Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 11

Chapter Eleven

……….Cikin gaggawa aka amshi Ummi a asibiti. Dan da ƙyar take fitar da numfashi, ga jinin da yake fita mata ta hanci da tayo tari da ya harmutsa dukkan zukatan su Yaya Muhammad. Hibbah kam ai tama koma musu tamkar zararriya. Dan koda za’a shige da Ummi sai da Yaya Umar ya riƙota shima hawaye masu ɗaci na cika masa idanu.
      Yaya Muhammad kam da baida wahalar zubda hawaye gefe kawai ya maida kansa yana sharewa. Umminsu itace duniyarsu. Itace farin cikinsu. Itace ta maye musu dukkan gurbi na dangin mahaifinsu da giɓin mahaifin nasu da suka rasa tsahon shekaru goma sha tara. Tayi haƙuri da damuwoyi kala-kala domin taga sunyi farin ciki. A kullum ƙoƙarin ta su zama mutanen kirki. Su zama masu haƙuri, su zama masu juriya. Su zama….  Su zama… Da yawa. To sukam idan akace sun rasata ina zasu saka kansu da rayuwarsu. Idan suna a gabanta sam basa tuna sun girma. Ganin kansu suke tamkar ƴan shekaru goma-goma. Bazasu so Ummi ta tafi ta barsu batare da sun cika mata burinta na ganin sunyi aure ba. Kamar yanda take addu’ar ganin zuri’arsu suma hakan shine fatansu a yanzun. Suna son yawan ganin dariya a saman fuskarta kamar yanda mahaifinsu yay sanda yana raye. Amma hakan duk bazata tabbataba sai tana a kusa da su……..
       “Ya ALLAH ka bama Ummi lafiya ka tashi kafaɗunta. ALLAH yasa ni na mutu a madadinta”.
      Furucin Muhibbat da ke kuka ya katsema Yaya Muhammad da su Yaya Abubakar tunaninsu. Gaba ɗayansu suka zuba mata idanu na ɗunbin tausayinta da ƙaunarta. Yarinya ce ita mai yawan walwala, kazarkazar, wauta, tsiwa, rawan kai, surutu duk a dalilin gata da kulawar da take samu da ga garesu. Tana matuƙar son Ummi, suma haka. Batasan mahaifinsu ba, shiyyasa suketa ƙoƙarin ganin sun cike mata gurbinsa.
        A hankali Yaya Abubakar ya taka inda take durƙushe gaban Yaya Umar da rauni ya cika zuciyarsa na tausayin kansu da autar ta su. Hannu biyu yasa ya kamota ya ɗaga tsaye. “Haba Muhibbat, maimakon kima Ummi addu’ar samun lafiya sai ki dinga ma kanki addu’ar mutuwa a madadinta?. Insha ALLAH Umminmu zata tashi da lafiyarta kinji. Ki mata addu’a da fatan alkairi, ALLAH ya na tare da ita kinji”.
        Kanta ta jinjina masa wasu zafafan hawayen na rige-rigen sakko mata. Yasa hannu ya share mata yana murmushin ƙarfin hali.
         “Ƙyaƙyƙyawa mai kama da Umminta a komai, sai dai raguwa ce bata kai Ummi jarumta ba”.
    Yaya Abubakar ya faɗa cikin ƙarfin hali yana ɗan ja mata kumatu. Maimakon tai dariya da tsalle kamar yanda ta saba idan ya faɗa mata hakan, sai ta faɗa jikinsa ta fashe da kuka. Kusan atare duk suka rumtse idanunsu, dan kukanta na matuƙar sake tada musu hankali.

        Kusan mintoci arba’in da biyu likitoci suka ɗauka tare da Ummi. Kafin ALLAH ya basu ikon fitowa. A kusan tare su Yaya Umar suka miƙe a zabure harda Hibbah dake jingine jikin Yaya Umar barcin wahala ya ɗauketa.
         Kusan a tare suka furta “Doctor ya jikin Ummin mu?”.
    Kallonsu yayi cikin furzar da numfashi yana cire norsemask ɗin fuskarsa. “Inason yin magana da ku a office”. Ya faɗa yana ƙoƙarin wucesu. A take suka rufa masa baya har Muhhibat da Yaya Umar ke riƙe da hannunta. Kusan tare suka shiga da doctor cikin office ɗin. Hakan da sukai sai tausayinsu ya sake kamashi. Dan a kallo ɗaya zakai musu ka hango ɗunbin so da ƙaunar da sukema mahaifiyar tasu. Bai wani tsaya ja musu rai ba yay musu bayani akan matsalar da ke tare da Ummi a ƙasan zuciya da hanjinta. Bincikensu ya nuna kuma ta jima da ciwon yana ta cinta a hankali, sai dai yafi nuna kansane a duk lokacin da wani ɓacin rai ko tashin hankali ya sameta. Amma zasu mata aiki insha ALLAH suna mata fatan samun lafiya.
           Duk da maganarsa ta ƙarshe taɗan sakasu jin sanyi hakan bai hana zukatansu shiga cikin matuƙar rauni ba. Ya ɗan ƙara faɗaɗa musu bayanai akan abinda za’a iya buƙata akan aikin da magungunanta. Tare da basu tabbacin inhar sun shirya a yau ɗin nan ma za’a iya mata aikin. A take sukace sun amince, duk da kuwa kuɗaɗen da ya ambata da wuya a iya samunsu kai tsaye da ga garesu. Badan suna da yawa bane sosai, kawai dai suɗin masu tasowa ne ba wasu ɗumbin kuɗaɗe suka tara ba. Amma dai tunda ya ce zasu iya bada rabi idan an kammala aikin su cika zasuyi ƙoƙarin su insha ALLAH.
         Take ya basu takarda Yaya Muhammad ya saka hannu. Daga haka suka fito domin tattaunawa akan zancen kuɗin. Dan doctor yace sai sun tura zaiyi ƙoƙarin haɗa wasu da ga kayan aikin insha ALLAH.
     Su dukansu suna aiki, Ammar ne kawai da Hibbah ƴan makaranta a cikinsu. Sai Yaya Umar da ke ɗan harkar kasuwanci saboda matsalar rashin samun aiki da matasa ke fama da shi a ƙasar nan. Sai ma yazam a yanzu yafi nutsuwa da kasuwancin sama da aikin da yay karatu akansa. Dama kuma su Yaya Muhammad ɗin nata son ganin sun ƙara masa ƙarfin jari tunda ALLAH yayma kasuwar tasa nasibi.
       Sun ɗan tattauna wajen ganin sun haɗa kuɗaɗen, cikin amincin ALLAH ma sai gashi an samu kusan rabin a hannunsu su uku. Idan Yaya Usman yazo shima zasuji mi za’a samu daga garesa. Abba dai basa saka rai game da shi sam.
       Basuyi zaman ɓata lokaci ba wajen fita su tattaro kuɗaɗaɗen har Yaya Usman da ya iso asibitin a yanzu shima, dan ya kasa jure zama acan saboda ya gwada ƙoƙarinsa na ganin an bashi Ammar amma hakan ya gagara saboda mugun ƙulli da Abba yaje yayi a station ɗin. Ya tahone kawai dan yasan insha ALLAH Yaya Abubakar zai fiddosa da zaran hankali ya kwanta. Kafin su dawo kuwa an gama shirya komai na shiga theater ɗin. Cikin amincin ALLAH zuwa ƙarfe takwas na dare aka shiga da Ummi. Sun bita da ƙyaƙyƙyawar addu’a da fatan dacewa a zahiri da baɗini.

      Yaya Muhammad ne ya fara fahimtar akwai yunwa tattare da Hibbah. Dan gaba ɗaya jikinta ya saki tamkar mara laka. Yana lura da ita ko salla a zaune ta dinga yinta. Hannu yasa ya kamo nata cike da kulawa yana faɗin, “Auta yaushe rabonki da abinci”.
        “Tun breakfast ɗin safe Yayanmu, amma kuma banajin yunwa”. Ta faɗa cikin sanyin da basu santa da shi ba.
     Su dukansu sai da suka dubeta cike da tausayi. Yaya Usman yay saurin barin wajen batare da yayi magana ba. Cikin lokaci ƙanƙani sai gashi ya dawo da teakaway.
        Zama yay da kansa zai bata amma sai tace ta ƙoshi. Dukansu babu wanda bai lallasheta ba amma tace ta ƙoshi. Sai da taga duk sun ɓata rai sanann ta amsa ta ci wanda ya saka mata a baki. Amsar cokali tayi ta ɗiba da kanta shima ta bashi. Ta sake ɗebowa ta bama Yaya Umar. Shima Yaya Abubakar haka. Sannan ta bama Yaya Muhammad shima. Dukansu murmushi suke mata a karon farko tun bayan shigowarsu asibitin da duk rayukansu suke a jagule. Amsa Yaya Usman ɗin yay ya cigaba da bata. Kusan lauma uku ta kauda kanta idanunta na cikowa da ƙwalla.
      “Miya faru kuma?”. Yaya Abubakar dake miƙa mata ruwa ya faɗa. Hawayen data matso suka silalo saman kumatunta. Muryarta na rawa tace, “Yayanmu Yaya Ammar fa?”.
         Shiru suka ɗanyi duk suna kallonta. Kafin Yaya Abubakar ya shafa kanta fuskarsa ɗauke da murmushin ƙarfin hali. “Karki damu shima zai dawo, insha ALLAH bazai kwana acan ba. Ƙarasa cin abincinki ina zuwa”. Ya ƙare maganar yana mikewa. Tashi Yaya Usman yay yabi bayansa.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button