita fa, to itace hajiyar birni kakar wannan shegiyar yarinyar da aka mannama Ramadhan.”
  Sosai tashin hankali ya bayyana a garesu, dan su ɗin shaidane akan wahalar da iyayensu mata musamman mahifiyarsu taci a wancan lokacin. Ko randa kakansu ya rasu mutane nata raɗeraɗin da karuwa mahifinsu yazo da ga loss. Sakamakon acan yake aiki. Ba kowa bane kuma face hajiyar birni. Bayan an bashi sarauta ma tasha kawo masa ziyara a ɓoye kamar yanda sukeji, harma ya furta cewar zai aureta shaƙiƙan dattijan masarauta sukai masa kacaca, aka kuma saka masa ido matuƙa har sai da aka rabashi da ita. 
 (Kowa yasan mahaifinsu mai-martaba na yanzu mutum ne da dama bayajin magana tun ƙuruciya, dan ita kanta fulani dake wannan babbotan adai rufe rufau, akwai babban akasin daya faru tsakaninta da mai-martaba ɗin tun tana ss2 secondary, bayyanar abin kunyar daya ƙunsa mata yasa iyayenta saurin zubar da shi aka rurrufe akai musu aure ya wuce da ita ƙasar waje sukaci gaba da karatu a can. Dan dama shi acan ɗin yake, wani zuwa hutu da yay ya ganta daga haka yayta jan ra'ayinta da soyayya har ya ƙunsa mata ciki. Gashi kuma ƴar uwarsa ce, dan kuwa ɗiyace ga ƙanwar mai martaba mahaifinsa kenan, kuma ƴar waziri ta wancan lokacin. Amma sai gashi yau duk sun manta da waɗan nan ta murje ido tana faɗin munin wani harda nuna ƙyamarsa.
     Wannan tunani na Fulani akan hajiyar birni kakar Raudha ya sake tada hankalin su gimbiya Su'adah. Duk da dai ita Addah Asmah tanayin komai ne dan ƴarta Aina, gefe kuma ga tsananin hassadar ƴar uwarta da take fama da ita shekaru aru-aru na finta da mijin nunawa sa'a. Dan kuwa Taura family sunfi family ɗin da take aure komai, shiyyasa take son ƴarta ta shiga gidan kodan su mallaki abinda ƴar uwar tata ke taƙama da shi, musamman daya kasance Ramadhan shine jika ɗaya namiji tilo a zuri'ar Alhaji Hameed Taura. Wanda ko a yanzu ALLAH kaɗai yasan iya abinda yake mallakinsa kodan kasancewarsa ɗan gaban goshin kakanin nasa. A gefe kuma shima ba azaune yake ba yana kan neman na kansa ne. Adda Asmah tasha saka gimbiya Su'adah a hanyar banza, sai dai ALLAH ya timaketa tana saurin gyara kuskurenta saboda samun tsayayyen miji irin Pa da tuni ya gama gano wacece yayar matar tasa. Sai dai bai taɓa gaya mataba gudun shiga tsakanin ƴan uwan juna.
  A take anan Adda Asmah ta gama tsara musu dolene wannan al'amari a haɗa da malamai gaskiya, Fulani ta amince, Gimbiya Su'adah dai tana ɗan janjeni, dan kuwa ita dai barta da ƙasaita da isa harma da rashin mutunci, amma bata yarda dabin malami ba. Shiyyasa anan ɓangaren kam basa shan inuwa ɗaƴa da adda Asmah ɗin..
  “Su'adah kinyin shiru! Ko baki amince ba ne?. Idan baki aminceba bawaifa dole bane, sai dai fa ki tabbatar Ramadhan ya sake miki nisa na har abada. Dan a baya gwara tunda a gida ɗaya kuke kina ganinsa yana ganinki, sai dai kawai an rabaki da shi bai miki kallon uwarsa sai kakanni ya ɗauka iyayensa. A yanzu ko ku dukane zaku rasa harsu karuwar su ɗauka. Dan kuwa dai sune masu amfana tunda ƴarsu yake aure.....”
    Wani dogon numfashi da ya katse Addah Asmah a magana Gimbiya Su'adah taja da ƙarfi, tuni idanunta sun kaɗa sunyi jazur saboda damuwa da ɓacin rai. Ji take tankar ta haɗiyi zuciya ta mutu dan baƙin ciki. “Adda dan ALLAH kibar wannan mugun fatan, dan wlhy inhar ina raye har gaban abada babu su babu wannan nasarar akansa. Ni kin sanni kawai dai bana son harka da maƙaryatannan, dan bokaye da malmn tsubbun nan mafi yawanci lokaci abinda suke faɗa ƙaryace kawai, sai dai aci maka kuɗi a barka sakarai”.
   “Bazan musa miki akwai irinsu ba, amma kema kinsan namu ba irin waɗan nan bane. Kuma ni da Ammay dai bazamu cutar da ke ba balle Ramadhan. Mu dama hausarmu anan muje musa a masa roƙon ALLAH ya karesa daga sharrinsu. sannan muɗau mataki kar yarinyarnan ta samu ciki, mu kuma dawo da hankalinsa kan Aina'u dan ɗanmu ya dawo hanunumu baki ɗaya”.
  Numfashi gimbiya Su'adah ta kuma ja a hankaki, kafin tace, “To shikenan na amince aje ɗin, amma gaskiya sai dai a samu wani amintacce yaje ni dai bazanje ba dan Abbansu ba yarda zai ba”.
 Fulani dake matuƙar jin takaicin ƴar tata Su'adah ta balla mata harara. “Tunda ke ɗin shashasha ce sanar masa zakiyi zakije wani waje. Wai nikam Su'adah yaushe zaki san ciwon kanki? Anya kuwa Basheer haka ya barki kuwa? A haka dai duk wanda ya ganki sai ya ɗauka wata jarumar gaske ce, sai dai basu san ƙatotuwar shashasha bace ba”.
   Ƙin cewa komai gimbiya Su'adah tayi, sai dai ta sake ɓata fuska alamr maganar mahaifiyar tasu bai mata daɗi ba. Haka suka sake ƙulla abubuwa daban-daban harda maƙudan kuɗaɗen da za'a kaima malaman wanda kaso biyu bisa uku Adda Asmah duk cutarsu tayi kawai.

BINGO. GOVERNMENT HOUSE

      Gaba ɗaya zaman gidan ya sakema Raudha tsanani tun zuwan su Lubnah, ga damuwar zancen aunty Hannah da kuku da taji shima ya kasa barin ranta. A wajen su Bilkisu kawai take samun sauki. Su kuma suna fita school tunda safe sai yamma suke dawowa. Duk da suma dai su Lubnah ɗin na fita aiki, Aina'u ce kawai bata aikin uwar komai sai kallon series kullum a lap-top. Sai ko gantalinta da samari dan a yanzu haka duk hanyar da zatabi ta sani na zuwa club da dare. Shiyyasa bata sakewa. gidan su Ramadhan idan tazo, saboda su dokane da 6 na yamma tayi aka kwaso yaran gidan daga islamiyya babu mai sake fita sai safiyar gobe. Kuma duk inda zaka sai dai driver ya kaika ya dawo da kai.

 Kwanan Ramadhan biyu ya dawo NAYA daga taron da suka gudanar a ƙasar Nigeria. Duk da dawowar rana yayi bai shigo gida ba, kai tsaye office ya wuce su Raudha ɗin ma a labarai sukaga dawowar tashi. Har kuma suka kwanta barci bai shigoba alamar wani abun ya tsayar da shi wanda bazai wuce zaman meeting ba.
  Ilai kuwa hasashen haka yake, dan kuwa dai zaman meeting ɗin sukai da su forma president anan cikin gidan akan son sasantawa game da batun cabinet daya sharɗanta yarda da 50-50 akan zaɓin shugabannin majalissa. Sai dai kuma a yau ɗin ma babu nasarar, dan kuwa dai Ramadhan yana akan bakansa. Da ga ƙarshe rai ɓace aka watse babu abinda aka cimmawa. Shima kansa rai ɓacen ya dawo gidan, dan haka baibi takan kowa ba yay shigewarsa ɗakinsa.
  Sai dai kuma kamar koyaushe dawowar tasa ta wanzu ne a kunnen Raudha dake zaune tana karatun Al-qur'ani bayan ta idar da salla. Agogo ta kalla, ƙarfe biyu saura. Taja numfashi zuciyarta na mamakin yanda al'amrin ke tafiya. Dama haka mulkin yake mutum ko lokacin kansa baida shi?. zata iya rantsewa tunda suka tare a gidan nan sau uku kacal taga ya dawo gida kafin takwas na dare. Sai ko randa suka fita ɗin nan daya shigo kusan biyar na yamma. Bakinta ta ɗan taɓe ta cigaba da karatunta zuciyarta na raya mata *_BAƘAR INUWA_* kennan. Gara rana da ke. Dan zama a ƙaton gida da cin mai daɗi da sunanka babba a ƙasa ne kawai jin daɗin. Talakan dake cikin waccan ranar yama fi mai mulkin jin daɗin duniyar. Tunda koba komai shi zai shigo ya huta a gidansa kan lokaci. Yaci yasha hankali kwance tare da iyalansa. Amma gasu anan kullum cikin haɗa tuggun yanda za'a halaka rayuwarsu akeyi. Bashi dake mulkin ba ba ita ƴar karoro ba dake amsa sunan matarsa.

   Koda ya kimtsa jikinsa duk yanda yaso kwanciya kasawa yay, dan yunwa yakeji sosai. Rabonsa da abinci tun breakfast na bankwana da sukayi a Nigeria shi da sauran shugabanin ƙasashe da suka halarci taro. Ga kansa na ciwo ga ɓacin ran da aka ƙara masa yanzun. Siririn tsaki yaja yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa, kafin ya tura lip ɗin nasa cikin baki ya fara tauna a hankali har sannan idonsa na a lumshe. Dan kwance yake a saman katafaren gadonsa da yaji lafiyayyun shimfiɗu na alfarma. Ƙafafunsa a ƙasa suke yana rigingine, sai filo da yay da hannayensa. A hankali ya buɗe idanunsa dake cike da gajiya da barci. ganin agogon na ƙara gudu ya sashi miƙewa ya fice a ɗakin, dan yafi buƙatar abinci mai nauyine baya son shan kowanne juice ko milk.
 Yasan bai dace yace zaije kitchen nema abinci ba, dan haka ya nufi ɗakin Raudha kai tsaye duk da zuciyarsa batason aikata hakan kuma.........✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button